Nations Bible

John 21

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Bayan wadannan abubuwa, Yesu ya sake bayyana kansa ga almajiran a bakin tekun Tibariya. Ga yadda ya bayyana kansa: 2Saminu Bitrus na tare da Toma wanda ake kira Dan Tagwai, da Natana'ilu daga Kana ta kasar Galili, da 'ya'yan nan na Zabadi, da kuma wadansu almajiran Yesu biyu. 3Saminu Bitrus yace masu, “Zani su.” sukace masa “Mu ma za mu je tare da kai.” Sai suka fita suka shiga jirgi, amma a daren nan basu kama komai ba. 4To, gari na wayewa, sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran basu gane cewa Yesu bane. 5Sai Yesu yace masu, “Samari, kuna da wani abinda za a ci?” Suka amsa masa sukace “A'a”. 6Yace masu, “Ku jefa taru dama da jirgin zaku samu wasu.” Suka jefa tarunsu har suka kasa jawo shi don yawan kifin. 7Sai almajirin nan da Yesu yake kauna yace wa Bitrus, “Ubangiji ne fa!” Da Saminu Bitrus yaji, Ashe, Ubangiji ne, yayi damara da taguwarsa, (don a tube yake), ya fada a tekun. 8Sauran almajiran kuwa suka zo a cikin karamin jirgi, (domin basu da nisa da kasa, kamar kamu dari biyu zuwa sama), janye da tarun cike da kifi. 9Da isowarsu gaci, sai suka ga garwashin wuta a wurin da kifi akai, da kuma gurasa. 10Yesu ya ce masu “Ku kawo wandansu daga cikin kifin da kuka kama yanzu”. 11Sai Saminu Bitrus ya hau, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku (153). Amma duk da yawansu, tarun bai tsage ba. 12Yesu yace masu, “Ku zo ku karya kumallo”. Daga cikin almajiran kuwa babu wanda yayi karfin halin tambayarsa “Ko shi wanene?” Domin sunsani Ubangiji ne. 13Yesu zo ya dauki gurasar ya ba su, haka kuma kifin. 14Wannan shine karo na uku da Yesu ya bayyana ga almajiransa bayan tashinsa daga matattu. 15Da suka karya kumallon, Yesu yace wa Saminu Bitrus, “Bitrus dan Yahaya, kana kaunata fiye da wadannan?” Bitrus yace masa “I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka” Yesu yace masa “Ka ciyar da 'ya'yan tumakina”. 16Ya sake fada masa karo na biyu, “Saminu Dan Yahaya, kana kaunata?” Bitrus Yace masa “I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka”. Yesu yace masa, “Ka lura da Tumakina”. 17Ya sake fada masa, karo na uku, “Bitrus Dan Yahaya, kana kaunata? Sai Bitrus bai ji dadi ba domin Yesu ya fada masa karo na uku, “Kana kaunata” Yace masa, “Ubangiji ka san komai duka, ka sani ina kaunarka.” Yesu yace masa “Ka ciyar da tumaki na. 18Hakika, hakika, Ina gaya maka, lokacin da kake kuruciyarka, kakan yi wa kanka damara, ka tafi inda ka ga dama. amma in ka tsufa, zaka mike hannuwanka wani yayi maka damara, ya kai ka inda baka nufa ba.” 19To Yesu ya fadi haka ne domin ya nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi ga daukakar Allah. Bayan ya fadi haka, sai yace wa Bitrus, ka biyo ni. 20Bitrus ya juya sai ya ga almajirin da Yesu yake kauna yana biye dasu; wanda ya jingina a kirgin Yesu lokacin cin jibin nan da yace “Ya Ubangiji, wanene zai bashe ka?” 21Da Bitrus ya gan shi, yace wa Yesu “Ya Ubangiji, Me mutumin nan zai yi?” 22Yesu yace masa, “Idan ina so ya zauna har in dawo ina ruwanka? Ka biyo ni.” 23Wannan zance ya yadu cikin 'yan'uwa cewa, wannan almajirin ba zai mutu ba. Alhali Yesu bai cewa Bitrus, wannan almajirin ba zai mutu ba, Amma “Idan ina so ya zauna har in dawo ina ruwanka?” 24Wannan shine almajirin da yake shaida wadannan abubuwa, wanda ya rubuta su, kuma mun tabbata shaidarsa gaskiya ne. 25Akwai kuma sauran abubuwa da yawa wanda Yesu yayi. Idan da an rubuta kowannensu daya bayan daya, ina gaya maku, ko duniya bazata iya daukar litattafan da za a rubuta ba.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Breakfast by the Sea of Tiberias

  • Among those gathered by the Sea of Tiberias were Thomas, also called Didymus—the Greek equivalent of his Hebrew name, meaning “twin”—and Nathanael of Cana in Galilee, whose name means “gift of God.” Nathanael is named only in the Gospel of John, which never lists Bartholomew, and the two have been identified with each other. Also present were the sons of Zebedee, James and John, whose father was a Galilean fisherman with two boats and hired servants.Sources: the Bible text itself · Thomas · Nathanael · Zebedee
  • Simon Peter, who invites the others to go fishing, had been trained to that work. Three times Jesus addresses him as “Simon son of John.” Easton's Bible Dictionary (1897) says the father’s name should be read “John,” as in the Revised Version, rather than “Jonas.”Sources: the Bible text itself · Simon Peter · Jonas
  • Cana, a town of Galilee near Capernaum and Nathanael’s birthplace, is not mentioned in the Old Testament. Some have identified it with Kana el-Jelil, eight or nine miles north of Nazareth; others with Kefr Kenna, about five miles northeast of Nazareth and twelve miles in a direct line from Tiberias. Nathanael was among those to whom Jesus showed himself alive after the resurrection at the Sea of Tiberias, and the chapter calls this the third such appearance to the disciples.Sources: the Bible text itself · Cana · Nathanael

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Sea of Galilee · 32.819, 35.590 · verse 1
  • Galilee · 32.760, 35.527 · verse 2

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.