Nations Bible

John 20

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1To da sassafe ranar farko ta mako, da sauran duhu, Maryamu Magadaliya ta zo kabarin, ta tarar an kawar da dutsen daga kabarin. 2Sai ta ruga da gudu zuwa wurin Saminu Bitrus tare da almajirin nan da Yesu ke kauna, tace masu, “Sun dauke Ubangiji daga kabarin, bamu kuwa san inda aka sa shi ba.” 3Sai Bitrus tare da almajirin nan suka fita, kuma suka tafi kabarin, 4dukansu suka ruga da gudu tare, amma daya almajirin ya riga Bitrus isowa kabarin, 5Sai ya sunkuya ya leka ciki, ya ga likkafanin lillin a wurin, amma fa bai shiga ciki ba. 6Sai Saminu Bitrus ya iso daga bayansa sai ya shiga kabarin, ya tarar da likkafanin lillin a ajiye. 7sai fallen kuma da yake kansa. Ba'a ajiye tare da likkafanin ba amma aka linkeshi aka ajiye shi daban. 8Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga ya gani, sai ya ba da gaskiya. 9Har ya zuwa wannan lokacin basu san nassin daya ce zai tashi daga matattu ba. 10Sai almajiran suka sake komawa gida kuma. 11Amma Maryamu tana tsaye a bakin kabarin tana kuka. Yayin da take kuka, sai ta sunkuya ta leka cikin kabarin. 12Sai ta ga mala'iku guda biyu cikin fararen kaya zaune, daya ta wurin kai daya kuma ta wurin kafafu inda aka kwantar da Yesu. 13Sukace mata, “Uwargida don me kike kuka? Sai tace masu, “Domin sun dauke Ubangijina, ban kuwa san inda suka ajiye shi ba. 14Bayan ta fadi haka, ta juya sai ta ga Yesu tsaye a wurin. Amma bata san cewa Yesu bane, 15Yesu yace mata, “Uwargida, me yasa kike kuka? Wa kuma kike nema? Domin tana zaton shine mai kula da lambun, sai tace masa, “Maigida in kaine ka dauke shi, gaya mani inda ka sa shi, ni kuwa in dauke shi.” 16Yesu yace mata, “Maryamu”. Sai ta juya, tace masa da Armaniyanci “Rabboni!” wato mallam. 17Yesu yace mata, kada ki taba ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna, amma kije wurin 'yan'uwana kice masu, zan je wurin Ubana da Ubanku, Allahna da kuma Allahnku”. 18Maryamu Magadaliya ta je tace wa almajiran, “Na ga Ubangiji” Ta kuma ce ya fada mata wadannan abubuwa. 19Da yamma a wannan rana, a rana ta farko ta mako, almajiran suna kulle a daki saboda tsoron Yahudawa, Yesu yazo ya tsaya a tsakaninsu, yace “Salama Agareku”. 20Bayan ya fadi haka, sai ya nuna masu hannuwansa da kuibinsa. Da almajiran suka ga Ubangiji, sai suka yi farin ciki. 21Yesu ya sake ce masu, “salama agareku. “Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka Ni ma na aike ku”. 22Da Yesu ya fadi haka, sai ya hura masu lumfashinsa, yace masu, “Ku karbi Ruhu Mai Tsarki. 23Duk wanda kuka gafarta wa zunubai, an gafarta masa; kowa kuka rike zunubansa, an rikesu.” 24Toma, daya daga cikin sha biyun, wanda ake kira Dan Tagwai, baya tare dasu lokacin da Yesu ya bayyana. 25Sauran almajiran sukace masa “Mun ga Ubangiji”. Sai yace masu, “In ban ga gurbin kusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsana a gurbin kusoshin ba, in kuma sa hannuna cikin kuibinsa ba, ba zan bada gaskiya ba. 26Bayan kwana takwas har wa yau almajiran na cikin gida, Toma ma na tare dasu, kofofin suna kulle, sai ga Yesu a tsakaninsu yace, “Salama agareku”. 27Sa'an nan yace wa Toma, “Iso nan da yatsanka, dubi hannuwana. Miko hannunka kuma kasa a kuibina, kada ka zama marar bada gaskiya, sai dai, mai bada gaskiya”. 28Toma ya amsa yace “Ya Ubangijina da Allahna!” 29Yesu yace masa, “Wato saboda ka gan ni, ka bada gaskiya? Albarka ta tabbata ga wadanda basu gani ba, amma kuwa sun bada gaskiya. 30Yesu yayi wadansu alamu da yawa dabam dabam a gaban almajiransa, wadanda ba'a rubuta a littafin nan ba. 31Amma an rubuta wadannan ne, domin ku bada gaskiya Yesu shine Almasihu, Dan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai cikin sunansa.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Seeing the risen Jesus

  • Mary Magdalene’s name comes from Magdala, the place of her birth, and was used to distinguish her from the other Marys in the Gospels. Easton's Bible Dictionary (1897) treats as mistaken the common idea that she was the woman called “a sinner” in Luke 7. In this chapter she finds the stone removed, later meets Jesus, and tells the disciples, “I have seen the Lord!”Sources: Mary Magdalene · the Bible text itself
  • Thomas, one of the Twelve, was also called Didymus, the Greek equivalent of his Hebrew name, meaning “twin.” Easton's Bible Dictionary (1897) says that all we know of him is recorded in the Gospel of John. He was absent when Jesus first appeared to the disciples; he said he would not believe unless he saw the nail marks in Jesus’ hands and put his hand into his side, and eight days later he answered, “My Lord and my God!”Sources: Thomas · the Bible text itself
  • When Mary recognized Jesus, she turned and addressed him in Hebrew as “Rabboni,” which the Gospel explains means “Teacher.” At first she had mistaken him for the gardener. That evening the disciples were together with the doors locked for fear of the Jews, when Jesus stood among them and said, “Peace be with you!”Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.