Nations Bible

Acts 4

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Yayin da Bitrus da Yahaya suna kan magana da mutanen, sai firistoci da shugaban masu tsaron Haikali da kuma Sadukiyawa suka afko masu. 2Sun damu sosai domin Bitrus da Yahaya suna koyar da mutane game da Yesu kuma suna shelar tashinsa daga matattu. 3Suka kama su suka jefa kurkuku sai washegari, domin yamma ta riga ta yi. 4Amma mutane da yawa da suka ji sakon suka ba da gaskiya; kimanin mazaje dubu biyar ne kuwa suka ba da gaskiya. 5Washegari, da shugabaninsu, da dattawansu, da Marubuta suka taru a Urushalima. 6Anas babban firist, yana nan, da Kayafa, da Yahaya da Iskandari, da dukan dangin babban firist 7Da suka kawo Bitrus da Yahaya a tsakiyarsu sai suka tambaye su, “Da wanne iko, ko cikin wanne suna k ka yi haka?” 8Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Ku shugabanni da dattawan jama'a, 9idan mu yau ana tuhumarmu saboda aikin kirki da aka yi ga wannan mara lafiya - ta yaya wannan mutum ya sami lafiya? 10Bari ku da dukan mutanen Isra'ila, ku san wannan, cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda kuka giciye, wanda Allah ya tayar daga matattu ta dalilinsa ne wannan mutumin yake tsaye a gaban ku lafiyayye. 11Yesu Almasihu ne dutsen da ku magina kuka ki, amma an mai da shi kan gini. 12Babu ceto daga kowanne mutum, domin babu wani suna da aka bayar karkashin sama, a cikin mutane wanda ta wurinsa za a iya samu ceto.'' 13Sa'adda, suka ga karfin halin Bitrus da Yahaya, suka gane mutane ne talakawa marasa ilimi, sai suka yi mamaki, suka kuma lura suka gane Bitrus da Yahaya sun kasance tare da Yesu. 14Da yake suna ganin mutumin nan da aka warkar tare da su, sai suka rasa abin yi. 15Amma bayan sun fitar da manzannin daga majalisa sai suka tattauna a tsakaninsu. 16Suka ce, “Yaya za mu yi da wadannan mutane? Babu shakka aikin al'ajibi ya faru ta wurinsu, kuma sananne ne ga dukan mazauna Urushalima, kuma ba mu da iko mu musanci haka. 17Amma saboda kada ya cigaba da yaduwa cikin mutane, bari mu yi masu kashedi kada su kara magana da kowa cikin wannan suna.'' 18Suka kira Bitrus da Yahaya suka dokace su kada su kara magana ko kuma koyarwa ko kadan a cikin sunan Yesu. 19Amma Bitrus da Yahaya suka amsa suka ce, ''Ko ya yi daidai a gaban Allah mu yi maku biyayya fiye da shi, ku hukunta. 20Baza mu iya daina magana game da abubuwan da muka ji kuma muka gani ba.'' 21Bayan sun sake yi wa Bitrus da yahaya kashedi, sai suka sake su, su tafi. Domin ba su iya samu wata hujja da za su hore su a kai ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru. 22Mutumin da ya sami wannan al'ajibi na warkarwa yana sama da shekara arba'in. 23Bayan an sake su, Bitrus da Yahaya suka zo cikin mutanensu suka ba da rahoton duk abin da manyan firistoci da dattawa suka fada masu. 24Da suka ji haka, suka daga muryarsu tare ga Allah suka ce, ''Ubangiji, kai da ka yi sama da duniya da teku da duk abin da ke cikinsu, 25kai wanda ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin ubanmu Dauda bawanka, ya ce, 'Me ya sa al'ummai suka tunzura, kuma mutane suke tunanin abubuwan banza? 26Sarakunan duniya sun hada kansu tare, kuma shugabanninsu sun taru don su yi gaba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.' 27Hakika, Hiridus da Buntus Bilatus, tare da al'ummai da mutanen Isra'ila, sun taru a wannan birni domin su yi jayayya da bawanka mai tsarki Yesu, shafaffe. 28Sun taru domin su aiwatar da dukan abin da hannunka da nufinka ya shirya zai faru. 29Yanzu, Ya Ubangiji ka dubi kashedin su, ka ba bayin ka ikon furta maganar ka gabagadi. 30Sa'adda ka mika hannunka domin warkarwa, alamu da al'ajibai su faru ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu.” 31Bayan sun gama addu'a, wurin da suka taru ya girgiza, suka cika da Ruhu Mai Tsarki, suka furta maganar Allah gabagadi. 32Babban taron da suka ba da gaskiya kansu hade yake; kuma ba wanda ya ce da abinda ya mallaka nasa ne; maimakon haka, komai na su daya ne. 33Da iko mai karfi manzannin suka yi shelar shaidarsu game da tashin Yesu Ubangiji daga matattu, babban alheri kuma na bisansu. 34Babu wani a cikinsu wanda ya rasa komai, domin masu filaye da gidaje suka sayar suka kawo kudin abin da suka sayar 35sai suka kawo kudin gaban manzanni. Aka rarraba wa kowanne mutum bisa ga bukatarsa. 36Yusufu, Balawi, mutumin tsibirin Kubrus, wanda manzannisu ka yi wa lakani da suna Barnaba. (wato, mai karfafa zuciya). 37Yana da fili sai ya sayar da shi ya kawo kudin gaban manzanni.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Peter and John before the Sanhedrin

  • The priests, the captain of the temple guard, and the Sadducees seized Peter and John because they were teaching the people and proclaiming in Jesus the resurrection of the dead. Caiaphas, who sat with the assembly the next day, belonged to the Sadducees.Sources: the Bible text itself · Caiaphas
  • Annas, called high priest here, had held that office from A.D. 7 to 14 until a Roman procurator deposed him. Caiaphas, who had married Annas's daughter, was raised to the office in A.D. 25; even so, some Jews may still have regarded Annas as the legal high priest, since Mosaic law treated the office as lifelong, and Annas was probably president or deputy of the Sanhedrin. John and Alexander, relatives of the high priest and otherwise unknown, sat with them.Sources: the Bible text itself · Annas · John (Relative of the High Priest) · Alexander (Son of Simon)
  • Peter, a fisherman from Bethsaida, and John, also a fisherman and a son of Zebedee, were brought before the rulers, elders, and scribes. The council marveled at their boldness when it realized that they were unschooled, ordinary men, and took note that they had been with Jesus.Sources: the Bible text itself · Simon Peter · John the Apostle

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 5, 16
  • Nazareth · 32.702, 35.298 · verse 10
  • Cyprus · 35.000, 33.000 · verse 36

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.