Nations Bible

Acts 3

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Sa'adda Bitrus da Yahaya suna hanya zuwa haikali a lokacin addu'ar karfe uku. 2Wani mutum, gurgu ne tun daga haihuwa, ana daukar sa kulluyomi zuwa kofar haikali da ake kira Kyakkyawa, domin bara gun mutanen da ke shiga haikalin. 3Da ya ga Bitrus da Yahaya suna shiga haikalin, sai ya roke su sadaka. 4Bitrus da Yahaya kuwa suka zuba masa ido, Bitrus ya ce, ''Ka dube mu.'' 5Gurgun nan kuwa ya dube su, yana tsammanin zai sami wani abu a wurin su. 6Amma Bitrus ya ce, “Azurfa da Zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, zan baka. A cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, Yi tafiya'' 7Bitrus ya kama hannun damarsa, ya daga shi; nan da nan kafafunsa da kashin idon sawayensa suka samu karfi. 8Da gurgun ya yunkura, ya mike tsaye sai ya fara takawa; ya shiga haikali tare da Bitrus da Yahaya, yana takawa, yana tsalle, yana kuma girmama Allah. 9Dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana kuma yabon Allah. 10Sun lura cewa, shine mutumin da ke zama yana bara a Kyakyawar kofar haikali; sai suka cika da mamaki domin abin da ya faru. 11Yayin da yake rike da Bitrus da Yahaya, dukan jama'a suka matso wurinsu, a gefen dakalin Sulaimanu, suna ta mamaki kwarai. 12Da Bitrus ya ga haka ya amsa wa jama'ar, “Ya ku mutanen Isra'ila, don me ku ke mamaki?” Don me ku ka zura mana ido, kamar mu ne muka sa shi ya yi tafiya da ikon kanmu ko adalcin mu? 13Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allah na iyayenmu ya girmama bawansa Yesu. Shi kuka ki kun kuma bashe shi a gaban Bilatus da ya so ya sake shi. 14Kuka ki Mai Tsarkin nan, Mai Adalcin, maimakon haka kuka ce a sakkar maku mai kisan kai. 15Kun kashe mai ba da rai, wanda Allah ya tayar daga matattu, mu kuwa shaidu ne ga wannan al'amari. 16Yanzu, ta bangaskiya ga sunansa - wannan mutum da kuke gani kuma kun san shi - ta wurin wannan sunan ne ya sami karfi. Bangaskiya cikin Yesu ta ba shi cikakkiyar lafiya, a gabanku duka. 17Ya ku 'yan'uwa, na san kun yi haka ne cikin rashin sani, yadda shugabaninku suka yi. 18Amma duk abubuwan da Allah ya fada ta bakin dukan anabawansa, cewa Almasihunsa zai sha wahala, yanzu ya cika. 19Saboda haka, Ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, domin lokacin sabuntuwa daga wurin Ubangiji ya zo; 20domin a aiko maku da Almasihu wanda aka kaddara wato, Yesu. 21Shine wanda dole sama ta karbe shi har zuwa lokacin komo da dukan abubuwa, game da abubuwan da Allah ya fada tun da ta bakin annabawansa tsarkaka. 22Musa hakika ya ce, 'Ubangiji Allah zai tayar maku da wani annabi kamar ni daga cikin, 'yan'uwanku. Za ku saurari dukan abin da zai fada maku. 23Zai kasance kowanne mutum da bai saurari annabin nan ba za a kau da shi gabadaya daga cikin mutanensa.' 24I, dukan annabawa tun daga Sama'ila da wadanda suka zo bayansa, sun yi magana sun ambaci wadannan kwanaki. 25Kune 'ya'yan annabawa da na alkawari wanda Allah ya yi da kakanninku, yadda ya ce wa Ibrahim, 'Daga zuriyarka dukan al'uman duniya za su sami albarka.' 26Bayan da Allah ya ta da bawansa, a gareku ne ya fara aiko shi, domin ya albarkace ku tawurin juyadda kowannenku daga muguntarsa.”

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Healing and Preaching at the Temple

  • The temple gate called Beautiful, where a man lame from birth was placed each day to beg, is named in this chapter. It is supposed to have been the door from the court of the Gentiles into the court of the women, and it was massive, covered with plates of Corinthian brass.Sources: Beautiful Gate · the Bible text itself
  • After the healing, the astonished crowd ran to Peter and John in the walkway called Solomon’s Colonnade. This was a colonnade, or cloister, probably on the eastern side of the temple; it is not mentioned with the first temple, but Josephus mentions a porch of that name in Herod’s temple.Sources: Solomon's Portico · the Bible text itself
  • In his address there, Peter said the people had handed Jesus over and rejected him before Pilate, although Pilate had decided to release him. A dictionary entry identifies Pontius Pilate as the sixth Roman procurator of Judea, from A.D. 26 to 36, with headquarters at Caesarea, though he frequently went up to Jerusalem; his name comes into prominent notice in connection with the trial of Jesus.Sources: Pontius Pilate · the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Beautiful Gate · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 2, 10
  • Nazareth · 32.702, 35.298 · verse 6
  • Solomon’s Portico · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 11

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.