Nations Bible

Acts 26

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Sai Agaribas ya ce wa Bulus, “Za ka iya kare kan ka.” Sai Bulus ya daga hannunsa ya fara kare kansa. 2“Ina farinciki, ya sarki Agaribas, game da saran da Yahudawa ke kawowa a kaina yau; 3musamman ma don kai masani ne game da al'adun Yahudawa da al'amuransu. Don haka, ina rokanka ka yi hakuri ka saurare ni. 4Hakika, dukan Yahudawa sun san yadda na yi rayuwa ta daga kurciyata a kasa ta, da kuma Urushalima. 5Sun san ni tun farko, kuma yakamata su yarda cewa na yi rayuwa kamar Bafarase, darikan nan mai tsatsauran ra'ayi ta addininmu. 6Yanzu ina tsaye a nan dominn a shari'anta ni, saboda alkawalin da Allah ya yi wa ubanninmu. 7Domin wannan shine alkawalin da kabilunmu goma sha biyu suka sa zuciya su karba, yayin da suke yin sujada da himma ga Allah dare da rana. Saboda wanan bege, Sarki Agaribas, Yahudawa ke tuhuma ta. 8Me ya sa wani zai yi tunani cewa abin mamaki ne Allah ya ta da mattatu? 9Da, na yi tunanin yin abubuwa gaba da sunan Yesu Banazarat. 10Na yi wadanan a Urshalima. Na kulle masu bi da yawa a kurkuku, sanadiyar iko da na samu daga wurin manyan firistoci, kuma da ake kashe su ma, ina ba da goyon baya. 11Na wahalshe su sau dayawa a cikin dukan majamiu ina kuma yin kokari in tilasta masu su yi sabo. Na yi gaba mai zafi da su kuma na tsananta masu har zuwa birane na wadansu kasashe. 12A sa'anda nake yin wannan, na tafi Dimashku da izinin manyan firistoci; 13a cikin tafiyata kuma, da tsakar rana, ya sarki, na ga haske daga sama da ya fi rana sheki, ya haskaka kewaye da ni da kuma wadanda ke tafiya tare da ni. 14Da dukanmu muka fadi kasa, na ji wata murya na magana da ni a harshen Ibraniyawa tana cewa, 'Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani? Yana da wuya ka hauri abin da ke mai tsini.' 15Sai na ce, 'Wanene kai ya Ubangiji?' Ubangiji ya amsa, 'Ni ne Yesu wanda kake tsanantawa. 16Yanzu ka tashi tsaye domin saboda wannan dalili ne na bayyana gare ka in sanya ka, ka zama bawa da mashaidi na game da abubuwan da ka sani a kaina yanzu da wadanda zan bayyana maka daga bisani; 17Zan kubutar da kai daga wurin mutane da kuma al'ummai da zan aike ka wurinsu, 18domin ka bude idanunsu ka juyo su daga duhu zuwa haske da daga ikon Shaidan zuwa ga Allah, domin su karbi gafarar zunubai da gado da zan ba wadanda na kebe wa kaina ta wurin bangaskiya gare ni.' 19Saboda haka, sarki Agaribas, ban yi rashin biyayya da wahayin da na gani daga sama ba; 20amma, da farko ga wadanda ke a Dimashku, sa'annan a Urushalima da kasar Yahudiya gaba daya, da dukan Al'ummai, na yi wa'azi domin su tuba su kuma juyo ga Allah, su yi ayyukan da suka chanchanci tuba. 21Domin wannan dalili ne Yahudawa suka kama ni a cikin haikali kuma suke kokari su kashe ni. 22Allah ya taimake ni har wa yau, domin in iya tsayawa gaban mutane kanana da manya, in bada shaida game da iyakar abin da annabawa da Musa suka fada zai faru; 23wato lallai Almasihu zai sha wahala, ya kuma zama na farko da za'a rayar daga matattu ya kuma yi shelar haske zuwa ga mutanen Yahudawa da Al'ummai.” 24Da Bulus ya gama kare kansa, Festas ya yi magana da babban murya, “Bulus, kana hauka; yawan iliminka yasa ka hauka.” 25Amma Bulus ya ce, “Ba na hauka, ya mai girma Festas; amma da karfin zuciya nake fadi kalmomin gaskiya da na natsuwa. 26Saboda sarkin ya san wadannan abubuwa duka; shi ya sa nake magana gabagadi, don na hakikance cewa, ba abin da ke a boye gare shi; gama ba a yi wadannan abubuwa a boye ba. 27Ko ka gaskanta da annabawa, Sarki Agaribas? Na sani ka gaskanta.” 28Agaribas ya ce wa Bulus, “A cikin karamin lokaci kana so ka rinjaye ni ka mai da ni Krista?” 29Bulus ya ce, “Ina roko ga Allah, domin ko a karamin lokaci ko a dogon lokaci, ba kai kadai ba, amma har da wadanda ke sauraro na yau su zama kamar ni, amma ban da wadannan sarkokin.” 30Sai sarki ya tashi tsaye tare da gwamna da Barniki da dukan wadanda ke zaune tare da su; 31da suka bar dakin taron, suka ci gaba da magana da juna suna cewa, “Wannan mutum bai yi wani abin da ya chanchanci mutuwa ko kuma dauri ba.” 32Agaribas ya ce wa Fastos, “Da mutumin nan bai daukaka kara zuwa ga Kaisar ba da an sake shi.”

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Paul's Defense before King Agrippa

  • Easton's Bible Dictionary (1897) identifies the Agrippa of this hearing as Agrippa II, born in Rome in A.D. 27 and brother of Bernice and Drusilla. It records that the emperor Claudius made him superintendent of the Temple in Jerusalem in A.D. 48 and governor of Chalcis in A.D. 50, and later king over the tetrarchy of Philip and Lysanias. That background illuminates Paul's appeal to the king's familiarity with Jewish customs and controversies, and Bernice, Agrippa's sister, was present and rose with the king and the governor when the hearing ended.Sources: Agrippa · Bernice · the Bible text itself
  • Festus, who had succeeded Felix as procurator of Judea, heard Paul at Caesarea in the presence of Herod Agrippa II and Bernice. He found nothing deserving death or imprisonment and would have released Paul, but Paul had appealed to Caesar, so Festus sent him to Rome.Sources: Portius Festus · the Bible text itself
  • Paul tells Agrippa that about noon, on the road to Damascus, he saw a light from heaven, brighter than the sun, shining around him and his companions, and heard a voice in Hebrew calling him Saul. Damascus lies about 133 miles north of Jerusalem. Easton's Bible Dictionary (1897) says Saul was his Hebrew name and that the name Paul was probably also given to him in infancy for use in the Gentile world; he was a native of Tarsus, the capital of Cilicia, a Roman province in southeastern Asia Minor.Sources: Paul · Damascus · the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 4, 10, 20
  • Nazareth · 32.702, 35.298 · verse 9
  • Damascus · 33.511, 36.306 · verses 12, 20
  • Judea · Today: Judea 1 · 31.777, 35.234 · verse 20

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.