Nations Bible

Acts 25

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Da Festas ya shiga lardin, kuma bayan kwana uku, ya tashi daga Kaisariya ya tafi Urushalima. 2Sai babban firist da manyan Yahudawa suka kawo wa Festas sara a kan Bulus. 3Suka roki tagomashi wurin Festas ya kira Bulus zuwa Urushalima domin su kashe shi a hanya. 4Amma Festas ya amsa masu cewa, Bulus dan sarka ne a Kaisariya, kuma ba da dadewa ba shi da kansa zai koma can. 5“Saboda haka duk wadanda za su iya, su biyo mu. Idan akwai wani laifi game da mutumin, sai ku zarge shi.” 6Bayan kwana takwas ko goma, sai ya gangara zuwa Kaisariya. Washegari ya zauna bisa kursiyin shari'a ya bada umarni a kawo Bulus a gabansa. 7Da Bulus ya iso, Yahudawa daga Urushalima suka tsaya kusa, suka yi ta kawo kararraki, amma basu iya tabbatar da su ba. 8Bulus ya kare kansa ya ce, “Ban yi wa kowa laifi ba, ko Yahudawa, ko haikali, ko kuma Kaisar.” 9Amma Festas yana neman farin jini wajen Yahudawa, sabo da haka ya tambayi Bulus ya ce, “Kana so ka je Urushalima in shari'anta ka a can game da wadannan abubuwa?” 10Bulus ya ce, “Ina tsaye a Ddakalin Shari'ar Kaisar inda dole a shari'anta ni. Ban yi wa Yahudawa laifi ba, kamar yadda ka sani sosai. 11Idan lallai na yi laifi kuma na yi abin da ya chanchanci mutuwa, ban ki ba in mutu. Amma idan zarginsu karya ne, kada kowa ya bashe ni gare su. Ina daukaka kara zuwa ga Kaisar.” 12Bayan Festas ya tattauna da majalisa ya amsa ya ce, “Kana kira ga Kaisar; za ka tafi wurin Kaisar.” 13Bayan wadansu kwanaki, sarki Agaribas da Barniki suka iso Kaisariya domin su ziyarci Festas. 14Da ya kasance kwanaki da yawa, Festas ya fada wa sarki labarin Bulus ya ce, “Akwai wani mutum dan sarka da Filikus ya bari a kurkuku. 15Sa'anda nake a Urushalima, babban firist da dattawan Yahudawa suka kawo kararsa gare ni, suka roka a kashe shi. 16Game da wannan na amsa na ce masu, ba al'adar Romawa ba ce a ba da mutum tagomashi; sai wanda ake kararsa an bashi zarafi ya kare kansa a gaban masu kararsa, ya kuma bada hujjojinsa game da kararakin. 17Saboda haka, da duk suka taru ban bata lokaci ba, washegari na zauna a kujerar shari'a, na ba da umarni a kawo mutumin. 18Da masu karar suka fadi kararsu, sai na fahimci karar ba wani muhimmin abu a cikinta. 19Sai dai na ga cewa jayayya ce tsakanin su ta addini a kan wani Yesu da ya mutu, wanda Bulus ya ce yana da rai. 20Na rasa yadda zan bincike wannan al'amarin, sai na tambaye shi ko zai je Urushalima a shari'anta shi kan wadannan abubuwa. 21Amma da Bulus ya nemi a lura da shi, Kaisar ya shari'anta shi, sai na ba da umarni a ajiye shi har sai na aika shi wurin Kaisar.” 22Agaribas yace wa Festas. “Zan so ni ma in saurari mutumin nan.” “Gobe za ka ji shi,” in ji Fostus. 23Washegari Agaribas da Barniki suka zo tare da kasaitaccen taro suka shiga dakin taro tare da hafsoshi da shugabanin gari. Da Festas ya ba da umarni, aka fito da Bulus wurinsu. 24Festas ya ce, “Sarki Agaribas da dukanku da kuke tare da mu a nan, kun ga mutumin nan, dukan Yahudawa sun gana da ni a Urushalima da nan kuma. Suna mani ihu cewa, bai chanchanta a bar shi da rai ba. 25Na gane bai yi wani abin da ya chanchanci mutuwa ba; amma saboda ya daukaka kara zuwa Kaisar, na yanke shawara in aika shi. 26Amma ba ni da wani dalili na musamman da zan rubuta wasika ga Kaisar. Saboda wannan dalili na kawo shi gabanku, masamman kai ya sarki Agaribas. Domin in sami karin abin da zan rubuta game da shi. 27Gama a ganina wauta ce in aika dan sarka ba tare da na rubuta laifi a kansa ba.”

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Paul's Appeal to Caesar

  • Caesarea, on the Mediterranean about seventy miles northwest of Jerusalem, was the capital of the Roman province of Judaea and the seat of the procurators. Herod the Great built it and named it after Caesar Augustus, and Festus sat on the judgment seat there; going up to Jerusalem and down to Caesarea follows the road between that coastal capital and the mountain city.Sources: Caesarea · Jerusalem · the Bible text itself
  • Easton's Bible Dictionary (1897) identifies Festus as the procurator of Judea who succeeded Felix; a few weeks after Festus took office, the case of Paul, whom Felix had left in prison at Caesarea, was reported to him. The same dictionary says he found nothing worthy of death or bonds and would have set Paul free had Paul not appealed to Caesar; after the appeal, Festus conferred with his council and replied that Paul would go to Caesar.Sources: Portius Festus · Felix · the Bible text itself
  • Agrippa II, born in Rome and brother of Bernice, was made superintendent of the Temple in Jerusalem by the emperor Claudius and later king over the tetrarchy of Philip and Lysanias. He and Bernice came down to Caesarea to pay their respects to Festus, who, at a loss over disputes about the Jews’ own religion and about a Jesus whom Paul affirmed to be alive, brought Paul before the king so he would have definite charges to write to the emperor.Sources: Agrippa · Bernice · the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Caesarea · Today: Caesarea Maritima · 32.500, 34.892 · verses 1, 4, 6, 13, 24
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 1, 3, 7, 9, 15, 20, 24
  • Rome · 41.892, 12.485 · verses 25, 27

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.