Acts 15
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Wadansu mutane suka zo daga Yahudiya suka koyar da 'yan'uwa, cewa, “Idan ba yi maku kaciya bisa ga al'addar Musa ba, ba za ku sami ceto ba.” 2Da Bulus da Barnaba suka tunkare su da mahawara, sai 'yan'uwa suka yanke shawara Bulus da Barnaba da wasu su je Urushalima wurin manzanni da dattawa a kan wannan magana. 3Da shike iklisiya ce ta aike su, sai suka bi ta Finikiya da ta Samariya suka sanar da tuban al'ummai. Ya kawo murna mai yawa a wurin 'yan'uwa. 4Bayan sun zo Urushalima, sai iklisiya da manzanni da dattawa, suka marabce su, sai suka fada masu abin da Allah ya yi ta wurinsu. 5Amma wadansu mutane wadanda suka ba da gaskiya daga cikin Farisawa, suka tashi suka ce, “Dole ne a yi masu kaciya a kuma umarce su su kiyaye dokar Musa.” 6Sai manzanin da dattawan suka taru don su duba wannan lamari. 7Bayan mahawara mai tsanani, sai Bitrus ya tashi ya ce masu, “'Yan'uwa, kun san lokacin baya da ya wuce, Allah ya yi zabi a cikinku, cewa ta bakina ne al'ummai za su ji bishara, su kuma ba da gaskiya. 8Allah, wanda ya san zuciya, ya yi masu shaida, ya kuma basu Ruhu Mai Tsarki kamar yadda ya yi mana; 9kuma bai bambanta mu da su ba, ya tsabtace zuciyarsu ta wurin bangaskiya. 10To, saboda haka don me kuke gwada Allah, kuna sa wa almajirai nauyi a wuya wanda ubanninmu duk da mu ba mu iya dauka ba? 11Amma mun gaskanta za mu samu ceto ta wurin alherin Ubangiji Yesu, kamar yadda suke.” 12Dukan taron jama'ar suka yi shiru sa'adda suke sauraron sakon shaidar da mamakin abin da Allah ya yi ta wurin Bulus da Barnaba a cikin al'ummai. 13Bayan sun gama magana, Yakubu ya amsa, ya ce, “'Yan'uwa, ku ji ni. 14Saminu ya fada yadda Allah ya fara nuna jinkai ga al'ummai domin ya dauke jama'a daga cikinsu domin sunansa. 15Maganar annabawa ta yarda da wannan, kamar yadda yake a rubuce, 16'Bayan wadannan abubuwa zan dawo, zan gina gidan Dauda wanda ya fadi kasa; in sake gina bangonsa, in tsayar da shi, 17saboda sauran jama'a su nemi fuskar Ubangiji, har da al'ummai da ake kira da sunana. 18Wannan shine abin da Ubangiji ya fadi, shi wanda ya yi wadannan abubuwa da aka sani tun zamanin da. 19Saboda haka, a gani na kada mu matsa wa al'umman da suka juyo gun Allah; 20amma zamu rubuta masu da cewa, su guje wa gumaka da zina da faskanci da maye da cin mushe. 21Tun zamanin da akwai mutane a kowanne birni wadanda suke wa'azi da karatun Musa a majami'u kowanne Asabaci.” 22Sai ya yi wa manzanin kyau su da dattawa da dukan iklisiyar su zabi Yahuza da Barnaba da Sila da dattawan iklisiya a tura su Antakiya tare da Bulus da Barnaba. 23Sai suka rubuta wasika, “Manzani da dattawa da 'yan'uwa zuwa ga al'ummai 'yan'uwa a Antakiya da Suriya da Kilikiya, gaisuwa mai yawa. 24Mun ji cewa wasu mutane daga cikinmu wadanda ba mu umarce su ba, sun fita daga cikinmu sun yi maku koyarwar da ta daga maku hankali. 25Ya yi kyau da dukanmu, muka amince mu zabi wadansu mutane mu tura su wurinku tare da Bulus da Barnaba, 26mutane wadanda suka sadaukar da ransu domin sunan Ubangiji Yesu Almasihu. 27Mun aika Yahuza da Sila su gaya maku wadannan abubuwa. 28Saboda haka ya yi kyau Ruhu Mai Tsarki da mu, kada mu sa maku nauyi fiye da wadannan abubuwan: 29ku bar yi wa gumaka hadaya, ku bar cin mushe da shan kayan maye da zina da faskanci, in kun kiyaye wadannan abubuwa za ku zauna lafiya. Ku huta lafiya.” 30Da aka sallame su, sai suka je Antakiya. Bayan sun tara jama'a sai suka ba su wasikar. 31Bayan da suka karanta ta, sai suka yi murna sosai saboda karfafawa. 32Yahuza da Sila, da shike su annabawa ne, suka karfafa 'yan'uwa da kalmomi masu yawa. 33Bayan sun yi kwananki a wurin, sai aka sallame su zuwa wurin 'yan'uwa wadanda suka aiko su. 34Amma ya gamshe Sila ya zauna a wurin. 35Amma Bulus da Barnaba suka tsaya a Antakiya da sauran 'yan'uwa, suna koyar da maganar Ubangiji. 36Bayan kwanaki kadan Bulus ya ce ma Barnaba, “Mu koma yanzu mu ziyarci dukan 'yan'uwa da muka yi masu bisharar Ubangiji, mu ga yadda suke. 37Barnaba yana so su dauki Yahaya wanda kuma ake kira Markus. 38Amma Bulus ya yi tunanin bai kamata a tafi da Markus ba, tun da ya bar su a Bamfiliya bai ci gaba da su ba. 39Nan jayayya ta tashi tsakaninsu, har suka rabu da juna sai Barnaba ya tafi tare da Markus suka ketare zuwa Kuburus. 40Amma Bulus ya zabi Sila suka tafi, bayan 'yan'uwa sun yi masu addu'ar alherin Allah ya kiyaye su. 41Bulus ya tafi ya zazzaga Suriya da Kilikiya yana ta karfafa iklisiyoyin.

Did you know?
The Council on Gentile Believers
- The dispute began in Antioch, on the Orontes about three hundred miles north of Jerusalem, then ranked third among the cities of the Roman empire, after Rome and Alexandria. On the way to the council, Paul and Barnabas passed through Phoenicia, a coastal strip about one hundred twenty miles long, and through Samaria. A chronological note dates the Jerusalem Council to AD 46.Sources: Antioch (Syria) · Phenicia · the Bible text itself · Jerusalem Council
- Easton's Bible Dictionary (1897) says that James, whom it calls the brother or near kinsman of Jesus, headed the church in Jerusalem and presided at the council on the Gentiles. The letter that followed was addressed to Gentile believers in Antioch, Syria, and Cilicia. Cilicia, Paul's home province and a maritime Roman province in the southeast of Asia Minor since 67 BC, included his native city of Tarsus.Sources: James (Brother of Jesus) · the Bible text itself · Cilicia · Paul
- Judas, called Barsabbas, and Silas, also known as Silvanus, were prophets and leading men of the Jerusalem church, sent to confirm the council's decision in person. A later sharp disagreement over John Mark, cousin of Barnabas, separated the two missionaries: Barnabas took Mark and sailed for Cyprus, while Paul chose Silas. A chronological note dates that parting to AD 47.Sources: the Bible text itself · Silas · John Mark · Paul and Barnabas part ways
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Antioch · Today: Antioch on the Orontes · 36.227, 36.172 · verses 1, 22, 23, 30, 35
- Judea · Today: Judea 1 · 31.777, 35.234 · verse 1
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 2, 3, 4, 22, 23, 33
- Phoenicia · 33.271, 35.196 · verse 3
- Samaria · Today: Samaria 2 · 32.276, 35.195 · verse 3
- Cilicia · 36.913, 34.892 · verses 23, 41
- Syria · Today: Syria 2 · 33.511, 36.306 · verses 23, 41
- Pamphylia · 37.000, 31.000 · verse 38
- Cyprus · 35.000, 33.000 · verse 39
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org