Acts 14
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1A lokacin da Bulus da Barnaba sun shiga garin Ikoniya suka shiga majami'an Yahudawa suka yi wa'azi yadda har mutane da yawa daga cikin Yahudawa da Hellinawa suka ba da gaskiya. 2Amma Yahudawa da basu yi biyayya ba, suka zuga al'umman har suka yi fushi da 'yan'uwan. 3Suka zauna a wurin na tsawon lokaci, suna yni maganarsu gabagadi da ikon Ubangiji, yana kuma shaidar sakon alherinsa. Ya yi wannan ta wurin alamu da al'ajibai ta hannun Bulus da Barnaba. 4Saboda haka mutanen garin sun rabu: wadansun su suka bi ra'ayin Yahudawa, wasu kuwa sun bi manzannin. 5Al'umman garin da Yahudawa sun nemi jan hankali shugabanninsu, don su wulakanta Bulus da Barnaba, su jajjefe su, 6da suka gane haka suka gudu zuwa biranen Likoniya, Listira da Darbe, da garuruwa wadanda ke kewaye da su, 7a can suka yi wa'azin bishara. 8A Listira akwai wani wanda ke zaune bai taba tashi da kafafunsa ba, don shi gurgu ne tun daga haihuwa. 9Wannan mutumin ya ji Bulus yana magana. Bulus ya kafa masa ido, ya gane mutumin na da bangaskiya da za a warkar da shi. Sai ya ce masa da murya mai karfi, “Tashi ka tsaya akan kafafunka” 10Sai mutumin ya yi tsalle ya fara tafiya da kafafunsa, yana yawo. 11Da jama'an garin sun ga abin da Bulus ya yi, suka tada muryarsu suna cewa da Likoniyanci, “Ai alloli sun ziyarce mu daga sama, da kamanin mutane.” 12Suna kiran Barnaba da sunan “Zafsa,” Bulus kuwa suka kira shi da sunan “Hamisa” domin shine yafi yin magana. 13Sai firist din zafsa wanda dakin yin masa sujada na kofar birni; ya kawo bijimai biyu da furannin da aka saka su kamar gammo; shi da jama'arsa suna so su yi masa hadaya. 14Amma da manzannin, wato Barnaba da Bulus, su ka ji labarin, suka yage rigunansu, suka hanzarta zuwa gun taron mutanen. 15Suna ta cewa, “Kuji! Ku mutane don me kuke wannan abin? Mu fa mutane ne kamarku. Mun kawo maku labari mai dadi ne, da cewa, ku rabu da abubuwa marar amfani, ku koma ga Allah mai rai, wanda ya hallici sama da kasa da teku da dukan abubuwa da ke cikinsu. 16A da dai ya bar mutane su yi abinda suka ga dama. 17Duk da haka, bai bar kansa ba tare da shaida ba, don yana bada abubuwa masu kyau, yana ba ku ruwan sama, lokatai masu albarka, ya cika ranku da abinci da farin ciki.” 18Duk da wadannan kalmomin da kyar, Bulus da Barnaba suka iya tsayar da su daga yi masu hadaya. 19Amma wasu Yahudawa daga Antakiya da wasunsu daga Ikoniya suka rinjayi tarun jama'ar. Suka jajjefi Bulus suka ja shi zuwa wajen garin, suna ganin kamar ya mutu. 20Duk da haka da almajirai suka kewaye shi a tsaitsaye, sai ya tashi ya koma cikin garin. Washegari, ya tafi Darba tare Barnaba. 21Bayan sun yi wa'azin bishara a wannan birnin suka kuma sami almajirai da yawa, suka dawo Listira, da Ikoniya da Antikiya. 22Suna karfafa zuciyar almajiran su rike bangaskiyarsu, su ci gaba da ita, suna ce masu, “Ta wurin jimrewa mai yawa zamu shiga mulkin Allah, don haka dole ne mu sha wahala.” 23Da suka zabar masu dattawa a kowace iklisiya, sai suka yi addu'oi da azumi, suka mika su ga Ubangiji, ga wanda suka gaskanta a gareshi. 24Sa'annan sun bi ta Bisidiya suka kai Bamfiliya. 25Da suka yi maganarsu a Biriya, sun wuce zuwa har Italiya. 26Ta jirgin ruwa zuwa Antakiya, a nan ne aka mika su ga alherin Allah don aikin da suka gama a yanzu. 27Da isowarsu Antakiya sun tara 'yan iklisiya a wuri daya, sun ba da labarin dukan abin da Allah ya yi ta wurinsu. Da yadda Ya bude kofa a wurin al'ummai ta bangaskiya. 28Sun zauna tare da almajiran na tsawon lokaci.

Did you know?
Paul and Barnabas in Lycaonia
- Iconium was the capital of Lycaonia, an inland Roman province of Asia Minor whose chief towns were Iconium, Lystra, and Derbe. Easton's Bible Dictionary (1897) places Iconium, the modern Konieh, at the foot of Mount Taurus, about 120 miles inland; Lystra lay in a wild district, and Derbe was a small town about twenty miles from Lystra, on the eastern part of the upland plain.Sources: Iconium · Lycaonia · Lystra · Derbe
- When a man lame from birth began to walk, the crowds at Lystra shouted in the Lycaonian language that the gods had come down in human form, calling Barnabas Zeus and Paul Hermes because Paul was the chief speaker. Easton's Bible Dictionary (1897) uses the Roman names Jupiter and Mercury, and says Barnabas was probably taken for Jupiter because of a stately, venerable appearance; of the local speech, it says the language was probably ancient Assyrian, though others have thought it a corrupt Greek mixed with Syriac words.Sources: the Bible text itself · Lystra · Lycaonia
- This passage through Lycaonia belongs to Paul's first missionary journey, which a timeline dates to AD 45 and about a year. Easton's Bible Dictionary (1897) notes that Paul did not suffer persecution at Derbe; from there he and Barnabas returned to Lystra, Iconium, and Pisidian Antioch to strengthen the disciples and appoint elders, then passed on through Pisidia.Sources: First Missionary Journey · Derbe · Antioch (Pisidia) · the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Iconium · Today: Konya · 37.872, 32.492 · verses 1, 19, 21
- Lycaonia · 38.000, 33.000 · verses 6, 11
- Lystra · Today: Tel Lystra · 37.602, 32.338 · verses 6, 8, 21
- Antioch · Today: Antioch in Pisidia · 38.306, 31.189 · verses 19, 21
- Pamphylia · 37.000, 31.000 · verse 24
- Pisidia · 38.306, 31.189 · verse 24
- Attalia · Today: Antalya · 36.881, 30.704 · verses 25, 26
- Perga · 36.960, 30.854 · verse 25
- Antioch · Today: Antioch on the Orontes · 36.227, 36.172 · verses 26, 27
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org