Nations Bible

2 Corinthians 3

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Muna fara sake yabon kanmu ne? Ba mu bukatar wasikun shaida daga gare ku ko zuwa gare ku, kamar wadansu mutane, ko ba haka ba? 2Ku da kanku kune wasikar shaidarmu, wadda aka rubuta a zukatanmu, wadda Kuma dukan mutane suka sani suke kuma karantawa. 3Kuma kun nuna ku wasika ne daga Almasihu, wadda muka isar. Ba da tawada aka rubuta ta ba amma da Ruhun Allah mai rai. Ba bisa allunan duwatsu aka rubuta ta ba, amma bisa allunan zukatan mutane. 4Gama wannan ne gabagadin da muke da shi cikin Allah ta wurin Almasihu. 5Ba mu da wata gwanintar kanmu da za mu yi takamar wani abu ya zo daga gare mu. Maimakon haka, gwanintar mu daga Allah take. 6Allah ne ya maishe mu kwararrun bayi na sabon alkawari. Wannan alkawari ne ba na rubutu ba amma na Ruhu. Gama rubutu kisa yake yi, amma Ruhu rai yake bayarwa. 7To hidimar da ta haifar da mutuwa- wadda aka rubuta bisa duwatsu- ta zo cikin irin wannan daukaka da har Israila ba su iya kallon fuskar Musa kai tsaye ba. Wannan kuwa saboda daukakar da ke fuskarsa ne, daukaka mai shudewa. 8Ina misalin girman daukakar hidimar da Ruhu ke yi? 9Gama idan hidimar kayarwa tana da daukaka, ina misalin yalwatar daukaka da hidimar adalchi za ta yi! 10Babu shakka, abin da aka maishe shi mai daukaka a da, ba ya da sauran daukaka a wannan fanni, saboda irin daukakar da ta zarce shi. 11To idan har mai shudewar nan ya na da daukaka, ina misalin daukakar da abu na dindindin zai samu! 12Dashike muna da wannan tabbaci, muna da gabagadi sosai. 13Ba kamar Musa muke ba wanda ya sa mayafi ya rufe fuskarsa, ta yadda mutanen Isra'ila basu iya kallon karshen daukaka mai shudewa ba kai tsaye. 14Amma tunaninsu ya zama a rufe. Har yau kuwa mayafin na nan sa'adda ake karanta tsohon alkawari. Ba a bude shi ba, saboda a cikin Almasihu ne kadai ake kawar da shi. 15Amma har yau, duk lokacin da ake karanta littafin Musa, akwai mayafi shimfide a zukatansu. 16Amma sa'adda mutum ya juyo wurin Ubangiji, an kawar da mayafin. 17To Ubangiji shine Ruhun. Inda Ruhun Ubangiji yake, akwai 'yanci. 18Dukan mu yanzu, da fuskoki marasa mayafi, muna ganin daukakar Ubangiji. Muna samun sakewa zuwa cikin irin wannan daukaka, daga wannan mataki na daukaka zuwa wani matakin, kamar dai daga wurin Ubangiji, wanda shine Ruhun.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

A More Glorious Covenant

  • The chapter asks whether letters of recommendation to or from the believers are needed, as some people require. It answers that the believers themselves are a letter from Christ, the result of this ministry, inscribed on the ministers' hearts and known and read by everyone.Sources: the Bible text itself
  • The chapter contrasts ink and tablets of stone with the Spirit of the living God writing on human hearts. It calls the ministry engraved in letters on stone a ministry of death and condemnation, and describes a new covenant of the Spirit, for the letter kills but the Spirit gives life.Sources: the Bible text itself
  • The Israelites could not gaze at Moses's face because of a glory that was fading, and Moses put a veil over his face so they would not look at the end of what was passing away. The chapter says that a veil still covers their hearts when Moses is read, and that it is taken away whenever anyone turns to the Lord.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.