2 Corinthians 2
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Don haka na yanke shawara daga bangarena, ba zan sake zuwa wurin ku cikin yanayi mai tsanani ba. 2Idan na bata maku rai, wa zai karfafa ni, in ba shi wanda na bata wa rai ba? 3Na rubuto maku kamar yadda na yi domin idan na zo gareku kada in sami bacin rai a wurin wadanda ya kamata su faranta mani rai. Ina da gabagadi game da dukan ku, cewa farincikin da nake da shi, shine kuke da shi duka. 4Domin kuwa na rubuto maku cikin kunci da bacin rai da kuma hawaye mai yawa. Ba zan so in sake bata maku rai ba. Maimakon haka, na so ku san zurfin kaunar da nake da ita domin ku. 5Idan wani ya kawo sanadin bacin rai, ba ni kadai ya kawo wa wannan abin ba, amma ta wani fannin- domin kada a tsananta- har a gare ku duka. 6Hukuncin nan da galibinku kuka yi wa mutumin nan ya isa. 7Don haka, yanzu a maimakon hukunci, ku gafarta masa, ku kuma ta'azantar da shi. Ku yi haka domin kada bakinciki mai yawa ya danne shi. 8Don haka ina karfafa ku da ku nuna irin kaunar da kuke yi masa a fili. 9Wannan shine dalilin da ya sa na rubuto maku, domin in gwada ku, ko kuna biyayya cikin komai. 10Duk mutumin da kuka gafarta wa, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta-idan na gafarta wani abu-an gafarta ne domin ku a gaban Almasihu. 11Wannan ya zama haka ne domin kada shaidan ya yaudare mu. Don ba mu jahilci irin makircinsa ba. 12Na samu budaddiyar kofa daga wurin Ubangiji yayin da nazo birnin Tarwasa, in yi wa'azin bisharar Almasihu a can. 13Duk da haka, raina bai kwanta ba, domin ban ga dan'uwana Titus a can ba. Sai na bar su a can, na dawo Makidoniya. 14Amma godiya ta tabbata ga Allah, wanda cikin Almasihu yake kai mu ga nasara a koyaushe. Ta wurin mu ya baza kamshi mai dadi na saninsa ko'ina. 15Gama mu, kamshi ne mai dadi na Almasihu ga Allah, a tsakanin wadanda ake ceton su, da kuma tsakanin wadanda suke hallaka. 16Ga mutanen da suke hallaka, kamshi ne daga mutuwa zuwa mutuwa. Ga wadanda suke samun ceto kuma kamshi ne daga rai zuwa rai. Wanene ya cancanci wadannan abubuwan? 17Gama mu ba kamar sauran mutane muke ba, masu sayar da maganar Allah domin samun riba. Maimakon haka, da tsarkakkiyar manufa, muke magana cikin Almasihu, kamar yadda Allah ya aiko mu, a gaban Allah.

Did you know?
Tears, Forgiveness, and the Journey through Troas
- Paul writes that he went to Troas to preach the gospel of Christ and that a door stood open for him in the Lord, yet he had no peace in his spirit because he did not find Titus there, so he said goodbye and went on to Macedonia. Troas was a city on the coast of Mysia, in the northwest of Asia Minor, named after ancient Troy, which lay about four miles to the north. In New Testament times Macedonia was a Roman province lying north of Greece.Sources: the Bible text itself · Troas · Macedonia
- Titus, whom Paul calls his brother, is the companion he did not find at Troas. He appears to have been a Gentile and was chiefly engaged in ministering to Gentiles. Paul sent him from Ephesus, where he was with Paul and Timothy, to Corinth to forward the church's contribution for the poor in Jerusalem.Sources: the Bible text itself · Titus
- Paul urges them to forgive and comfort the person who caused grief, so that he will not be overwhelmed by excessive sorrow, and so that Satan will not outwit them, since they are not unaware of his schemes. Satan means adversary or accuser. In the New Testament the name is used interchangeably with the devil, and it is so used more than thirty times.Sources: the Bible text itself · Satan
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org