2 Corinthians 12
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Dole ne in yi fahariya, ko dashike bata da ribar komai. Amma zan ci gaba da wahayoyi da ruyoyi daga Ubangiji. 2Na san wani mutum cikin Almasihu, wanda shekaru goma sha hudu da suka wuce-ko a cikin jiki ne ko ba a jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani-an dauke shi zuwa sama ta uku. 3Kuma na san wannan mutumin-ko cikin jiki ko kuma ba cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani- 4an dauke shi zuwa Firdausi ya kuma ji madaukakan al'amura wadanda ba mai iya fadi. 5A madadin irin wannan mutumin zan yi fahariya. Amma a madadin kaina ba zan yi fahariya ba, sai dai game da kumamancina. 6Idan ina so inyi takama, ba zai zama wauta ba, domin gaskiya zan rika fada. Amma zan guje wa fahariya, domin kada wani ya dauke ni fiye da abinda ya gani ko ya ji daga gare ni. 7Zan kuma gujewa fahariya saboda irin wadannan gagaruman ruyoyi. Domin kada in cika da girman kai, an ba ni kaya cikin jikina, manzon shaidan ya wahalshe ni, domin kada in yi girman kai dayawa. 8Na roki Ubangiji har sau uku domin ya kawar mini da wannan. 9Amma ya ce mani, “Alherina isasshe yake a gare ka, domin ta wurin kumamanci karfi yake cika.” Don haka zan gwammace takama a akan kasawata, domin ikon Almasihu ya zauna a ciki na. 10Sabili da haka a gamshe nake ta dalilin Almasihu, cikin kumamanci, ko raini, ko matsaloli, ko jarabobi, ko kuma nawaya. Don ko dayaushe na raunana, ina da karfi kuma. 11Na zama wawa! Amma ku ne kuka tilasta mani haka, ya kamata ku yabe ni, domin ban kasa ga wadan da ake kira manyan manzanni ba, ko da shike ni ba komai ba ne. 12Cikakkun alamun mazanni sun faru a tsakanin ku, da cikakken hakuri, alamu da abubuwan ban mamaki da manyan ayyuka. 13Ta yaya kuka zama da rashin muhimmanci akan sauran Ikkilisiyoyin, sai dai don ban zama matsala a gare ku ba? Ku gafarce ni a kan wannan laifin. 14Duba! A shirye nake domin in zo gare ku karo na uku. Ba zan so in zamar maku nawaya ba, domin ba kayanku nake so ba. Amma ku nake so. Domin ba 'ya'ya ne ya kamata su yi wa iyaye tanadi ba. Amma iyaye ne ya kamata su yi wa 'ya'ya tanadi. 15Zan yi murnar biyan bukatunku, ko ya kai ga in bada rai na. Idan ni na kaunace ku, sosai, sai ni za a kaunata kadan? 16Amma kamar yadda yake, ban nawaita maku ba. Amma, da shike ni mai dabara ne, Ni ne na kama ku da yaudara. 17Ko na cutar da ku ta wurin wadanda na turo maku? 18Rokar Titus na yi domin ya zo gare ku, sa'an nan na turo shi da wani dan'uwa. Ko da na turo Titus, ya cutar da ku ne, ba cikin hanya daya muka yi tafiya ba? Ba a sawu daya muka yi tafiya ba? 19Kuna tsammanin a dukan wannan lokaci muna kare kan mu a gaban ku ne? A gaban Allah, a cikin Almasihu muke fadin komai domin ku sami karfi. 20Ina tsoro domin idan na zo ba zan same ku yadda nake zato ba. Ina tsoro kuma ba za ku same ni kamar yadda ku ke zato ba. Ina tsoron cewa za a sami gardandami, kishi, barkewar fushi, buri na son kai, gulma, girman kai da yamutsi. 21Ina tsoron cewa bayan na dawo, Allahna zai iya kaskantar da ni a gaban ku. Ina tsoron cewa zan yi bakinciki domin mutane dayawa da suka yi zunubi kafin yanzu, wadanda kuma ba su tuba daga rashin tsarki da zina da fasikanci da ayyukan sha'awa da suka aikata ba.

Did you know?
Revelations, a thorn, and Titus's visit
- This chapter tells of a man in Christ who, fourteen years earlier, was caught up to the third heaven and to Paradise and heard things too sacred for words, which a person is not permitted to tell. Paul says he will boast about that man, not about himself, except in his weaknesses; he also says that, because of these surpassingly great revelations, he was given a thorn in the flesh, which he never names.Sources: the Bible text itself
- Paul calls the thorn a messenger of Satan, given to torment him, and says he pleaded with the Lord three times that it be taken away. The name Satan means adversary or accuser; Easton's Bible Dictionary (1897) notes that in the New Testament it is used interchangeably with the devil, and is so used more than thirty times.Sources: the Bible text itself · Satan
- Paul says he urged Titus to visit them and sent our brother with him, then asks whether Titus exploited them in any way. Easton's Bible Dictionary (1897) says Titus appears to have been a Gentile whom Paul refused to have circumcised, and that Paul sent him from Ephesus to Corinth to forward the church's collection for the poor saints in Jerusalem.Sources: the Bible text itself · Titus
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org