Nations Bible

2 Corinthians 11

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Ina fatan za ku jure da ni cikin wauta kadan. Ko da yake lallai kuna jurewa da ni! 2Domin ina kishi sabili da ku. Kishi na kuwa irin na Allah ne domin ku. Tun da na alkawartar da ku a cikin aure ga miji daya. Na kuma yi alkawarin in gabatar da ku kamar budurwa mai tsarki ga Almasihu. 3Gama ina fargaba a kan ku, ko watakila, kamar yadda macijin ya yaudari Hauwa'u ta wurin kissarsa, Ya zamana tunaninku ya kauce daga sahihiyar sadaukarwa ga Almasihu. 4Anar misali idan wani ya zo ya kawo shelar wani Yesu daban da wanda muka yi maku wa'azinsa. Ko kuma kun karbi wani ruhu daban da wanda muka karba. Ko kuma kun karbi wata bishara daban da wadda muka karba. Amincewar da kuka yi wa wadannan abubuwa ta isa! 5Don kuwa ina tsammanin ba a baya nake ba ga sauran wadanda ake kira manyan manzanni. 6To ko ma ba a ilimantar da ni ba akan yin jawabi, ban rasa horarwar ilimi ba. Ta kowace hanya kuma cikin abubuwa duka mun sanar da ku wannan. 7Na yi zunubi ne da na kaskantar da kai na domin a daukaka ku? Domin na yi maku wa'azin bisharar Allah kyauta. 8Na yi wa sauran Ikilisiyoyi kwace ta wurin karbar gudummuwa daga wurin su domin inyi maku hidima. 9Lokacin da ina tare da ku kuma na sami kai na cikin bukata, ban dora wa kowa nauyi ba. Domin 'yan'uwa da suka zo daga Makidoniya sun biya bukatuna. A cikin komai na kebe kaina daga zama nawaya a gare ku, kuma zan cigaba da yin haka. 10Kamar yadda gaskiyar Almasihu ke ciki na, ba zan yi shiru da wannan fahariya tawa ba a cikin dukan kasar Akaya. 11Don me? Saboda ba na kaunar ku? Allah ya sani. 12Amma abinda na ke yi, zan cigaba da yi. Zan yi haka ne domin in yanke zarafin wadanda ke son samun zarafi kamar mu akan abubuwan da suke fahariya da shi. 13Don irin wadannan mutane manzannin karya ne masu aikin yaudara. Suna badda kama kamar manzannin Almasihu. 14Wannan ba abin mamaki ba ne, domin shaidan ma yakan badda kama ya fito kamar mala'ikan haske. 15Ba wani babban abin mamaki ba ne idan bayin sa sun badda kamanninsu don a dauka bayin adalci ne su. Karshen su zai zama sakamakon abin da suka aikata. 16Ina kara fadi: Kada wani ya yi zaton ni wawa ne. Idan kun yi zaton hakan, to ku dauke ni kamar wawan don inyi fahariya kadan. 17Abinda nake fadi game da wannan gabagadi mai fahariya ba bisa ga amincewar Ubangiji ba ne, amma ina magana a matsayin wawa. 18Tun da mutane dayawa suna fahariya bisa ga jiki, ni ma zan yi fahariya. 19Gama kuna murnar tarayya da wawaye. Ku masu hikima ne! 20Kuma kuna hakuri da wanda zai bautar da ku, idan ya tauye ku, yana amfani da ku don ribar kansa, idan ya dauki kansa fiye da ku, ko ya mammare ku a fuska. 21Ina mai cewa mun kunyata da muka rasa gabagadin yi maku haka. Duk da haka idan wani zai yi fahariya-Ina magana kamar wawa-Ni ma zan yi fahariya. 22Su yahudawa ne? Ni ma haka. Su Isra'ilawa ne? Nima haka. Su zuriyar Ibrahim ne? Nima haka. 23Su bayin Almasihu ne? (Ina magana kamar ba ni cikin hankalina) na fi su ma. Na ma yi aiki tukuru fiye da su duka, shiga kurkuku fiye da kowa, a shan duka babu misali, a fuskantar haduran mutuwa da yawa. 24Daga hannun yahudawa sau biyar na sha bulala ''Arba'in ba daya''. 25Sau uku na sha dibga da sanduna. Sau daya aka jejjefe ni da duwatsu. Sau uku na yi hadari a jirgin ruwa. Na yi tsawon dare da yini guda a tsakiyar teku. 26Ina shan tafiye tafiye, cikin hadarin koguna, cikin hadarin 'yan fashi, cikin hadari daga mutane na, cikin hadari daga al'ummai, cikin hadarin birni, cikin hadarin jeji, cikin hadarin teku, cikin hadarin 'yan'uwan karya. 27Na sami kaina ina aiki tukuru cikin mawuyacin hali, cikin yin dare dayawa ba barci, cikin yunwa da kishin ruwa, cikin yawan azumi, cikin sanyi da tsiraici. 28Baya ga wadannan duka, akwai nauyi a kaina kullayaumin saboda damuwata akan Ikkilisiyoyi duka. 29Waye kumama, wanda ban zama kumama akan shi ba? Wanene aka sa yayi tuntube, kuma ban kuna ba? 30Idan zan yi fahariya, zan yi fahariya akan abinda ke nuna kasawata. 31Allah kuma Uba na Ubangijinmu Yesu, wanda ya isa yabo har abada, ya san ba karya nake yi ba! 32A Damasku, gwamnan da ke mulki karkashin sarki Aritas yasa aka yi tsaron birnin Damasku domin a kama ni. 33Amma ta taga cikin kwando aka ziraro ni bayan ganuwar birni, na kuwa kucce daga hannunsa.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Foolish Boasting and False Apostles

  • The chapter closes with Paul's escape from Damascus, where the governor under King Aretas had the city guarded in order to arrest him, and he was lowered in a basket through a window in the wall. Easton's Bible Dictionary (1897) identifies Aretas as king of Arabia Petraea and says that, after the emperor Tiberius died in A.D. 37, Aretas took possession of Damascus, when Paul returned there from Arabia. The same dictionary calls Damascus the most ancient of Oriental cities and the capital of Syria, about 133 miles north of Jerusalem.Sources: the Bible text itself · Aretas · Damascus
  • Paul says that when he was with them and in need, he was a burden to no one, because brothers who came from Macedonia supplied his needs, and that this boast will not be silenced in the regions of Achaia. In New Testament times Macedonia was a Roman province north of Greece, governed by a propraetor with the title of proconsul. Achaia, in the sense in which the name is used in the New Testament, was the other Roman province, covering the Peloponnesus and the south of Greece.Sources: the Bible text itself · Macedonia · Achaia
  • Paul fears that his readers' minds may be led astray from their simple and pure devotion to Christ, just as Eve was deceived by the serpent's cunning, and he warns that false apostles masquerade as apostles of Christ. He adds that this is no wonder, for Satan himself masquerades as an angel of light, and his servants as servants of righteousness. A dictionary entry notes that Satan, meaning adversary or accuser, is also called the old serpent and, in this same letter, the god of this world.Sources: the Bible text itself · Satan

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Macedonia · 41.600, 22.540 · verse 9
  • Achaia · 38.720, 22.540 · verse 10
  • Damascus · 33.511, 36.306 · verse 32

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.