1 Corinthians 11
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Ku yi koyi da ni, kamar yadda nake koyi da Almasihu. 2Yanzu ina yaba maku ne, don kuna tunawa da ni cikin abu duka. Ina kuma yaba maku wajen bin al'adun da na ba ku daidai yadda na ba ku. 3Amma fa ina son ku fahimta da cewa, shugaban kowane mutum Almasihu ne, shugaban kowace mace mutumin ne, shugaban Almasihu Allah ne. 4Kuma duk mutumin da ya yi addu'a ko annabci kansa a rufe, ya wulakanta shugabansa. 5Amma duk macen da ta yi addu'a ko annabci kanta a bude, ta wulakanta shugabanta. Gama yayi dai dai da idan tayi aski. 6Gama idan mace ba zata rufe kanta ba, to ta yanke gashinta ya zama gajere. Idan abin kunya ne mace ta yanke gashinta ko ta aske kanta, bari ta rufe kanta. 7Bai kamata na miji ya rufe kansa ba, tun da yake shi siffa ne da daukakar Allah. Amma mace daukakar namiji ce. 8Don kuwa namiji ba daga jikin mace yake ba. A maimako, matar daga jikin namiji take. 9Ba a kuma halicci namiji don mace ba. A maimako, an halicci mace don namiji. 10Shi ya sa mace za ta kasance da alamar iko a kanta, saboda mala'iku. 11Duk da haka, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, haka kuma namiji ba a rabe yake da mace ba. 12Kamar yadda mace take daga namiji, haka ma namiji kuma haihuwar mace ne. Amma dukkan abubuwa daga Allah suke. 13Ku hukunta da kanku: Daidai ne mace ta yi addu'a ga Allah kanta a bude? 14Ashe, ko dabi'a bata nuna maku cewa abin kunya ne namiji, ya kasance da dogon gashi ba? 15Ba dabi'a ta koya maku cewa idan mace tana da dogon gashi, daukakar ta ne ba? Gama domin rufewa aka yi mata baiwar gashin. 16To idan wani yana da niyyaryin gardama game da wannan, mu dai bamu da wata al'adar, ikilisiyoyin Allah kuma haka. 17Amma game da umarnin dake biye, ban yaba maku ba, taruwarku ba ta kirki ba ce, ta rashin gaskiya ce. 18Farko dai sa'adda kuke, taron ikklisiya, na ji har akwai rarrabuwa tsakaninku, har na fara amincewa da maganar. 19Dole ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya gane wadanda suke amintattu a cikinku. 20Domin, in kun taru a wuri daya, ba jibin Ubangiji kuke ci ba! 21Ya yin da kuke ci, kowa na cin abincinsa ne kamin sauran Wani yana jin yunwa, wani kuma ya zarin ci, har ya bugu. 22Baku da gidajen da zaku ci ku sha, kuna raina ikkilisiyar Allah, kuna kuma wulakanta wa wadanda basu da komai? To, me zan ce maku? Yaba maku zan yi? Ba zan yaba maku ba akan wannan. 23Amma abin da na karba a gun Ubangiji shi nake baku cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi ya dauki gurasa. 24Bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “wanna shi ne jikina wanda yake saboda ku, ku yi domin tunawa da ni.” 25Ta wannan hanya kuma, sai ya dauki kokon, ya ce, “kokon nan na sabon alkawari ne, da aka tabbatar da shi da cikin jinina. Ku yi haka kuna sha don tunawa da ni.” 26Duk sa'adda kuke cin gurasar nan, kuna kuma sha cikin kokon nan, kuna bayyana mutuwar Ubangiji ke nan, har sai ya dawo. 27Saboda haka duk wanda ya ci gurasar nan, ko ya sha a cikin kokon nan, na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulakanta jikin Ubangiji da jininsa. 28Sai kowa ya fara auna kansa, kafin ya ci gurasar, ya kuma sha a cikin kokon nan. 29In kowa ya ci, ya sha ba tare da rarrabewa da jikin Ubangiji ba, lalle ya jawowa kansa hukunci, ta wurin ci da sha da ya yi. 30Shi ya sa da yawa a cikin ku suke raunana, kuma suna fama da rashin lafiya, har ma wasun ku da dama suka yi barci. 31Amma, in mun auna kanmu, ba a za a hukunta mu ba. 32In kuwa Ubangiji ne ya ke hukunta mu, To, muna horuwa ke nan, don kada a kayar damu tare da duniya. 33Saboda haka, ya ku 'yan'uwana, idan kuka tattaru don cin abinci, sai ku jira juna. 34Idan kuwa wani yana jin yunwa, ya ci a gida, kada ya zama taronku ya jawo maku hukunci. Batun sauran abubuwan da kuka rubuta kuwa, zan ba da umarni a kai sa'ad da na zo.

Did you know?
Covered heads and the Lord's Supper
- The chapter sets out an order of head: the head of every man is Christ, the head of the woman is man, and the head of Christ is God. It also says that in the Lord neither woman nor man is independent of the other, because woman came from man and man is born of woman, and everything comes from God. When they pray or prophesy, a man with his head covered dishonors his head, and a woman with her head uncovered dishonors her head, as if it were shaved; she ought to have a sign of authority on her head because of the angels, and the churches of God are said to have no other practice.Sources: the Bible text itself
- The writer offers no praise for their gatherings, which he says do more harm than good. He has heard that divisions appear when they come together as a church, and in part he believes it; each person goes ahead without sharing, so one remains hungry while another gets drunk, and therefore it is not the Lord's Supper they eat. He tells them to wait for one another and, if anyone is hungry, to eat at home, so that coming together will not result in judgment.Sources: the Bible text itself
- He says he received from the Lord what he also passed on: on the night he was betrayed, the Lord Jesus took bread, gave thanks, broke it, and said it was his body, for them; after supper he took the cup and called it the new covenant in his blood, to be done in remembrance of him. As often as they eat this bread and drink this cup, they proclaim the Lord's death until he comes. Whoever eats or drinks in an unworthy manner is guilty of sinning against the body and blood of the Lord, so each person must examine himself, because eating and drinking without recognizing the body brings judgment.Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org