1 Corinthians 10
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Ina son ku sani, 'yan'uwa, cewa ubaninmu duka suna karkashin gajimarai kuma sun bi ta cikin teku. 2Dukansu an yi masu baftisma cikin gajimarai da kuma teku, 3kuma dukansu sun ci abincin ruhaniya iri daya. 4Dukansu sun sha abin sha na ruhaniya iri daya. Gama sun sha daga wani dutsen ruhaniya da ya bisu, kuma wannan dutsen Almasihu ne. 5Amma Ubangiji bai ji dadin yawancinsu ba, saboda haka gawawakin su suka bazu a jeji. 6Wadan nan al'amura, an rubuta mana su domin muyi koyi da su, kada mu yi sha'awar miyagun ayyuka kamar yadda suka yi. 7Kada ku zama masu bautar gumaka kamar yadda wadansun su suka yi. Wannan kamar yadda aka rubuta ne, “Mutanen sukan zauna su ci su sha kuma su tashi suyi wasa.” 8Kada mu shiga zina da faskanci kamar yadda yawancin su suka yi, a rana guda mutane dubu ashirin da uku suka mutu. 9Kada mu gwada Almasihu kamar yadda yawancinsu suka yi, macizai suka yi ta kashe su. 10kada kuma ku zama masu gunaguni kamar yadda suka yi, suka yi ta mutuwa a hannun malaikan mutuwa. 11Wadannan abubuwa sun faru dasu ne a matsayin misalai a garemu. An rubuta su domin gargadinmu - mu wadanda karshen zamanai yazo kanmu. 12Saboda haka, bari duk wanda yake tunanin shi tsayyaye ne, to yayi hattara kada ya fadi. 13Babu gwajin da ya same ku wanda ba a saba da shi ba cikin dukan mutane. A maimako, Allah mai aminci ne. Da ba zaya bari ku jarabtu ba fiye da iyawarku. Tare da gwajin zai tanadar da hanyar fita, domin ku iya jurewa. 14Saboda haka ya kaunatattu na, ku guji bautar gumaka. 15Ina magana da ku kamar masu zurfin tunani, domin ku auna abin da ni ke fadi. 16Kokon albarka da muke sa wa albarka, ba tarayya bane cikin jinin Almasihu? Gurasa da muke karyawa ba tarayya bane cikin jikin Almasihu? 17Domin akwai gurasa guda, mu da muke dayawa jiki daya ne. Dukanmu munci daga gurasa daya ne. 18Dubi mutanen Isra'ila: ba wadanda ke cin hadayu ke da rabo a bagadi ba? 19Me nake cewa? gunki wani abu ne? Ko kuma abincin da aka mika wa gunki hadaya wani abu ne? 20Amma ina magana game da abubuwan da al'ummai suke hadaya, suna wa aljannu ne hadaya ba Allah ba. Ba na son kuyi tarayya da al'janu! 21Ba zaku sha daga kokon Ubangiji ku kuma sha na Al'janu ba, ba za kuyi zumunta a teburin Ubangiji ku yi a na Al'janu ba. 22Ko muna so mu sa Ubangiji kishi ne? Mun fi shi karfi ne? 23“Komai dai dai ne,” amma ba komai ke da amfani ba, “Komai dai dai ne,” amma ba komai ke gina mutane ba. 24Kada wani ya nemi abinda zaya amfane shi. A maimako, kowa ya nemi abinda zaya amfani makwabcinsa. 25Kana iya cin duk abin da ake sayarwa a kasuwa, ba tare da tamboyoyin lamiri ba. 26Gama “duniya da duk abin da ke cikin ta na Ubangiji ne.” 27Idan marar bangaskiya ya gayyace ka cin abinci, kana kuma da niyyar zuwa, ka je ka ci duk abinda aka kawo maka, ba tare da tamboyoyin lamiri ba. 28Amma idan wani ya ce maka, “Wannan abinci an yi wa gumaka hadaya da shi ne” To kada ka ci. Wannan za ka yi ne saboda wanda ya shaida maka, da kuma lamiri ( gama duniya da dukan abinda ke cikin ta na Ubangiji ne). 29Ba ina nufin lamirin ka ba, amma lamirin wanda ya fada maka. Don me za a hukunta 'yanci na domin lamirin wani? 30Idan na ci abincin tare da bada godiya, don mi za a zage ni don abin da na bada godiya a kansa? 31Saboda haka, ko kana ci ko kana shi, ka yi komai domin daukakar Allah. 32Kada ka zama sanadiyyar tuntube, ga Yahudawa, ko Helenawa, ko ikilisiyar Allah. 33Na yi kokari in farantawa dukan mutane rai cikin dukan abubuwa. Ba riba nake nema wa kaina ba, amma domin kowa. Na yi wannan ne domin su sami ceto.

Did you know?
Wilderness Warnings and the Lord's Table
- Paul says he does not want the Corinthians unaware that the forefathers were all under the cloud and all passed through the sea, and that they were baptized into Moses in the cloud and in the sea. They all ate the same spiritual food and drank the same spiritual drink from the spiritual rock that accompanied them, and he says that rock was Christ.Sources: the Bible text itself
- Paul says God was not pleased with most of them, for they were struck down in the wilderness. He lists idolatry, sexual immorality in which twenty-three thousand died in one day, testing Christ, which brought death by snakes, and complaining, punished by the destroying angel, and calls these events examples written down as warnings.Sources: the Bible text itself
- He calls the cup of blessing and the bread that is broken a participation in the blood and body of Christ, and says pagan sacrifices are offered to demons, not to God, so the two tables cannot be shared. Food sold in the meat market may be eaten without raising questions of conscience, for "The earth is the Lord's, and the fullness thereof," but if someone says it was offered to idols, it should be refused for that person's conscience.Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org