Nations Bible

Ezekiel 44

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.

Sarki, Lawiyawa, Firistoci

1Sai mutumin ya komo da ni zuwa ƙofar waje na wuri mai tsarki, wadda take fuskantar gabas, tana kuwa a rufe. 2Ubangiji ya ce mini, “Wannan ƙofar za tă kasance a rufe. Ba za a buɗe ta ba; ba wanda zai shiga ta wurinta. Za tă kasance a rufe domin Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya shiga ta wurinta. 3Sarki kansa ne kaɗai zai zauna a hanyar shiga don yă ci a gaban Ubangiji. Zai shiga ta hanyar shirayin hanyar shiga yă kuma fita a wannan hanya.”

4Sa’an nan mutumin ya kawo ni ta hanyar ƙofar arewa zuwa gaban haikali. Na duba na kuma ga ɗaukakar Ubangiji tana cika haikalin Ubangiji, sai na fāɗi rubda ciki.

5Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ka lura sosai, ka saurara sosai ka kuma mai da hankali ga kome da na faɗa maka game da dukan ƙa’idodi game da haikalin Ubangiji. Ka lura sosai da ƙofar shigar haikali da kuma dukan ƙofofin wuri mai tsarki. 6Faɗa wa ’yan tawayen gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ayyukan banƙyamarku sun isa haka, ya gidan Isra’ila! 7Ban da dukan sauran ayyukanku na banƙyama, kun kawo baƙi marasa kaciya a zuciya da jiki a wurina mai tsarki, kun kuma ƙazantar da haikalina yayinda kuke miƙa mini abinci, kitse da kuma jini, kun kuma karya alkawarina. 8A maimakon yin ayyukanku bisa ga abubuwana masu tsarki, kun sa waɗansu su lura da wurina mai tsarki. 9Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba baƙo marar kaciya a zuciya da jiki da zai shiga wurina mai tsarki, kai, har ma da baƙin da suke zama a cikin Isra’ila.

10“ ‘Lawiyawan da suka yi nesa da ni sa’ad da Isra’ila suka kauce da kuma waɗanda suka karkata daga gare ni suka bi gumakansu, dole su ɗauki alhakin zunubinsu. 11Za su iya yin hidima a wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin haikali suna kuma hidima a cikinsu; za su iya yankan hadayun ƙonawa da sadaka don mutane su kuma tsaya a gaban mutane su yi musu hidima. 12Amma domin sun yi musu hidima a gaban gumakansu suka sa gidan Isra’ila ya yi zunubi, saboda haka na ɗaga hannu na rantse cewa dole su ɗauki alhakin zunubinsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. 13Ba za su yi kusa don su yi hidima kamar firistoci ko su zo kusa da abubuwana masu tsarki ko hadayuna mafi tsarki ba; dole su sha kunya saboda ayyukansu na banƙyama. 14Duk da haka zan sa su su lura da ayyukan haikali da kuma dukan ayyukan da za a yi a cikinsa.

15“ ‘Amma firistoci, waɗanda suke Lawiyawa kuma zuriyar Zadok waɗanda suka yi aminci ta wurin yin ayyukansu a wurina mai tsarki sa’ad da Isra’ilawa suka kauce daga gare ni, su ne za su zo kusa don hidima a gabana; za su tsaya a gabana don miƙa hadayun kitse da jini, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. 16Su ne kaɗai za su shiga wurina mai tsarki; su ne kaɗai za su zo kusa da teburina don yin hidima a gabana su kuma yi hidimata.

17“ ‘Sa’ad da suka shiga ƙofofin fili na can ciki, dole su sa tufafin lilin; kada su sa wani rigar da aka yi da ulu yayinda suke hidima a ƙofofin fili na can ciki da cikin haikali. 18Za su naɗa rawunan lilin a kawunansu, su kuma sa wandunan lilin. Kada su sa wani abin da zai sa su yi zuffa. 19Sa’ad da suka fita daga haikali zuwa fili na waje inda mutane suke, sai su tuɓe rigunan da suka yi hidima da su su bar su a tsarkakan ɗakuna, su sa waɗansu riguna, don kada su tsarkake mutane ta wurin rigunansu.

20“ ‘Ba za su aske kawunansu ko su bar gashin kansu ya yi tsayi ba, amma sai su sausaye gashin kansu. 21Kada firist ya sha ruwan inabi sa’ad da zai shiga fili na can ciki. 22Kada su auri gwauruwa ko macen da aka sāke; za su auri budurwai ne kaɗai na Isra’ilawa ko gwaurayen firistoci. 23Za su koyar da mutanena bambanci tsakanin tsarki da rashin tsarki su kuma nuna musu yadda za su bambanta marar tsarki da mai tsarki.

24“ ‘A duk wani rashin jituwa, firistoci za su zama alƙalai su kuma yanke magana bisa ga farillaina. Za su kiyaye dokokina da ƙa’idodina a dukan ƙayyadaddun bukukkuwana, su kuma kiyaye Asabbataina da tsarki.

25“ ‘Firist ba zai ƙazantar da kansa ta wurin zuwa kusa da gawa ba; amma, in gawar mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ko ɗansa ko ’yarsa, ko ɗan’uwansa ko ’yar’uwarsa ce, to, ba zai ƙazantar da kansa ba. 26Bayan ya tsarkaka, dole yă jira har kwana bakwai. 27A ranar da ya shiga fili na can ciki na wuri mai tsarki don hidima a wuri mai tsarki, zai miƙa hadaya don zunubi saboda kansa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

28“ ‘Ni ne kaɗai zan zama abin gādon da firistoci za su kasance da shi. Kada ka ba su wani mallaka a Isra’ila; zan zama mallakarsu. 29Za su ci hadaya ta gari, hadaya don zunubi da hadaya don laifi; da kuma kowane keɓaɓɓen abu a Isra’ila da za a ba wa Ubangiji zai zama nasu. 30Mafi kyau na nunan farinku da kuma dukan kyautanku na musamman za su zama na firistoci. Za ku ba su rabo na fari na ɓarzajjen hatsinku saboda albarka ta kasance a gidanku. 31Firistoci ba za su ci mushen tsuntsu ko na dabba ba, ba kuwa za su ci waɗanda namun jeji suka kashe ba.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Sanctuary Ordinances and the Priesthood

  • The prophet distinguishes between the general Levites and the priests descended from Zadok. Because Zadok's line remained faithful when Israel strayed, they alone were granted the privilege of entering the inner sanctuary and ministering at the altar.Sources: Zadok · the Bible text itself
  • Priests entering the inner court were required to wear pure linen garments and turbans rather than wool to avoid perspiring. Before returning to the outer court among the people, they had to change into everyday clothing in the holy chambers so that their consecrated garments would not transmit holiness to the people.Sources: the Bible text itself
  • The outer east gate of the temple was permanently closed because the glory of the God of Israel had entered through it. Only the prince was permitted to sit within its portico to partake of communal meals before the Lord.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Most Holy Place · Today: on Mount Moriah · 31.778, 35.236 · verse 13
  • Holy Place · Today: on Mount Moriah · 31.778, 35.236 · verse 27

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.