Ezekiel 43
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.
Ɗaukaka ta komo haikali
1Sai mutumin ya kawo ni ƙofar da take fuskantar gabas, 2sai na ga ɗaukakar Allah na Isra’ila tana tahowa daga gabas. Muryarsa ta yi kamar rurin ruwaye masu gudu, ƙasa kuma ta haskaka da ɗaukakarsa. 3Wahayin da na gani ya yi kamar wahayin da na gani sa’ad da ya zo don yă hallaka birnin, kamar kuma wahayin da na gani kusa da Kogin Kebar, na kuwa fāɗi rubda ciki. 4Ɗaukakar Ubangiji ta shiga haikali ta ƙofar da take fuskantar gabas. 5Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kawo ni cikin fili na can ciki, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin.
6Yayinda mutumin yana tsaye kusa da ni, na ji wani yana magana da ni daga cikin haikalin. 7Ya ce, “Ɗan mutum, wannan shi ne kursiyina da wurin tafin ƙafafuna. A nan ne zan zauna a cikin Isra’ilawa har abada. Gidan Isra’ila ba zai ƙara ɓata sunana mai tsarki ba, ko su ko sarakunansu, ta wurin karuwanci da gumakan da ba su da rai, sarakunansu a masujadan kan tudu. 8Sa’ad da suka sa madogarar ƙofarsu kusa da madogarar ƙofata, da katanga kawai a tsakanina da su, sun ɓata sunana mai tsarki ta wurin ayyukansu masu banƙyama. Saboda haka na hallaka su cikin fushina. 9Yanzu bari su kawar da karuwancinsu da gumakansu waɗanda ba su da rai na sarakunansu daga gabana, zan kuwa zauna a cikinsu har abada.
10“Ɗan mutum, ka bayyana haikalin ga mutanen Isra’ila, don su ji kunya saboda zunubansu. Bari su yi la’akari da fasalin, 11kuma in suka ji kunyar abubuwan da suka aikata, sai ka sanar musu fasalin haikalin da shirye-shiryensa, ƙofofinsa na shiga da fita, dukan fasalinsa da dukan ƙa’idodinsa da dokokinsa. Ka rubuta waɗannan a gabansu saboda su yi aminci da fasalinsa su kuma kiyaye dukan ƙa’idodinsa.
12“Wannan ita ce dokar haikalin. Dukan filin da yake kewaye a kan dutsen, zai zama wuri mafi tsarki. Dokar haikalin ke nan.
Bagade
13“Waɗannan su ne aune-aunen bagade a tsawon kamu, wannan kamu shi ne kamun tafin hannu. Zurfin magudanar ruwansa kamu ɗaya ne fāɗinsa kuma kamu ɗaya, tare da da’ira kamun tafi ɗaya kewaye da gefensa. Wannan kuma shi ne tsayin bagaden. 14Daga lambatun da yake a ƙasa har zuwa ƙaramin mahaɗin da yake ƙasa wanda ya kewaye bagade, tsayinsa kamu biyu ne, fāɗinsa kuma kamu guda. Daga ƙaramin mahaɗi zuwa babban mahaɗin wanda ya kewaye bagade, zai zama kamu huɗu, fāɗinsa kuwa kamu ɗaya. 15Murhun bagaden kamu huɗu ne, akwai ƙahoni guda huɗu sun miƙe sama daga murhun. 16Murhun bagaden murabba’i ne, tsawonsa kamu goma sha biyu, fāɗinsa kuma kamu goma sha biyu. 17Gefen bisa ma murabba’i ne, tsawonsa kamu goma sha huɗu fāɗinsa kuma kamu goma huɗu, da da’ira da yake da fāɗin rabin kamu da magudanan ruwa kamu guda kewaye. Matakan bagaden suna fuskantar gabas.”
18Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa waɗannan su ne za su zama ƙa’idodi don yin hadaya ta ƙonawa da yayyafawar jini a kan bagaden sa’ad da aka gina shi. 19Za ka ba da ɗan bijimi a matsayin hadaya ta ƙonawa ga firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, na iyalin Zadok, waɗanda suke zuwa kusa don hidima a gabana, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. 20Za ka ɗibi jininsa ka zuba shi a ƙahoni huɗu na bagaden a gefen bisa da kuma kewaye da da’irar, ta haka za ka tsarkake bagaden ka kuma yi kafara dominsa. 21Za ka ɗauki bijimi na hadaya don zunubi ka ƙone shi a sashen da aka shirya na haikalin a wani wuri waje da wuri mai tsarki.
22“A rana ta biyu za ka miƙa bunsuru marar lahani domin hadaya don zunubi, za a kuma tsarkake bagaden yadda aka yi da bijimin. 23Sa’ad da ka gama tsarkake shi, sai ka miƙa ɗan bijimi da kuma rago daga cikin garke, dukansu marasa lahani. 24Za ka miƙa su a gaban Ubangiji, firistoci kuma za su barbaɗe gishiri a kansu su kuma miƙa su kamar hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.
25“Kwana bakwai za ka tanada bunsuru kullum domin hadaya don zunubi; za ka kuma tanada ɗan bijimi da rago daga garke, dukansu marasa lahani. 26Kwana bakwai za su yi kafara saboda bagaden su kuma tsarkake shi; ta haka za su keɓe shi. 27A ƙarshen waɗannan kwanaki, daga rana ta takwas zuwa gaba, firistoci za su miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama a kan bagade. Sa’an nan zan karɓe ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”

Did you know?
The Return of the Glory and the Altar
- Ezekiel witnesses the glory of God returning to the temple through the eastern gate, connecting this appearance directly to the visions he first experienced by the river Chebar in Babylon.Sources: the Bible text itself · Chebar
- The sanctuary duties and altar consecration are reserved exclusively for the Levitical priests from the family of Zadok, who served as high priest during the reigns of David and Solomon.Sources: the Bible text itself · Zadok
- The altar measurements are given in long cubits, which equal a standard cubit plus a handbreadth. A seven-day ritual of purification and atonement with blood and salt was required before regular offerings could be presented on the eighth day.Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 3
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org