Nations Bible

Ezekiel 21

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.

Babilon, takobin hukuncin Allah

1Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2“Ɗan mutum, ka kafa fuskarka gāba da Urushalima ka kuma yi wa’azi a kan wuri mai tsarki. Ka yi annabci gāba da ƙasar Isra’ila 3ka faɗa mata, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ina gāba da ke. Zan ja takobina daga kubensa in karkashe adalai da mugaye daga cikinki. 4Domin zan karkashe adalai da kuma mugaye, ba zan rufe takobina a kan kowa daga kudu zuwa arewa ba. 5Sa’an nan duka mutane za su san cewa Ni Ubangiji na ja takobina daga kubensa; ba zai sāke koma kuma ba.’

6“Saboda ka yi nishi, ɗan mutum! Yi nishi a gabansu da ajiyar zuciya da ɓacin rai. 7Kuma sa’ad da suka tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Domin labarun da suke fitowa. Kowace zuciya za tă narke kowane hannu kuma ya gurgunta; kowane ruhu zai sume kowane gwiwa kuma ta rasa ƙarfi kamar ruwa.’ Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”

8Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 9“Ɗan mutum, yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa,

“ ‘Takobi, takobi,

wasasshe da kuma gogagge,

10wasasshe don kisa,

gogagge har yana walwal kamar walƙiya!

“ ‘Kada ku yi farin ciki, hukunci yana zuwa, domin kowa ya ƙi jin abin da na yi gargaɗi a kai.

11“ ‘An ba da wannan takobi don a goge,

don a kama da hannu;

an washe shi aka kuma goge,

shiryayye don a yi kisa da shi.

12Ka yi kuka ka yi makoki, ɗan mutum,

gama yana gāba da dukan sarakunan Isra’ila.

An jefa su ga takobi

tare da jama’ata.

Saboda haka ku buga ƙirjinku.

13“ ‘Gwaji tabbatacce zai zo. Kuma a ce sandan Yahuda, wanda takobi ya ƙi, ya ci gaba? In ji Ubangiji Mai Iko Duka.’

14“Saboda haka fa, ɗan mutum ka yi annabci

ka kuma tafa hannuwanka.

Bari takobi ya yi sara sau biyu,

har sau uku ma.

Takobin kisa ne,

takobi ne don kisa mai girma,

zai kewaye su a kowane gefe.

15Domin zukata su narke

da yawa kuma su fāɗi,

na tsai da takobin kisa

a dukan ƙofofinsu.

Kash! A sa ya haska kamar walƙiya,

ana riƙe da shi don kisa.

16Ya takobi, yi sara zuwa dama

ka yi kuma zuwa hagu,

duk inda aka juya ka.

17Zan tafa hannuwana,

fushina kuwa zai sauka.

Ni Ubangiji na faɗa.”

18Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 19“Ɗan mutum, ka nuna hanyoyi biyu inda takobin sarkin Babilon zai bi, duka biyun su fara daga ƙasa guda. Ka kafa shaida inda hanyar za tă rabu zuwa cikin birni. 20Ka nuna hanya guda wadda takobi zai fāɗo wa Rabba ta Ammonawa ɗayan kuma da zai fāɗo a kan Yahuda da kuma Urushalima mai katanga. 21Gama sarkin Babilon zai tsaya a mararrabar hanya, a inda hanyar ta rabu biyu, don yă yi duba. Zai jefa ƙuri’a da kibiyoyinsa, zai nemi shawarar gumakansa, zai bincike hanta. 22A hannunsa na dama ƙuri’a don Urushalima za tă fito, inda zai kafa dundurusai, ya ba da umarni kisa, a yi kururuwar yaƙi, a kafa dundurusai a kan ƙofofi, a gina mahaurai a kuma yi ƙawanya. 23Zai zama kamar duban ƙarya ne ga waɗanda suka yi rantsuwar yin masa biyayya, amma zai tunashe su game da laifinsu ya kuma kama su.

24“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin ku mutanen nan kun tuna da laifinku ta wurin tawaye, kun kuma bayyana zunubanku cikin dukan abin da kuke yi, domin kun yi haka, za a kama ku.

25“ ‘Ya kai ƙazantaccen mugu, yerima Isra’ila, wanda kwanansa ta zo, wanda lokacin hukuncinsa ya cika fal, 26ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ka kunce rawanin, ka ɗauke rawanin nan. Ba zai zama kamar yadda yake ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da mai girma. 27Hallaka! Hallaka! Zan hallaka shi! Ba za a maido da shi ba sai ya ga ainihin mai shi; gare shi zan bayar da shi.’

28“Kai kuma, ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da Ammonawa da kuma zarginsu.

“ ‘Takobi, takobi,

an ja don kisa,

an goge don cinyewa

yana haske kamar walƙiya!

29Duk da wahayin ƙarya game da kai,

duban ƙarya game da kai,

za a sa shi a wuyan

mugaye waɗanda za a kashe,

waɗanda kwanansu ta zo,

waɗanda lokacin hukuncinsu ya cika fal.

30“ ‘Ka mai da takobi a kubensa.

A inda aka halicce ka,

a ƙasar kakanninka,

zan hukunta ka.

31Zan zub da hasalata a kanka

in hura maka wutar fushina;

Zan ba da kai a hannun mugayen mutanen

da suka gwanince a hallakarwa.

32Za ka zama itacen wuta,

za a zub da jininka a ƙasarka,

ba za a ƙara tuna da kai ba;

gama Ni Ubangiji na faɗa.’ ”

Did you know?

The Drawn Sword and Divination at the Crossroads

  • Ezekiel depicts the king of Babylon standing at a crossroads deciding whether to attack Rabbah, the chief city of the Ammonites east of the Jordan, or Jerusalem. To make his choice, the king uses three ancient divination practices: casting lots with shaken arrows, consulting idols, and inspecting an animal liver.Sources: the Bible text itself · Rabbah
  • The chapter employs vivid poetic imagery of a sharpened, polished sword flashing like lightning to depict incoming judgment. Ezekiel accompanies this message with dramatic physical actions, being commanded to groan bitterly, strike his thigh, and clap his hands together.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 2, 20, 21, 22, 23
  • Babylon · 32.543, 44.422 · verses 19, 21, 23
  • Ammon · 31.955, 35.934 · verses 20, 28
  • Rabbah · Today: Amman · 31.955, 35.934 · verses 20, 21

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.