Ezekiel 20
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.
Isra’ila ’yan tawaye
1A shekara ta bakwai, a wata na biyar a rana ta goma, waɗansu dattawan Isra’ila suka zo don su nemi nufin Ubangiji, suka kuwa zauna a ƙasa a gabana.
2Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 3“Ɗan mutum, ka yi magana da dattawan Isra’ila ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kun zo ne ku nemi shawarata? Muddin ina raye, ba zan bari ku nemi shawarata ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’
4“Za ka hukunta su? Za ka hukunta su, ɗan mutum? To, sai ka kalubalance su da ayyukan banƙyamar kakanninsu 5ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da na zaɓi Isra’ila, na ɗaga hannuna, na rantse wa zuriyar gidan Yaƙub na kuma bayyana kaina gare su a Masar da hannun da na ɗaga na ce musu, “Ni ne Ubangiji Allahnku.” 6A ranar na yi musu rantsuwa cewa zan fitar da su daga Masar zuwa ƙasar da na samo musu, ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasa mafi kyau cikin dukan ƙasashe. 7Na kuma ce musu, “Kowannenku ya zubar da mugayen siffofin da kuka kafa idanunku a kai, kuma kada ku ƙazantar da kanku da gumakan Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
8“ ‘Amma sai suka yi tawaye a kaina ba su kuwa saurare ni ba; ba su zubar da mugayen siffofin da suka kafa idanunsu a kai ba, balle su ƙi gumakan Masar. Saboda haka zan zubo hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a Masar. 9Amma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da suka zauna a ciki da kuma a idanun al’ummai da na bayyana kaina ga Isra’ilawa ta wurin fitar da su daga Masar. 10Saboda haka na fisshe su daga Masar na kawo su cikin hamada. 11Na ba su ƙa’idodina na kuma sanar musu da dokokina, gama mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu. 12Na kuma ba su Asabbataina kamar alama tsakaninmu, domin su san cewa Ni Ubangiji ne yake tsarkake su.
13“ ‘Duk da haka mutanen Isra’ila suka yi mini tawaye a cikin hamada. Ba su bi ƙa’idodina ba amma suka ki dokokina, ko da yake mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu, suka ɓata Asabbataina ƙwarai. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma hallaka su a hamada. 14Amma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da a idonsu na fisshe su. 15Na kuma ɗaga hannu na rantse musu a hamada cewa ba zan kawo su ƙasar da na ba su ba, ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasa mafi kyau cikin dukan ƙasashe, 16domin sun ƙi dokokina ba su kuwa bi ƙa’idodina ba suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Gama zukatansu sun fi so su bauta wa gumakansu. 17Duk da haka na dube su ta tausayi ba zan hallaka su ko in kawo ƙarshensu a hamada ba. 18Na faɗa wa ’ya’yansu a hamada, “Kada ku bi farillai kakanninku ko ku kiyaye dokokinsu ko ku ƙazantar da kanku da gumakansu. 19Ni ne Ubangiji Allahnku; ku bi ƙa’idodina ku kuma kula ku kiyaye dokokina. 20Ku kiyaye Asabbataina da tsarki, don su zama alama tsakaninmu. Ta haka za ku san cewa ni ne Ubangiji Allahnku.”
21“ ‘Amma ’ya’yan suka yi mini tawaye. Ba su bi ƙa’idodina ba, ba su kula su kiyaye dokokina ba, ko da yake mutumin da ya kiyaye su zai rayu ta wurinsu, suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a hamada. 22Amma na janye hannuna, kuma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da a idonsu na fisshe su. 23Na kuma ɗaga hannu na rantse musu cewa zan watsar da su cikin al’ummai in kuma warwatsa su cikin ƙasashe, 24domin ba su kiyaye dokokina ba amma suka ƙi ƙa’idodina suka kuma ƙazantar da Asabbataina, idanunsu suka yi sha’awar gumakan kakanninsu. 25Na kuma ba da su ga farillan da ba su da kyau da dokokin da ba za su rayu ta wurinsu ba; 26na bari suka ƙazantu ta wurin kyautai, hadayar kowane ɗan fari don in cika su da abin tsoro domin su san cewa ni ne Ubangiji.’
27“Saboda haka, ɗan mutum, ka yi magana da mutanen Isra’ila ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a wannan kuma kakanninku suka saɓe ni ta wurin yashe ni. 28Sa’ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su suka kuma ga tudu mai tsawo ko itace mai ganye, a can suka miƙa hadayunsu, suka yi sadakokin da suka tsokane ni na yi fushi, suka miƙa turaren ƙanshinsu suka kuma zuba sadakokinsu na sha. 29Sai na ce musu, Wane ɗakin tsafi kuke tafiya?’ ” (Ana ce da shi Bama har wa yau.)
Hukunci da Maidowa
30“Domin haka ka faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa za ku ƙazantar da kanku yadda kakanninku suka yi ne ku yi sha’awar mugayen siffofinsu? 31Sa’ad da kuka miƙa kyautai naku, hadayar ’ya’yanku maza a wuta, kuna cin gaba da ƙazantar da kanku da duka gumakanku har wa yau. Zan bari ku nemi shawarata, ya gidan Isra’ila? Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba zan bari ku nemi shawarata ba.
32“ ‘Kukan ce, “Kuna so ku zama kamar sauran al’ummai, kamar sauran mutanen duniya, waɗanda suke bauta wa itace da dutse.” Amma abin da kuke tunani ba zai taɓa faruwa ba. 33Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan yi mulki a kanku da hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi da kuma fushi. 34Zan fitar da ku daga al’ummai in tattara ku daga ƙasashe inda aka warwatsa ku, da hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi da kuma fushi. 35Zan kawo ku cikin hamadar al’ummai a can kuwa, fuska da fuska, zan hukunta ku. 36Yadda na hukunta kakanninku a hamadar ƙasar Masar, haka zan hukunta ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. 37Zan lura da ku yayinda kuke wucewa ƙarƙashin sanda, zan kuma kawo ku cikin daurin alkawari. 38Zan fitar da waɗanda suke mini tayarwa da kuma ’yan tawaye. Ko da yake zan fitar da su daga ƙasar da suke zama, duk da haka ba za su shiga ƙasar Isra’ila ba. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.
39“ ‘Game da ku, ya gidan Isra’ila, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ku tafi ku bauta wa gumakanku, kowannenku! Amma daga baya tabbatacce za ku saurare ni ba kuwa za ku ƙara ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku ba. 40Gama a kan dutsena mai tsarki, dutse mai tsayi na Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, a can a ƙasar gidan Isra’ila gaba ɗaya za su bauta mini, a can kuwa zan karɓe su. A can zan bukaci hadayunku da sadake sadakenku mafi kyau, tare da dukan tsarkakan hadayunku. 41Zan karɓe ku kamar turare mai ƙanshi sa’ad da na fitar da ku daga al’ummai na kuma tattara ku daga ƙasashe inda aka warwatsa ku, zan kuma nuna kaina mai tsarki a cikinku a idon al’ummai. 42Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji sa’ad da na kawo ku cikin ƙasar Isra’ila, ƙasar da na ɗaga hannu na rantse zan ba wa kakanninku. 43A can za ku tuna da halinku da kuma dukan ayyukanku waɗanda kuka ɓata kanku da su, za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda mugayen abubuwan da kuka aikata. 44Za ku san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na yi muku haka saboda sunana ba bisa ga mugayen hanyoyinku da ayyukanku marasa kyau ba, ya gidan Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Annabci a kan kudu
45Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 46“Ɗan mutum, ka kafa fuskarka wajen kudu; ka yi wa’azi a kan kudu ka kuma yi annabci a kan kurmin ƙasar kudu. 47Ka faɗa wa kurmin kudanci, ‘Ji maganar Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da sa maka wuta, za tă kuwa cinye dukan itatuwanki sarai, da ɗanye da busasshe. Ba za a kashe wutar da take ci ba, kuma kowace fuska a kudu zuwa arewa za tă ƙone. 48Kowa zai san cewa Ni Ubangiji ne ya ƙuna ta; ba za a kashe ta ba.’ ”
49Sai na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka! Suna zance a kaina cewa, ‘Ba misalai kawai yake yi ba?’ ”

Did you know?
Israel’s History of Rebellion and the Forest of the South
- When elders of Israel came to Ezekiel to inquire of God, the prophet was instructed not to answer them directly, but instead to recount generations of idolatry extending back to their ancestors' time in Egypt and throughout the wilderness.Sources: the Bible text itself · Egypt
- The chapter highlights Israel's persistent worship at unauthorized high places, referring to such elevated sites as Bamah, where sacrifices and incense were illicitly offered under leafy trees and on high hills.Sources: the Bible text itself · Bamah
- At the conclusion of the chapter, Ezekiel is commanded to prophesy against the south, specifically directing an oracle of unquenchable fire against the forest of the Negeb, an arid region extending south of Judah.Sources: the Bible text itself · Negeb
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org