Nations Bible

Romanos 6

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Me kuwa zamu ce yanzu? Sai mu ci gaba da yin zunubi domin Alheri ya yawaita? 2Ba zai taba faruwa ba. 'Yaya za'ace mu da muka mutu cikin zunubi mu ci gaba da rayuwa cikin sa? 3Ba ku san cewa duk wadanda aka yi masu baftisma cikin Almasihu Yesu an yi masu baftisma har ya zuwa mutuwarsa ne ba? 4An kuwa binne mu tare da shi, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa. Haka kuma ya kasance ne domin kamar yadda Almasihu ya tashi daga matattu cikin daukakar Uba. Sakamakon haka muma zamu yi tafiya cikin sabuwar rayuwa. 5Domin kuwa idan muna tare dashi cikin kamannin mutuwarsa zamu kuwa zauna tare dashi har ga kamannin tashinsa. 6Mun kuma san cewa, an giciye wannan tsohon mutunmin nan namu tare dashi, domin a hallaka jikin zunubi. wanna kuwa ya kasance ne domin kada mu ci gaba da bautar zunubi. 7Duk kuma wanda ya mutu an ambace shi a matayin adali akan zunubi. 8Amma idan muka mutu tare da Almasihu, mun bada gaskiya zamu yi rayuwa tare dashi. 9Muna da sanen cewa an tada Almasihu daga matattu, don haka kuwa ba matacce yake ba. Mutuwa kuma bata da iko a kansa. 10Game da mutuwar da yayi ga zunubi yayi sau daya kuma domin dukka. Rayuwar da yake yi kuma yana yi wa Allah ne. 11Don haka ku ma sai ku dauki kanku a matsayin matattu ga zunubi amma rayayyu ga Allah cikin Almasihu Yesu. 12Sabili da haka kada ku bar zunubi yayi mulki a cikin jikinku, har ku yi biyayya ga sha'awarsa. 13Kada ku mika gabobin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin rashin adalci. Amma ku mika kanku ga Allah rayayyu daga mutuwa. Ku kuma mika gabobin jikinku ga Allah a matsayin kayan aiki na adalci. 14kada ku ba zunubi dama yayi mulki a kanku, domin ba karkashin doka kuke ba, amma karkashin alheri kuke. 15To sai me? Sai mu yi zunubi wai don ba a karkashin doka muke ba amma alheri. ba zai taba faruwa ba. 16Ba ku san cewa duk ga wanda kuka mika kanku a matsayin bayi, a gareshi ku bayi ne ba? Wannan fa gaskiya ne, ko dai ku bayi ne ga zunubi wanda kaiwa ga mutuwa ko kuma bayi ga biyayya wanda ke kaiwa ga adalci. 17Amma godiya ta tabbata ga Allah! domin da ku bayin zunubi ne, amma kun yi biyayya daga zuciyarku irin salon koyarwar da aka baku. 18An 'yantar daku daga bautar zunubi, an kuma maishe ku bayin adalci. 19Ina magana da ku kamar mutum, domin kasawarku ta nama da jini. Kamar yadda kuka mika gabobin jikinku ga kazamta da miyagun ayyuka, haka ma yanzu ku mika gabobin jikinku a matsayin bayi na adalci. 20Domin a lokacin da kuke bayin zunubi, ku yantattu ne ga adalci. 21A wannan lokacin wanne amfani kuka samu na ayyukan da yanzu kuke jin kunyarsu? Domin kuwa sakamakon wadannan ayyuka shine mutuwa. 22Amma yanzu da da aka yantar daku daga zunubi aka mai da ku bayin Allah, amfaninsa ku kuwa shine tsarkakewarku. Sakamakon kuwa shine rai na har abada. 23Don kuwa sakamakon zunubi mutuwa ne. Amma kyautar Allah itace rai madauwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.

Você sabia?

Mortos para o pecado, vivos para Deus

  • Romanos 6 começa perguntando se as pessoas deveriam continuar no pecado para que a graça aumente, e responde: “De modo nenhum!” Quem morreu para o pecado, argumenta o capítulo, não pode continuar vivendo nele.Fontes: o próprio texto bíblico
  • O batismo é apresentado como batismo em Cristo Jesus e em sua morte, e como sepultamento com ele, para que, assim como Cristo foi ressuscitado dentre os mortos pela glória do Pai, os que estão unidos a ele andem em novidade de vida.Fontes: o próprio texto bíblico
  • Por causa da fraqueza da carne, o capítulo diz que fala em termos humanos e compara a vida à escravidão: a pessoa se torna escrava daquilo a que obedece, seja o pecado, que leva à morte, seja a obediência, que leva à justiça. O texto termina contrastando o salário do pecado, que é a morte, com o dom de Deus, que é a vida eterna em Cristo Jesus, nosso Senhor.Fontes: o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.