Apocalipse 9
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Sa'annan mala'ika na biyar ya busa kahonsa. Na ga tauraro daga sama da ya fado zuwa duniya. An ba tauraron nan mabudin hanyar rami marar iyaka. 2Ya bude hanyar rami marar iyaka, sai hayaki ya fito daga kofar kamar hayaki daga babban ramin wuta. Rana da iska suka juya duhu, sabili da hayakin da ke fitowa daga kofar ramin. 3Daga cikin hayakin kuwa sai ga fari sun fito zuwa duniya, aka ba su iko kamar na kunamai cikin duniya. 4Aka gaya masu kada su yi wa ciyayi da kowanne koren ganye ko itace illa, sai dai mutanen da basu da hatimin Allah a goshinsu. 5Ba a basu izini su kashe wadannan mutane ba, sai dai su azabtar da su na watani biyar. Zafinsu kuwa zai zama kamar na cizon kunama idan ta harbi mutum. 6A kwanakin nan mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su same ta ba. Za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za ta guje su. 7Farin kuwa suna kama da dawakai da aka shirya domin yaki. A bisa kansu akwai wani abu kamar rawanan zinariya, fuskokinsu kuma kamar na 'yan adam. 8Gashinsu kuma kamar na mata yake, hakoransu kamar hakoran zaki. 9Sulkunansu kuma kamar na karfe, karar fikafikansu kuma kamar karar kekunan dawakin yaki masu yawa da dawakai da aka shirya domin zuwa yaki. 10Suna da wutsiya da kari kamar kunamai; A wutsiyar su kuma suna da ikon da zai azabtar da mutane na tsawon wata biyar. 11Suna da wani kamar sarki a kansu, mala'ikan rami marar iyaka. Sunansa da Ibraniyanci Abadon, da Helenanci kuma Afoliyon. 12Bala'i na fari ya wuce. Duba! Bayan wannan akwai masifu guda biyu masu zuwa. 13Mala'ika na shida ya busa kahonsa, sai na ji murya daga kahonin bagadin zinariya da ke gaban Allah. 14Muryar ta ce wa mala'ika na shida da ke rike da kahon, “Kwance mala'ikun nan hudu da ke daure a babban kogin Yufiretis,'' 15Mala'iku hudun da aka shirya domin wannan sa'a, da wannan rana, da wannan wata, da kuma wannan shekara, aka sake su su kashe daya bisa uku na 'yan adam. 16Yawan sojoji da ke kan dawakai shine 200, 000, 000. Na ji adadin su. 17Haka na ga dawakan a cikin wahayina da mahayansu: Sulkunansu jawur kamar wuta, bakin shudi, da kuma ruwan doruwa. Kawunan dawakan suna kama da na zakuna, daga bakunansu kuma wuta, da hayaki da farar wuta suka fito. 18Aka kashe daya bisa uku na mutane ta annoban nan uku: wuta, hayaki da farar wuta da suka fito daka bakunansu. 19Domin iko na dawakan na bakunansu da wutsiyoyinsu - domin wutsiyoyinsu suna kama da macizai, kuma suna da kawuna wadanda dasu suke ji wa mutane rauni. 20Sauran 'yan adam, da ba a kashe su ta wannan annoba ba, basu tuba daga ayyukan da suka yi ba. Basu kuma daina bautar aljanu da gumakan zinariya, da azurfa, da tagulla, da dutse, da itace ba - abubuwan da ba su gani, ji, ko tafiya. 21Basu kuma tuba ba daga kisan kai, sihiri, fasikanci, ko kuma ayyukansu na sata ba.
Você sabia?
O abismo, o destruidor e o Eufrates
- Em Apocalipse 9, os gafanhotos são governados pelo anjo do Abismo, chamado Abadom em hebraico e Apoliom em grego. O Dicionário Bíblico de Easton (1897) explica o nome hebraico como destruição e o grego como destruidor, e sugere tomar a palavra como personificação da ideia de destruição ou como o Sheol, o reino dos mortos. Observa que o termo hebraico é traduzido como destruição em Jó e Provérbios, enquanto a Revised Version conserva Abaddon nas três últimas dessas passagens.Fontes: o próprio texto bíblico · Apollyon
- Em Apocalipse 9, a sexta trombeta solta quatro anjos presos junto ao grande rio Eufrates. O Dicionário Bíblico de Easton (1897) registra o nome hebraico Perath, o assírio Purat e a forma persa em cuneiforme Ufratush, da qual vem o grego Eufrates; diz que o nome grego significa água doce e o assírio, a corrente ou a grande corrente. Nas Escrituras, o rio é muitas vezes apenas o rio ou o grande rio, citado como um dos rios do Paraíso e como limite da terra prometida aos descendentes de Abraão.Fontes: o próprio texto bíblico · Euphrates
- Apocalipse 9 apresenta a quinta trombeta como o primeiro de três ais. Seus gafanhotos podem atormentar as pessoas por cinco meses com uma ferroada como a de um escorpião, mas não lhes é permitido matar. Passado esse ai, os cavalos vistos na sexta trombeta matam um terço da humanidade com o fogo, a fumaça e o enxofre que saem de suas bocas.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Euphrates · Hoje: Euphrates River · 31.004, 47.442 · versículo 14
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org