Apocalipse 6
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Na duba lokacin da Dan Ragon ya bude daya daga cikin hatiman bakwai, sai na ji daya daga cikin rayayyun halittattun hudu ya fada da murya kamar tsawa, ''Zo!” 2Sai Na duba sai ga wani farin doki, mahayinsa na rike da baka, kuma an bashi rawani. Ya fito a matsayin mai nasara domin ya yi nasara. 3Sa'anda Dan Ragon ya bude hatimi na biyu, sai na ji rayayyen halitta na biyu ya ce, ''Zo!'' 4Sai wani doki ya fito waje - jawur. Ga mahayin aka bashi dama ya dauke salama daga duniya, domin mutanen ta su karkashe juna. Wannan mahayin an bashi babbar takobi. 5Sa'anda Dan Ragon ya bude hatimi na uku, sai na ji rayayyen halita na uku ya ce, ''Zo!'' Na ga bakin doki, mai hawanta na rike da ma'auni a cikin hannunsa. 6Sai na ji kamar wata murya daga cikin rayayyun halittattun nan hudu ta ce, “Mudun alkama guda a kan albashin yini, kuma mudun sha'ir uku. Amma kar ka bata mai da kuma ruwan inabi.” 7Da Dan Ragon ya bude hatimi na hudu, na ji muryar rayayyen halitta na hudu ya ce, ''Zo!'' 8Sai na ga wani doki ruwan toka. Mai hawansa an bashi suna mutuwa, hades kuma tana biye da shi. An basu iko bisa kashi hudu na duniya su kashe da takobi, yunwa, cututtuka, da kuma namomin jeji na duniya. 9Da Dan Ragon ya bude hatimi na biyar, a karkashin bagadi sai na ga rayukan wadanda aka kashe saboda maganar Allah, da kuma shaidar da suka rike. 10Suka yi kuka da babban murya, ''Sai yaushe ya mai iko duka, Mai Tsarki da gaskiya, zaka shari'anta mazaunan duniya, ka kuma dauki fansar jininmu? 11Sai kowanne dayan su aka bashi farar tufa aka kuma fada masu su kara jira na lokaci kadan har sai adadin abokan bautar su da kuma 'yan'uwansu maza da mata wadanda aka kashe ya cika, kamar yadda aka kashe su. 12Da Dan Ragon ya bude hatimi na shidan, ina kallo sai ga babbar girgizar kasa. Rana ta zama baki kirin kamar bakar tufa, wata kuma ya zama kamar jini. 13Taurarin sama suka fado kasa, kamar yadda itacen baure ke karkade 'ya'yansa da basu nuna ba, yayin da babbar iska ta kada. 14Sama kuma ta bace kamar takardar da aka nannade. Kowanne dutse da tsibiri aka kau da shi daga wurinsa. 15Sai sarakan duniya da muhimman mutane da sarakunan yaki, attajirai, da masu iko, tare da kowanne mutum, bawa da 'yantacce suka boye cikin duwatsu da tsaunuka. 16Suka ce wa tsaunuka da duwatsu, “Ku fado bisan mu! Ku boye mu daga fuskar wanda yake zaune bisa kursiyin da kuma fushin Dan Ragon. 17Domin babban ranar fushin sa ta zo. Wa zai iya tsayawa?''

Você sabia?
A Abertura dos Seis Selos
- Os primeiros quatro selos revelam quatro cavaleiros em cavalos branco, vermelho brilhante, preto e amarelo, convocados um a um pelos quatro seres viventes. Cada cavaleiro traz uma aflição distinta sobre a terra, desde a conquista e a retirada da paz até a fome generalizada, a peste e a morte.Fontes: o próprio texto bíblico
- O terceiro cavaleiro segura uma balança, acompanhado por uma proclamação que fixa o preço de uma medida de trigo ou três de cevada em um denário, refletindo uma grave escassez e racionamento de alimentos enquanto o azeite e o vinho são poupados.Fontes: o próprio texto bíblico
- Com a abertura do quinto e do sexto selos, o foco se volta para as almas dos mártires debaixo do altar e, em seguida, para imensas convulsões cósmicas e terrestres que levam pessoas de todas as classes sociais a se esconderem em cavernas nas montanhas.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org