Nations Bible

Apocalipse 4

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Bayan wadannan abubuwa na duba, sai ga budaddiyar kofa a sama. Muryar fari da na ji kamar kakaki, na cewa hauro in nuna maka abubuwan da dole za su faru bayan wadannan al'amura.” 2Nan da nan ina cikin Ruhu, sai na ga wani kursiyin da aka ajiye shi a sama, da wani zaune bisansa. 3Shi da ke zaune a kan tana da kamanin yasfa da yakutu. Akwai Bakangizo kewaye da kursiyin kamanin bakangizon kuwa zumurudu. 4A kewaye da kursiyin kuwa akwai kursiyoyi ashirin da hudu, masu zama bisa kursiyoyin nan kuwa dattawa ne ashirin da hudu, sanye da fararen tufafi, da kambunan zinariya bisa kawunansu. 5Daga kursiyin walkiya na ta fitowa, cida, da karar aradu. Fitilu bakwai na ci a gaban kursiyin, fitilun sune ruhohin Allah guda bakwai. 6Gaban kursiyin akwai tekun gilashi, mai haske kamar karau. A tsakiyar kursiyin da kewayen kursiyin akwai rayayyun hallitu guda hudu cike da idanu gaba da baya. 7Rayayyen hallitta na farko na da kamanin zaki, rayayyen hallitta na biyun kamanin dan maraki ne, rayayyen hailitta na uku fuskar sa kamar dan adam, kuma rayayyen hallitta ta hudu na da kamanin gaggafa mai tashi. 8Dukan rayayyun hallittan nan hudu na da fukafukai shida shida, cike da idanu a bisa da karkashin fukafukan. Dare da rana ba sa daina cewa, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki ne Ubangiji Allah, mai iko duka, shine da shine yanzu shine mai zuwa.” 9A dukan lokacin da rayayyun hallittun nan suke ba da girma, daukaka, da godiya ga shi da ke zaune bisa kursiyin, wanda ke raye har abada abadin, 10sai dattawan nan ashirin da hudu suka fadi da fuskokinsu a kasa gaban shi da ke zaune bisa kursiyin. Suka yi sujada ga shi da ke rayuwa har abada abadin, suna jefar da kambinsu a gaban kursiyin, suna cewa, 11“Ka cancanta, ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka karbi yabo da daukaka da iko. Domin kai ka hallicci dukan komai, da kuma nufinka ne, suka kasance aka kuma hallicce su.

Você sabia?

O trono e a adoração

  • O capítulo começa quando o narrador olha e vê uma porta aberta no céu. A voz que ele já tinha ouvido, semelhante a uma trombeta, o chama para subir e ver o que deve acontecer depois; imediatamente ele está no Espírito e vê um trono, com alguém sentado que parece jaspe e cornalina, cercado por um arco-íris que brilha como esmeralda.Fontes: o próprio texto bíblico
  • O próprio texto explica uma das imagens: as sete tochas de fogo que ardem diante do trono são os sete Espíritos de Deus. Do trono saem relâmpagos, estrondos e trovões, e diante dele há algo como um mar de vidro, límpido como cristal.Fontes: o próprio texto bíblico
  • Quatro seres viventes rodeiam o trono, semelhantes a um leão, a um bezerro, a um rosto humano e a uma águia em voo. Cada um tem seis asas e está coberto de olhos, e de dia e de noite não param de proclamar santo o Senhor Deus Todo-Poderoso. Sempre que eles dão glória, vinte e quatro anciãos vestidos de branco, com coroas de ouro, prostram-se, lançam as coroas diante do trono e declaram digno aquele que está sentado, porque criou todas as coisas e pela sua vontade elas existem.Fontes: o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.