Nations Bible

Apocalipse 13

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Sai na ga wani dabba yana fitowa daga teku. Yana da kahonni goma da kawuna bakwai. A kan kahonninsa akwai kambi goma, a kan kowanne kansa akwai suna na sabo. 2Wannan dabban da na gani yana kama da damisa, kafafunsa kuma kamar na beyar, bakinsa kuma kamar na zaki. Wannan diragon ya ba shi karfinsa, da kursiyinsa da ikonsa mai girma na sarauta. 3Daya daga cikin kawunan dabban ya yi kamar an kashe shi, amma rauninsa mai tsanani ya warke. Sai dukan duniya ta yi mamaki a yayin da suke bin dabban. 4Su ma suka yi wa diragon sujada, domin ya ba dabban ikonsa. Suka yi wa dabban sujada suna ta cewa, “Wanene kamar dabban? Wa kuma zai iya yin fada da shi?” 5Aka ba dabban baki da zai iya fadin kalmomin fahariya da sabo. Ya sami izini na zartar da iko har wata arba'in da biyu. 6Sai dabban ya bude bakinsa yana maganganun sabo ga Allah: yana sabon sunansa, da mazauninsa, da kuma wadanda ke zaune a sama. 7Aka yarje wa dabbar ya yi yaki da masu bi ya kuma yi nasara da su. An kuma ba shi iko bisa kowacce kabila, da jama'a, da harshe, da al'umma. 8Dukan wadanda ke zaune a duniya za su yi masa sujada, dukan wadanda tun hallitar duniya ba a rubuta sunayensu a littafin rai na Dan Rago ba, wanda aka yanka. 9Idan wani yana da kunne, bari ya ji. Duk wanda za a dauke shi zuwa bauta, ga bauta zai tafi. 10Duk wanda za a kashe da takobi, da takobi za a kashe shi. Wannan kira ne na dauriya, hakuri da bangaskiya ga wadanda suke da tsarki. 11Sai na ga wani dabban na fitowa daga cikin kasa. Yana da kahonni biyu kamar na dan rago, ya kuma yi magana kamar maciji. 12Ya zartar da dukan ikon dabban na farko a gabansa, ya kuma sa duniya da duk mazaunanta su yi wa dabban nan na farko sujada, wanda aka warkar masa da rauni mai kamar na ajali. 13Ya yi manyan al'ajibai. Har ya sa wuta ta sauko kasa daga sama a gaban mutane. 14Ta wurin alamu da aka yarje masa ya yi, ya yaudari mazaunan duniya. Ya ce masu su yi wata siffa don girmama dabban da yake da raunin takobi, amma duk da haka ya rayu. 15Aka yarje masa ya ba da numfashi ga siffar dabban domin siffar ta yi magana, ta kuma sa a kashe duk wadanda suka ki yin sujada ga dabban. 16Ya kuma tilasta kowa, kanana da manya, mawadata da matalauta, masu yanci da bayi, su karbi alama a hannun dama ko kuma a goshi. 17Ba shi yiwuwa wani ya saya ko ya sayar sai dai yana da alamar dabban, wato lambar nan da ke wakiltar sunansa. 18Wannan na bukatar hikima. Idan wani yana da hikima, sai ya kididdige lambar dabban nan. Gama lambar ta mutum ce. Lambarta itace 666.

Você sabia?

Duas bestas, adoração e o número 666

  • A primeira besta sobe do mar com sete cabeças e dez chifres, com dez coroas reais nos chifres e nomes blasfemos nas cabeças. Ela é como um leopardo, com pés de urso e boca de leão, e o dragão lhe dá o seu poder, o seu trono e grande autoridade.Fontes: o próprio texto bíblico
  • Uma das cabeças parece mortalmente ferida, mas a ferida mortal é curada, e o mundo inteiro se maravilha e segue a besta. As pessoas adoram o dragão que deu autoridade à besta, e adoram a besta; a ela é permitido falar blasfêmias arrogantes e agir por quarenta e dois meses, guerrear contra os santos e vencê-los, e ter autoridade sobre toda tribo, povo, língua e nação.Fontes: o próprio texto bíblico
  • Uma segunda besta sobe da terra com dois chifres como os de um cordeiro, mas fala como um dragão e exerce toda a autoridade da primeira besta. Por meio de grandes sinais, até fogo descendo do céu, ela engana os habitantes da terra para que façam uma imagem da besta que foi ferida pela espada e ainda assim viveu, e exige que todas as pessoas, pequenas e grandes, ricas e pobres, livres e escravos, recebam uma marca na mão direita ou na testa, de modo que ninguém possa comprar ou vender sem ela. O capítulo pede sabedoria para calcular o número da besta, o número de um homem: 666.Fontes: o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.