Nations Bible

Marcos 8

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1A kwanakin nan, akwai wani gagaruman taron mutane, kuma basu da abincin ci. Yesu ya kirawo almajiransa yace masu, 2“Ina tausayin taron mutanen nan domin kwana uku kenan suna nan tare da ni babu abinci. 3Idan na salame su su koma gidajensu ba tare da sun ci abinci ba, za su galabaita a hanya domin gidajensu na da nisa.” 4Almajiransa suka amsa masa cewa, “A ina za mu iya samu gurasa a wannan jeji da zai ishi wadannan mutane haka?” 5Ya tambaye su, “gurasa nawa kuke da su?” Sai suka ce, “Bakwai.” 6Ya umarci mutanen da su zauna. Ya dauki gurasar bakwai, bayan da ya yi godiya, ya kakarya gurasar, sa'annan ya umarci almajiransa da su raba wa mutanen. Su kuwa suka raba masu. 7Suna kuma da kananan kifaye kadan. Bayan da ya yi godiya akan su, ya umurci almajiran su rabawa mutanen. 8Sun ci sun koshi. Suka tattara ragowar, har sun cika kwanduna bakwai. 9Akwai maza kimanin dubu hudu a wurin. Yesu ya sallame su. 10Nan take, ya shiga jirgin ruwa da almajiransa zuwa shiyyar Dalmanuta. 11Sai Farisawa suka zo suka fara gardama da shi. Suna nema ya nuna masu alama daga sama, domin su gwada shi. 12Ya ja numfashi a ruhunsa yana cewa, “Don me wannan tsarar tana neman alama. Hakika ina gaya maku, babu wata alama da za a ba wannan tsarar.” 13Sai ya bar su ya sake shiga jirgin zuwa hayin tafkin. 14A lokacin nan, almajiransa sun manta su dauki gurasa. Domin gurasa daya ce tak a garesu cikin jirgin ruwan. 15Ya gargade su, “ku yi hattara da yisti na Farisawa da Yisti na Hirudus.” 16Almajiran suka fara tattaunawa a tsakaninsu, “Saboda ba mu da gurasa ne.” 17Yesu yana sane da wannan, sa'annan ya ce masu, “Don me kuke tattaunawa akan rashin gurasa? Har yanzu baku gane ba? Har yanzu ba ku da sane? Ko zuciyar ku ta duhunta ne?” 18Kuna da idanu, ba ku gani? Kuna da kunnuwa, ba ku ji? Ba ku tuna ba? 19Da na kakkarya gurasar a cikin mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka samu ragowa? Suka ce masa, “Goma sha biyu.” 20Kuma da na kakarya gurasa bakwai a cikin mutane dubu hudu, kwanduna nawa kuka dauka cike da ragowar? Suka ce masa, “bakwai.” 21Ya ce masu, “har yanzu baku gane ba?” 22Sun zo Baitsaida. Mutanen wurin suka kawo masa wani makaho, sai suka roke shi ya taba shi. 23Yesu ya rike hanun makahon, ya jagorance shi zuwa bayan kauyen. Da ya tofa yawunsa a idon mutumin, kuma ya dora hanunsa akan mutumin, sai ya tambaye shi “kana ganin wani abu kuwa?” 24Ya daga ido sai ya ce, “ina ganin mutane na tafiya kamar itatuwa.” 25Ya sake dora masa hannu a idanuwansa, mutumin ya bude idanuwansa, sai ya fara ganin gari da kyau. 26Yesu ya sallame shi zuwa gidansa nan take, ya ce masa, “kada ka shiga cikin garin” 27Yesu da almajiransa sun shiga kauyukan kaisariya ta Filibi. Da suke kan hanya, sai ya tambaye su, “Shin wanene mutane ke ce da ni?” 28Suka amsa masa suka ce, Yahaya mai Baftisma. Wasu suka ce, “Iliya”. wadansu kuma, 'Daya daga cikin anabawa”. 29Ya tambaye su, “Amma me ku ke ce da ni?” Bitrus ya ce, “Kai ne Almasihu.” 30Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa game da shi. 31Sai ya fara koya masu cewa, dole ne Dan Mutum ya sha wahala, dattawa da marubuta da manyan Firistoci zasu ki shi, a kuma kashe shi. Bayan kwana uku, zai tashi daga matattu. 32Ya fadi wannan afili. Sai Birus ya ja shi gefe ya fara tsauta masa. 33Amma Yesu ya juya ya dubi almajiransa sa'annan ya tsautawa Bitrus yana cewa, “Ka koma bayana Shaidan, domin kana kula da abubuwan mutane ne kawai, ba na Allah ba.” 34Sai ya kira taron jama'ar da almajiransa a wuri daya, ya ce masu, “Duk wanda yake so ya bini, dole ne ya musunci kansa, ya dauki giciyensa ya biyo ni. 35Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi, amma duk wadda ya rasa ransa domina da kuma bishara zai cece shi. 36Me zai amfani mutum idan ya sami dukan duniya sannan ya rasa ransa. 37Me mutum zai bayar amaimakon ransa? 38Duk wanda ke jin kunyata ko maganata a wannan mazinaciyar tsara mai zunubi, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa a lokacin da ya dawo cikin daukakar Ubansa da Malaiku masu tsarki.”

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Ver quem é Jesus

  • Depois que cerca de quatro mil homens comeram e foram recolhidos sete cestos de pedaços, Jesus entrou no barco com os discípulos e foi para a região de Dalmanuta, nome que aparece só neste capítulo. Era um lugar no lado oeste do mar da Galileia, perto de Magdala. No relato paralelo em Mateus, ele chega aos limites de Magdala, que provavelmente era o nome grego de uma das torres de vigia da margem ocidental do lago.Fontes: o próprio texto bíblico · Dalmanutha
  • Em Betsaida, algumas pessoas trouxeram um cego, e Jesus o levou pela mão para fora do povoado, cuspiu-lhe nos olhos e pôs as mãos sobre ele. No início, o homem via as pessoas como árvores que andavam; só quando Jesus tornou a pôr as mãos sobre os olhos dele a visão foi plenamente restaurada. A cidade é descrita no lado leste do lago, a cerca de duas milhas subindo o Jordão, na Gaulanítide; Filipe, o tetrarca, a ampliou e a chamou de Julias, por causa da filha do imperador, embora alguns tenham suposto que havia uma só Betsaida, construída dos dois lados do lago, perto de onde o Jordão nele entra.Fontes: o próprio texto bíblico · Bethsaida
  • Jesus e os discípulos seguiram para os povoados ao redor de Cesareia de Filipe, cidade situada cerca de vinte milhas ao norte do mar da Galileia, junto à base do monte Hermom, na nascente superior do Jordão, e descrita como o limite norte do seu ministério público. Segundo alguns, ela antes fora Baal-Gade ou Baal-Hermom, um santuário cananeu de Baal, e depois foi chamada Pânio ou Paneias, por causa de uma caverna profunda e cheia de água perto da cidade. Ali Pedro disse: "Tu és o Cristo"; e, quando repreendeu Jesus por ensinar que o Filho do Homem tinha de sofrer muitas coisas, ser morto e ressuscitar depois de três dias, Jesus respondeu: "Para trás de mim, Satanás", nome que significa adversário ou acusador.Fontes: o próprio texto bíblico · Caesarea Philippi · Satan

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Caesarea Philippi · Hoje: Banias · 33.246, 35.693 · versículo 27
  • Galilee · 32.760, 35.527 · versículo 27

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.