Nations Bible

Marcos 6

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Ya bar su ya zo garinsu, almajiransa su ka biyo shi. 2Sa'adda ranar Asabar tazo ya shiga cikin masujada ya yi koyarwa. Mutane da yawa da su ka ji koyarwarsa su ka yi mamaki, suka ce daga ina ya sami irin wannan koyarwar? Wacce irin hikima ce Allah ya ba shi haka? Wadanne irin ayyukan al'ajibi ya ke yi da hannuwansa? 3Wannan ba kafintan nan ba ne dan Maryamu, dan'uwan Yakubu da Yosi da Yahuza da Saminu? Ba ga 'yan'uwan sa 'yan mata mu na tare da su ba? Ba su ji dadi ba a ransu saboda Yesu. 4Yesu ya ce, “Annabi ba ya rasa daraja sai a gidansa da garinsa da cikin danginsa.” 5Bai iya yin wani aikin al'ajibi a wurin ba sai dai mutane kadan marasa lafiya ya dorawa hannu ya warkar da su. 6Rashin bangaskiyarsu ya ba shi mamaki. Sai ya tafi cikin kauyuka na kewaye da su ya yi ta koyarwa. 7Ya kira almajiransa su goma sha biyu, ya aike su biyu-biyu, ya ba su iko a kan aljanu, 8ya dokace su kada su dauki komai tare da su domin wannan tafiya, sai dai sanda kadai. Kada su dauki abinci ko jaka ko kudi a cikin aljihunsu, 9sai dai su sa takalmi kadai, kada su sa taguwa biyu a jikinsu. 10Ya ce da su, idan ku ka shiga wani gida sai ku zauna a gidan har lokacin da za ku tashi. 11Idan ku ka je wani gari aka ki karbar ku, ku karkabe kurar da ke kafufunku ta zama shaida kan mutanen garin. 12Sai suka tafi suka yi ta shela ga mutane cewa su tuba daga zunubansu. 13Sun fitar da aljanu da yawa, suka shafawa mutane da yawa mai suka warkar da su. 14Sarki Hirudus ya ji wannan, gama sunan Yesu ya zama sananne a wurin kowa da kowa. Wadansu suna cewa Yahaya mai yin baftisma ne ya tashi daga matattu shi ya sa ake yin wadannan ayyukan al'ajibi ta wurinsa. 15Wadansu kuma suna cewa, “Iliya,” Har yanzu wadansu suna cewa daya “daga cikin annabawa ne na da can.” 16Sa'adda Hirudus ya ji wannan sai ya ce, “Yahaya wanda na fillewa kai shine ya tashi.” 17Saboda Hirudus ne ya sa aka kama Yahaya aka kulle shi a kurkuku saboda Hirodiya( matar Filibus dan'uwansa), domin ya aure ta. 18Saboda Yahaya ya gaya wa Hirudus cewa bai halarta ya auri matar dan'uwansa ba. 19Sai ita Hirodiya ta yi kudurin ta kashe Yahaya amma bai yiwu ba. 20Domin Hirudus yana jin tsoron Yahaya, domin ya sani shi mai adalci ce, mai tsarki kuma. Domin haka Hirudus bai so wani abu ya faru da Yahaya ba, amma ya kan fusata idan ya ji wa'azin yahaya. Duk da haka da fari ciki yakan saurare shi. 21Amma sai dama ta samu inda Hirodiya za ta iya yin abin da ta ke so ta yi. A lokacin kewayowar ranar haihuwar sa, sai Hirudus ya shirya liyafa domin manyan da ke aiki tare da shi a cikin gwamnatin sa, da shugabannin da ke cikin Galili. 22Diyar Hirodiya ta zo ta yi masu rawa, rawarta kuwa tagamshi Hirudus da bakinsa. Sarki ya ce da yarinyar, “ki tambayi duk abin da ki ke so ni kuwa zan ba ki shi”. 23Ya rantse mata da cewa”Ko menene ki ka ce ki na so, ko da rabin mulkina ne” 24Sai ta fita ta je ta tambayi mamarta, “ me zan ce ya bani?” Sai ta ce kan Yahaya Mai Yin Baftisma. 25Sai ta dawo da sauri cikin dakin taro wurin sarki ta ce da shi, “Ina so ka ba ni kan Yahaya Mai Yin Baftisma a cikin tire.” 26Sarki ya damu kwarai, amma saboda ya yi alkawari ga kuma ofisoshinsa, ba dama ya ce a'a. 27Sai sarki ya aiki wani soja ya ba shi ummurni ya je ya kawo kan Yahaya. Sojan ya je ya fillo kan sa daga cikin kurkuku. 28Ya kawo kan a cikin tire ya ba yarinyar, yarinyar kuma ta kai wa mamarta. 29Da almajiran su ka ji labari, suka zo suka dauki gawarsa suka rufe a cikin kabari. 30Almajiran suka zo wurin Yesu, suka fada masa dukkan abin da suka yi da abin da suka koyar. 31Sai ya ce da su “ku je cikin kebabben wuri domin ku huta kadan,” domin mutane suna ta kaiwa da komowa, ba su sami damar hutawa ba balle su ci abinci 32Sai suka tafi kebabben wuri a cikin jirgin ruwa su kadai. 33Amma mutane da yawa sun gansu suna tafiya sun kuma gane su, sai suka fito daga cikin dukan garuruwa da gudu har su ka kai wurin kafin su zo. 34Sa'adda suka zo bakin gaba Yesu ya ga taron mutane da yawa sai ya ji tausayinsu domin sun yi kamar tumakin da ba da mai kiwo. Sai ya cigaba da koya masu abubuwa da yawa. 35Sa'adda yamma ta yi, almajiran sa suka zo suka ce da shi, “wurinnan kebabben wuri ne kuma ga lokaci ya tafi. 36Ka sallami mutanen nan domin su shiga cikin garuruwa da kauyuka da ke kusa domin su sayi abin da zasu ci. 37Amma sai ya ba su amsa ya ce,”Ku ku basu abinci su ci mana”. Sai suka ce da shi, “ma iya zuwa mu sawo gurasa ta sule dari biyu mu basu su ci?” 38Sai ya ce dasu, “Dunkulen gurasa guda nawa kuke dasu? Kuje ku gani.” Dasuka gano sai suka ce da shi, dunkule biyar ne da kifi guda biyu.” 39Sai ya ba da umarni mutanen su dukka su zauna a kan danyar ciyawa. 40Suka zauna kungiya kungiya wadansu su dari wadansu hamsin. 41Sai ya dauki dunkulen gurasa guda biyar da kifi guda biyu, ya ta da kansa sama, yasa albarka, ya kakkarya dunkulen gurasan, ya ba almajiran domin su rabawa taron jama'a duka. 42Dukansu suka ci suka koshi. 43Suka tattara gutsattsarin gurasar suka cika kwanduna guda goma sha biyu da gutsattsarin da kuma gutsattsarin kifin. 44Mutanen da suka ci gurasar sun kai mutum dubu biyar. 45Nan da nan ya ce almajiran sa su hau jirgin ruwa su yi gaba kafin ya zo, su je Baitsaida. Shi kuma ya tsaya domin ya sallami taron mutanen. 46Bayan da suka tafi shi kuma ya hau kan dutse domin ya yi addu'a. 47Har yamma ta yi jirgin ruwan ya na tsakiyar rafi shi kuma yana kan tudu shi kadai. 48Ya gansu suna wahala gama iska ta hana su tafiya. Wajan karfe hudu na asuba sai ya tawo wurin su yana tafiya a kan ruwa, yana so ya wuce gaban su. 49Sa'adda suka gan shi ya na tafiya a kan ruwa suka yi tsammani fatalwa ce, suka yi ihu, 50gama su duka sun gan shi, tsoro ya kama su. Sai nan da nan ya yi magana dasu ya ce, “Ku karfafa ni ne! kada ku ji tsoro!'' 51Ya shiga cikin jirgin ruwan tare dasu, sai iska ta dena bugawa. Sai suka yi mamaki kwarai. 52Gama basu gane batun dunkulen ba. Maimakon haka, sai zukatansu suka taurare. 53Sa'adda suka haye su zo kasar Janisarita suka sa wa jirgin sarka. 54Su na fitowa daga cikin jirgin kenan, mutane suka gane cewa Yesu ne. 55Mutane suka ruga cikin yankin su, suka kawo marasa lafiya a bisa shinfidun su zuwa wurinsa, dukan inda suka ji yana zuwa. 56Ko ina ya shiga birni da kauye, ko a cikin kasar sukan kawo marasa lafiya a kasuwanni suna rokonsa su taba ko da habar rigarsa, dukan wadanda suka taba kuwa suka warke.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Ministério, Oposição e Milagres

  • Quando Jesus ensinou na sinagoga de sua cidade natal, os moradores locais se escandalizaram com ele, identificando-o por sua profissão de carpinteiro e citando sua mãe Maria e seus irmãos Tiago, José, Judas e Simão.Fontes: o próprio texto bíblico · Mary (Mother of Jesus) · James (Brother of Jesus) · Simon
  • João Batista foi preso e executado por Herodes Antipas após declarar que o casamento de Herodes com Herodias, a antiga esposa de seu irmão Filipe, não era lícito.Fontes: o próprio texto bíblico · Herod Antipas · Herodias · Philip
  • Ao enviar os Doze discípulos de dois em dois pela Galileia, Jesus os instruiu a levar apenas um bordão e sandálias, dependendo inteiramente da hospitalidade dos lares que os recebessem.Fontes: o próprio texto bíblico · Galilee

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Nazareth · 32.702, 35.298 · versículo 1
  • Galilee · 32.760, 35.527 · versículo 21
  • Gennesaret · Hoje: El Ghuweir · 32.861, 35.507 · versículo 53

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.