Nations Bible

Mateus 8

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Da Yesu ya sauko daga dutsen, sai taro masu yawa suka bi shi. 2Sai wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ubangiji, in dai ka yarda, za ka iya tsarkake ni.” 3Yesu ya mika hannunsa ya taba shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan da nan aka tsarkake shi daga kuturtarsa. 4Yesu ya ce masa, 'Ka tabbata, ba ka gaya wa kowa komai ba. Sai dai ka je ka nuna kan ka ga firist, ka kuma bayar da baiko da Musa ya umarta domin shaida garesu? 5Da Yesu ya shiga kafarnahum, sai wani hafsa ya zo gunsa ya roke shi, 6Ya ce, Ubangiji, bawana na kwance shanyayye a gida, yana shan azaba kwarai.” 7Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.” 8Sai hafsan, ya ce, “Ubangiji, ban isa har ka zo gida na ba, amma sai ka yi magana kawai, bawana kuwa zai warke. 9Domin ni ma ina karkashin ikon wani ne, ina kuma da sojoji a karkashina, sai in ce wa wannan, 'je ka,' sai ya je, wani kuma in ce masa, 'zo,' sai ya zo, in ce wa bawa na, 'yi abu kaza,' sai ya yi,” 10Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya maku, ko a cikin isra'ila ban taba samun bangaskiya mai karfi irin wannan ba. 11Na gaya maku, da yawa za su zo daga gabas da yamma, su zauna cin abinci tare da Ibrahim da Ishaku, da Yakubu a cikin mulkin sama. 12Amma 'ya'yan mulkin kuwa sai a jefa su cikin matsanancin duhu. Can za su yi kuka da cizon hakora.” 13Yesu ya ce wa hafsan, “Je ka! Bari ya zamar maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi,” A daidai wannan sa'a bawansa ya warke. 14Da Yesu ya shiga gidan Btrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance da zazzabi. 15Yesu ya taba hannunta, zazzabin ya sake ta, ta kuma tashi ta fara yi masa hidima. 16Da maraice ya yi, sai mutanen suka kakkawo wa Yesu masu aljanu da yawa. Da magana kawai ya fitar da aljanun, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. 17Ta haka kuwa maganar annabi Ishaya ta samu cika cewa, “Shi da kansa ya debe rashin lafiyar mu, ya dauke cututtukan mu.” 18Sa'adda Yesu ya ga taro masu yawa kewaye da shi, sai ya ba da umarni su tafi su koma wancan hayi na tekun Galili. 19Sai wani marubuci ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.” 20Yesu ya ce masa, “Yanyawa suna da ramukansu, tsuntsayen sama kuma da shekunan su, amma Dan mutum ba shi da wurin da zai kwanta.” 21Wani cikin almajiran ya ce masa, “Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne mahaifina.” 22Amma Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne matattunsu.” 23Da Yesu ya shiga jirgi, almajiransa suka bi shi. 24Sai ga wata babbar iska ta taso a tekun, har rakuman ruwa suka fara shan kan jirgin. Amma Yesu yana barci. 25Sai almajiran sa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!” 26Yesu ya ce masu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu karancin bangaskiya?” Sa'annan ya tashi, ya tsauta wa iskar da tekun. Sai wurin gaba daya ya yi tsit. 27Mutanen suka yi al'ajibi, suka ce, “Wanne irin mutum ne wannan, wanda har iska da teku ma suke masa biyayya?”. 28Da Yesu ya zo daga wancan hayin a kasar Garasinawa, mutane biyu masu al'janu suka fito suka same shi. Suna fitowa daga makabarta kuma suna da fada sosai, har ma ba mai iya bin ta wannan hanya. 29Sai suka kwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai dan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?” 30To akwai wani garken aladu masu yawa na kiwo, babu nisa da su. 31Sai al'janun suka roki Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.” 32“Yesu ya ce masu, “To, ku je.” Sai aljanun suka fita, suka shiga cikin aladun. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka fada cikin tekun, suka hallaka a ruwa. 33Mutanen masu kiwon aladun suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin komai da komai, musamman abin da ya faru da masu al'janun. 34Sai duk jama'ar gari suka fito su sami Yesu. Da suka gan shi, suka roke shi ya bar kasarsu.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Curas, fé e o mar

  • Cafarnaum, cidade em que Jesus entra neste capítulo, era uma cidade da Galileia que não aparece no Antigo Testamento. O Easton's Bible Dictionary (1897) diz que ela se tornou a “sua própria cidade” depois que ele deixou Nazaré, e inclui o pedido do centurião e a cura na casa de Pedro entre os acontecimentos ali situados.Fontes: Capernaum · o próprio texto bíblico
  • Jesus diz que muitos virão do oriente e do ocidente para participar do banquete com Abraão, Isaque e Jacó no reino dos céus. O Easton's Bible Dictionary (1897) apresenta Abraão como filho de Terá e herdeiro das promessas, Isaque como o único filho de Abraão com Sara, e Jacó — também chamado Israel — como o filho gêmeo mais novo de Isaque e Rebeca.Fontes: o próprio texto bíblico · Abraham · Isaac · Jacob (Israel)
  • Mateus apresenta as curas daquela noite como cumprimento do que foi dito por meio do profeta Isaías: “Ele tomou as nossas enfermidades e carregou as nossas doenças.” O Easton's Bible Dictionary (1897) identifica Isaías como filho de Amoz, que profetizou nos reinados de Uzias, Jotão, Acaz e Ezequias.Fontes: o próprio texto bíblico · Isaiah

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Gadara · Hoje: Umm Qais · 32.656, 35.679 · versículo 28

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.