Mateus 4
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Sa'an nan Ruhu ya bi da Yesu zuwa cikin jeji, domin Ibilis ya gwada shi. 2Da ya yi azumi kwana arba'in dare da rana, daga baya yunwa ta kama shi. 3Sai mai jarabtar nan ya zo, ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.” 4Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake cewa, 'Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace magana da ta ke fitowa daga wurin Allah.''' 5Sa'an nan Ibilis ya kai shi tsattsarkan birni ya dora shi can kan kololuwar ginin haikali, 6ya ce masa, “In kai Dan Allah ne, to dira kasa. Domin a rubuce yake cewa, 'Zai ba mala'ikunsa umarni game da kai,' kuma, 'Za su daga ka da hannuwansu, domin kada ka yi tuntube da dutse.''' 7Yesu ya ce masa, “kuma a rubuce yake, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.''' 8Kuma, sai Ibilis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo kwarai, ya nuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. 9Ya ce masa, “Dukan wadannan zan baka idan ka rusuna ka yi mani sujada.'' 10Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.''' 11Sa'an nan Ibilis ya rabu da shi, sai kuma mala'iku suka zo suka yi masa hidima. 12To, da Yesu ya ji an kama Yahaya, sai ya tashi zuwa kasar Galili. 13Ya bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin tekun Galili, kan iyakar kasar Zabaluna da Naftali. 14Wannan ya faru domin a cika fadar annabi Ishaya cewa, 15“Kasar Zabaluna da kasar Naftali, ta bakin teku, da hayin Kogin Urdun, Galili ta al'ummai! 16Mutane mazauna duhu suka ga babban haske, sannan ga wadanda ke zaune a yankin da inuwar mutuwa, haske ya keto masu.” 17Daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin mulkin sama ya kusa.” 18Yana tafiya a bakin tekun Galili, sai ya ga wadansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, domin su masunta ne. 19Yesu ya ce masu, “Ku zo, ku biyo ni, zan mai da ku masuntan mutane.” 20Nan da nan sai suka bar tarunsu, suka bi shi. 21Da Yesu ya ci gaba da tafiya, sai ya ga wadansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da mahaifinsu Zabadi, suna gyaran tarunsu. Sai ya kira su. 22Nan take suka bar mahaifinsu da jirgin, suka bi shi. 23Yesu ya zazzaga dukan kasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar mulkin, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya a cikin mutane. 24Labarinsa ya bazu a cikin dukan kasar Suriya, kuma mutanen suka kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farfadiya, da shanyayyu. Yesu ya warkar da su. 25Taro masu yawa suka bi shi daga kasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da kasar Yahudiya, har ma daga hayin Urdun.

Você sabia?
Do deserto às margens da Galileia
- O tentador neste capítulo é chamado tanto de diabo como de Satanás, nome que significa "adversário" ou "acusador". Um dicionário bíblico observa que, no Novo Testamento, Satanás é usado de forma intercambiável com o diabo, e que ele tentou Jesus no deserto. Depois de jejuar quarenta dias e quarenta noites, Jesus recusou as exigências de transformar pedras em pão, de lançar-se do pináculo do templo e de adorar Satanás em troca dos reinos do mundo, respondendo com as Escrituras até que o diabo o deixou e anjos o serviram.Fontes: o próprio texto bíblico · Satan
- Quando Jesus soube que João tinha sido preso, retirou-se para a Galileia, deixou Nazaré e foi morar em Cafarnaum, à beira-mar, na região de Zebulom e Naftali, mudança que Mateus liga a palavras ditas por meio do profeta Isaías. Uma nota geográfica explica que a Galileia permaneceu por muito tempo ocupada por seus antigos habitantes e por isso passou a ser chamada "Galileia dos gentios". Cafarnaum não é mencionada no Antigo Testamento; um verbete sobre o lugar diz que, depois de Jesus ser expulso de Nazaré, ela se tornou a sua própria cidade.Fontes: o próprio texto bíblico · Galilee · Capernaum
- Caminhando à beira do mar da Galileia — um lago que o Evangelho de João também chama de mar de Tiberíades, com cerca de doze milhas e meia de comprimento —, Jesus chamou dois pares de irmãos que trabalhavam como pescadores. Simão, chamado Pedro, e André estavam lançando uma rede; um dicionário bíblico observa que André, de Betsaida, fora primeiro discípulo de João Batista, e que os dois irmãos só se tornaram acompanhantes habituais de Jesus depois da prisão de João. Mais adiante, Tiago e João, filhos de Zebedeu, estavam num barco com o pai consertando redes; Jesus os chamou, e os dois pares deixaram o trabalho e o seguiram.Fontes: o próprio texto bíblico · Andrew · James (Son of Zebedee) · Sea of Galilee
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 5, 25
- Galilee · 32.760, 35.527 · versículos 12, 13, 15, 23, 25
- Judea · Hoje: Judea 1 · 31.777, 35.234 · versículos 12, 25
- Nazareth · 32.702, 35.298 · versículo 13
- Jordan · Hoje: Jordan River · 31.761, 35.558 · versículos 15, 25
- Sea of Galilee · 32.819, 35.590 · versículo 18
- Syria · Hoje: Syria 2 · 33.511, 36.306 · versículo 24
- Decapolis · 32.717, 35.800 · versículo 25
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org