Nations Bible

Mateus 22

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Yesu ya sake yi masu magana da misalai, yace, 2“Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya wa dansa liyafar aure. 3Ya aiki bayinsa su kira wadanda aka gayyata su zo liyafar auren, amma suka ki zuwa. 4Sai sarkin ya sake aiken wasu bayin, yace, “Ku gaya wa wadanda aka gayyata, “Duba, na shirya liyafata. An yanka bajimaina da kosassun 'yanmarukana, an gama shirya komai. Ku zo wurin bikin auren.” 5Amma mutanen ba su dauki sakon da mahimmanci ba kuma suka yi tafiyarsu. Wani ga gonarsa, wani ga kasuwancinsa. 6Sauran kuma suka kama bayin sarkin, suka wulakanta su, suka kuma kashe su. 7Amma sarkin ya ji haushi. Ya aika sojojinsa, ku kashe masu kisan kan nan, ku kuma kone birnin su. 8Sai ya ce wa bayinsa, 'An gama shirya bikin, amma wadanda aka gayyata ba su cancanta ba. 9Saboda haka ku je bakin hanya ku gayyaci iyakar yawan mutanen da za ku samu zuwa bukin auren.' 10Bayin suka tafi hanya suka tattaro dukan mutanen da suka samu, da masu kyau da marassa kyau. Zauren auren kuwa ya cika makil da baki. 11Amma da sarkin ya zo don ya ga bakin, sai ya ga wani wanda bai sa kayan aure ba. 12Sai sarkin ya ce masa, 'Aboki, ta yaya ka shigo nan ba tare da kayan aure ba?' Mutumin kuwa ya rasa ta cewa. 13Sai sarkin ya ce wa bayinsa, 'Ku daure mutumin nan hannu da kafa, ku jefa shi cikin duhun, inda za ayi kuka da cizon hakora.' 14Gama mutane dayawa aka kira, amma kadan aka zaba.”' 15Sai Farisawan suka tafi suka shirya makirci akan yadda zasu kama shi ta maganarsa. 16Suka tura masa almajiransu, da Hirudiyawa. Suka ce ma Yesu, “Mallam, mun san kai mai gaskiya ne, kuma kana koyar da hanyar Ubangiji da gaskiya. Ba ka damu da ra'ayin kowa ba, kuma ba ka nuna bambanci a tsakanin mutane. 17To gaya mana, menene tunaninka? Ya halarta a biya haraji ga Kaisar ko a'a?” 18Amma Yesu ya gane muguntarsu yace, “Don me kuke gwada ni, ku munafukai? 19Ku nuna mani sulen harajin.” Sai suka kawo masa sulen. 20Yesu yace masu, “Hoto da sunan wanene wadannan?” 21Suka ce masa, “Na Kaisar.” Sai Yesu ya ce masu, “To ku ba Kaisar abubuwan dake na Kaisar, Allah kuma abubuwan dake na Allah.” 22Da suka ji haka, suka yi mamaki. Sai suka bar shi suka tafi. 23A ran nan sai wadansu Sadukiyawa, wadanda suka ce ba tashin matattu, suka zo wurinsa. Suka tambaye shi, 24cewa, “Mallam, Musa yace, 'Idan mutum ya mutu, bashi da 'ya'ya, dole dan'uwansa ya auri matarsa ya kuwa haifawa dan'uwansa 'ya'ya. 25Akwai wasu 'yan'uwa bakwai. Na farkon yayi aure sai ya mutu. Da shike bai bar 'ya'ya ba. Ya bar wa dan'uwansa matarsa. 26Sai dan'uwansa na biyu shi ma yayi haka, haka kuma na ukun, har zuwa dan'uwan na bakwai. 27Bayan dukansu, sai matar ta mutu. 28To a tashin matattu, matar wa zata zama a cikin su bakwai din? Don duk sun aure ta.” 29Amma Yesu ya amsa yace masu, “Kun bata, domin ba ku san litattafai ko ikon Allah ba. 30Domin a tashin matattu basu aure, ba kuma a bada su aure. Maimaikon haka, suna kama da mala'ikun sama. 31Amma game da tashin matattu, ba ku karanta abinda Allah ya fada maku ba, cewa, 32'Nine Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu'? Allah ba Allah na matattu bane, amma na rayayyu.” 33Da taron suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa. 34Amma da Farisawan suka ji cewa Yesu ya kure Sadukiyawa, sai suka tattara kansu. 35Daya daga cikinsu, masanin shari'a, yayi masa tambaya, yana gwada shi- 36“Mallam, wace doka ce mafi girma a cikin shari'a?” 37Yesu yace masa, “Ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.' 38Wannan itace babbar doka ta farko. 39Doka ta biyu kuma kamar ta take- 'Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.' 40Akan wadannan dokoki ne dukkan shari'a da annabawa suka rataya.” 41Yayin da Farisawa suke tattare wuri daya, Yesu yayi masu tambaya. 42Yace, “Me kuke tunani game da Almasihu? Shi dan wanene?” Suka ce masa, ''Dan Dauda ne.” 43Yesu yace masu, “To ta yaya kuma Dauda cikin Ruhu ya kira shi Ubangiji, yana cewa, 44“Ubangiji ya cewa wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na mai da makiyanka matakin sawayenka.” 45Idan Dauda ya kira Almasihu 'Ubangiji,' ta yaya ya zama dan Dauda?” 46Ba wanda ya iya bashi amsa, ba kuma wanda ya kara yi masa tambayoyi tun daga wannan rana.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Um banquete e um dia de perguntas

  • Os desafios deste capítulo acontecem todos no mesmo dia: fariseus e herodianos perguntam se é lícito pagar impostos a César, saduceus que dizem não haver ressurreição contam o caso de sete irmãos e uma viúva, e um especialista na Lei pergunta qual é o maior mandamento. Uma lista do episódio o chama de Debates no Templo e lhe atribui a duração de um dia; a narrativa acrescenta que, a partir daquele dia, ninguém mais ousou interrogar Jesus.Fontes: o próprio texto bíblico · Debates in the Temple
  • Ao responder aos saduceus, Jesus cita as palavras “Eu sou o Deus de Abraão, o Deus de Isaque e o Deus de Jacó” e diz que Deus não é Deus dos mortos, mas dos vivos. Um dicionário bíblico chama Abraão, filho de Terá, de pai de uma multidão; descreve Isaque como o único filho de Abraão com Sara e o mais longevo dos três patriarcas; e identifica Jacó, também chamado Israel, como o mais novo dos filhos gêmeos de Isaque e Rebeca.Fontes: o próprio texto bíblico · Abraham · Isaac · Jacob (Israel)
  • Perguntados de quem o Cristo é filho, os fariseus respondem que é de Davi. Um verbete de dicionário explica o nome Davi como Amado e o identifica como o oitavo e mais novo filho de Jessé, cidadão de Belém. Jesus então pergunta como Davi, falando no Espírito, pode chamar o Cristo de Senhor, e ninguém consegue responder.Fontes: o próprio texto bíblico · David

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.