Nations Bible

Lucas 3

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1A cikin shekara ta goma sha biyar da Tibariyus Kaisar ke mulki, Bilatus Babunti kuma ke jagorar Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, dan'uwansa Filibus yana sarautar yankin Ituriya da Tirakonitis, Lisaniyas kuma na sarautar yankin Abiliya, 2kuma zamanin da Hanana da Kayafa suke manyan firistoci, maganar Allah ta zo wurin Yahaya dan Zakariya, a cikin jeji. 3Ya yi tafiya cikin dukan yankuna da ke kewaye da Kogin Urdun, yana wa'azin baftismar tuba domin gafarar zunubai. 4Kamar yadda aka rubuta a cikin littafin annabi Ishaya, “Ga muryan wani yana kira a cikin jeji, 'Shirya hanyar Ubangiji, ka daidaita tafarkunsa! 5Za a cika kowani kwari, za a fasa kowani dutse a kuma baje kowani tudu, za a mike karkatattun hanyoyi, za a cike hanyoyi masu gargada, 6kuma dukan mutane za su ga ceton Allah.” 7Sai Yahaya ya kara fada wa taron jama'ar da ke zuwa domin ya yi masu baftisma, “Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargadeku ku guje wa fushin nan mai zuwa? 8Ku ba da 'ya'ya da sun cancanci tuba, kada ku kuma fara cewa a cikinku, 'Muna da Ibrahim a matsayin Ubanmu', domin ina gaya maku, Allah yana iya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin wadannan duwatsu. 9Yanzu kuwa, an rigaya an sa gatari a gindin itatuwa. Sabili da haka, duk itacen da bai ba da 'ya'ya masu kyau ba za a sare shi kasa a kuma jefa shi cikin wuta.” 10Sai mutanen da ke cikin taron jama'ar suka tambaye shi cewa, “To me za mu yi?” 11Ya amsa ya ce masu, “Idan wani yana da taguwa biyu, sai ya ba wanda bashi da ita daya, kuma wanda yake da abinci ya yi haka nan.” 12Masu karban haraji ma suka zo domin a yi masu baftisma, suka ce masa, “Malam, me za mu yi?” 13Ya ce masu, “Kada ku karba kudi fiye da yadda aka umarce ku.” 14Wasu sojoji ma suka tambaye shi cewa, “To, mu fa? Yaya za mu yi?” Ya ce masu, “Kada ku kwace wa wani kudi, kada ku kuma yi wa wani zargin karya. Ku dogara ga albashinku.” 15Ana nan da mutane ke sauraron zuwan Almasihu, kowa yana ta tunani a zuciyar sa game da Yahaya, ko shi ne Almasihu. 16Yahaya ya amsa ya ce masu duka, “Game da ni dai, na yi maku baftisma da ruwa, amma akwai wani tafiye wanda ya fi ni iko, ban ma isa in kwance maballin takalmansa ba. Shi zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta. 17Kwaryar shikarsa na hanun sa domin ya share masussukarsa da kyau ya kuma tara alkama a cikin rumbunsa. Amma zai kona buntun da wuta marar mutuwa. 18Da gargadi masu yawa ya yi wa mutanen wa'azin bishara. 19Yahaya kuma ya tsauta wa sarki Hirudus domin ya auri matar dan'uwansa, Hiruduya, da kuma sauran abubuwan da Hirudus ya yi. 20Amma Hirudus ya kara yin wani mugun abu. Ya sa an kulle Yahaya a cikin kurkuku. 21Ana nan, lokacin da ake yiwa dukan mutane baftisma, aka yiwa Yesu mai baftisma. Lokacin da yake yin addu'a, sai sama ta bude, 22kuma Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa a kamanin kurciya, sai wata murya ta fito daga sama, “Kai ne kaunataccen Da na. Ina jin dadin ka.” 23Ana nan Yesu da kansa, da ya fara, yana kimanin shekara talatin. Shi dan (kamar yadda ake tsammani) Yusufu ne, dan Heli, 24dan Matat, dan Lawi, dan Malki, dan Yanna, dan Yusufu, 25dan Matatiya, dan Amos, dan Nahum, dan Hasli, dan Najjaya, 26dan Ma'ata, dan Matatiya, dan Shimeya, dan Yuseka, dan Yoda, 27dan Yowana, dan Resa, dan Zarubabila, dan Shiyaltiyel, dan Niri, 28dan Malki, dan Addi, dan Kosama, dan Almadama, dan Er, 29dan Yosi, dan Aliyeza, dan Yorima, dan Matat, dan Lawi, 30dan Saminu, dan Yahuda, dan Yusufu, dan Yonana, dan Aliyakima, 31dan Malaya, dan Mainana, dan Matata, dan Natan, dan Dauda, 32dan Yesse, dan Obida, dan Bu'aza, dan Salmon, dan Nashon, 33dan Amminadab, dan Adimi, dan Arama, dan Hezruna, dan Feresa, dan Yahuda, 34dan Yakubu, dan Ishaku, dan Ibrahim, dan Tera, dan Nahor, 35dan Serug, dan Reyu, dan Feleg, dan Abiru, dan Shela, 36dan Kainana, dan Arfakshada, dan Shem, dan Nuhu, dan Lamek, 37dan Metusela, dan Anuhu, dan Yaret, dan Mahalel, dan Kainana, 38dan Enosh, dan Shitu, dan Adamu, dan Allah.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

João Batista prepara o caminho

  • Lucas situa a pregação de João no décimo quinto ano de Tibério César, enteado de Augusto, que o sucedeu em 14 d.C. e morreu em 37 d.C. O Dicionário Bíblico de Easton (1897) observa que João iniciou seu ministério público naquele ano e que Pôncio Pilatos, o sexto procurador romano da Judeia, de 26 a 36 d.C., manteve a sede em Cesareia num período que abrangeu os ministérios de João e de Jesus. Herodes Antipas, filho de Herodes, era então tetrarca da Galileia.Fontes: o próprio texto bíblico · Tiberius · Pontius Pilate · Herod Antipas
  • O capítulo situa esses acontecimentos durante o sumo sacerdócio de Anás e de Caifás. O Dicionário Bíblico de Easton (1897) registra que Anás foi sumo sacerdote de 7 a 14 d.C. e foi deposto pelo procurador romano, e que Caifás, que havia se casado com a filha de Anás, foi elevado a esse cargo em 25 d.C. O mesmo verbete sugere que os judeus ainda podiam considerar Anás o sumo sacerdote legítimo, pois a lei de Moisés mantinha o cargo por toda a vida, e que ele provavelmente servia com Caifás como presidente do Sinédrio ou como adjunto do sumo sacerdote.Fontes: o próprio texto bíblico · Annas
  • João, filho de Zacarias, era de linhagem sacerdotal: o pai era sacerdote da turma de Abias, e a mãe, Isabel, pertencia às filhas de Arão. O Dicionário Bíblico de Easton (1897) observa que a missão de João era objeto de profecia, inclusive a voz que clama no deserto em Isaías, e que seu nascimento ocorreu seis meses antes do de Jesus. Neste capítulo, ele prega um batismo de arrependimento em toda a região ao redor do Jordão, e o tetrarca Herodes depois o prende, após João o repreender por causa de Herodias.Fontes: o próprio texto bíblico · John the Baptist

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Abilene · 33.627, 36.106 · versículo 1
  • Galilee · 32.760, 35.527 · versículos 1, 19
  • Ituraea · 33.400, 35.850 · versículo 1
  • Judea · Hoje: Judea 1 · 31.777, 35.234 · versículo 1
  • Trachonitis · Hoje: Lajat · 32.969, 36.455 · versículo 1
  • Jordan · Hoje: Jordan River · 31.761, 35.558 · versículo 3

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.