Nations Bible

Lucas 24

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Da sassafe a ranar farko ta mako, suka zo kabarin, suka kawo kayan kamshi wadda suka shirya. 2Sai suka samu dutsen a mirgine shi daga kabarin. 3Suka shiga ciki, amma ba su sami jikin Ubangiji Yesu ba. 4Ya faru kuwa, yayin da suke a rikice game da wannan, ba zato, mutane guda biyu suka tsaya a gabansu da tufafi masu walkiya. 5Sa'adda matan suka sunkuyar da kansu kasa domin tsoro, suka ce wa matan, “Don me kuke neman mai rai ciki matattatu? 6Baya nan, amma ya tashi! Ku tuna fa yadda ya yi maku magana tun sa'adda ya ke Galili, 7cewa za a ba da Dan Mutum ga mutane masu zunubi su kuma giciye shi, a rana ta uku, zai tashi kuma” 8Sai matan suka tuna da kalmominsa, 9suka koma daga kabarin sai suka gaya wa sha dayan wadannan abubuwan da dukan sauran. 10Su Maryamu Magadaliya, Yuwana, Maryamu uwar Yakubu, da sauran matan da ke tare da su suka ba manzanni rohoton wadannan abubuwan. 11Amma manzannin suka dauki maganar kamar ba ta da amfani, kuma ba su bada gaskiya ga matan ba. 12Duk da haka Bitrus ya tashi, sai ya gudu zuwa kabarin, ya sunkuya yana kallon ciki, sai ya gan likaftani linin kadai. Sa'annan Bitrus ya tafi gidansa, yana ta mamakin abinda ya faru. 13A ranan nan, sai ga biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani kauye suna Imawus, wanda nisansa kimanin mil ne daga Urushalima. 14Suna tattaunawa da junansu game da dukan abubuwan da suka faru. 15Sai ya zama da cewa, sa'adda su ke tattaunawa tare da tambayoyi, sai Yesu da kansa ya matsa kusa yana tafiya tare da su. 16Amma idanunsu basu iya ganewa da shi ba. 17Yesu ya ce masu, “Menene ku ke magana akai sa'adda ku ke tafiya?” Suka tsaya a wurin suna bakin ciki. 18Daya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa, “Kai ne kadai mutumin da ke Urushalima wanda bai san abubuwan da suka faru a can a wannan kwanakin ba?” 19Yesu ya ce masu, “Wadanne abubuwa?” Suka amsa masa, “Abubuwa game da Yesu ba Nazarat, wanda ya ke annabi ne, mai manyan ayuka da kalmomi daga Allah da kuma mutane. 20Da yadda manyan firistoci da masu mulkinmu suka bada shi domin a hukunta shi ga mutuwa a kuma giciye shi. 21Amma mun yi begen cewa shine wanda za ya yantar da Isra'ila. I, bayan wannan kuma, yanzu kwana uku kenan tunda wadannan abubuwan suka faru. 22Amma har'ila yau, wadansu mata da ke tare da mu sun yi mana abin al'ajabi, da suka kasance a kabarin tunda sassafe. 23Sa'adda ba su sami jikinsa ba, suka zo, da cewa su ma sun ga wahayin mala'iku wadanda suka ce masu ya na da rai. 24Wasu maza wadanda ke tare da mu suka tafi kabarin, suka tarar da shi kamar yadda matan suka fada. Amma ba su ganshi ba.” 25Yesu ya ce masu, “Ku mutane masu wauta da marasa ba da gaskiya ga abin da annabawa suka fada! 26Bai zama dole ne Almasihu ya sha wahalan wadannan abubuwan ba, ya kuma shiga cikin daukakarsa?” 27Sa'annan da farko daga Musa da har zuwa dukan annabawa, Yesu ya fasara masu duka abubuwa da ke game da kansa a dukan littattafai. 28Da suka yi kusa da kauyen, inda suke tafiya, ko da yake Yesu ya yi kamar zai wuce su. 29Amma suka tilasta shi, cewa, “Ka zauna da mu, gama yamma ta yi kusa rana kuma ta kusa karewa.” Sai Yesu ya tafi ya zauna da su. 30Ya faru cewa, sa'adda ya zauna tare da su domin ya ci abinci, sai ya dauki gurasan, ya albarkace shi, ya kakkarya, sai ya ba su. 31Sa'annan idanunsu suka bude, da suka gane shi, sai ya bace daga garesu, 32Suka ce wa junansu, ashe zuciyarmu ba ta yi kuna a cikinmu ba, sa'adda yake magana da mu a hanya, sa'adda ya bude mana littattafai?” 33Suka tashi a wancan sa'a, sai suka koma Urushalima. Suka sami sha dayan nan tare, da wadanda suke tare da su, 34cewa, “Lalle ne Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman.” 35Sai suka fadi abubuwan da suka faru a hanya, da yadda aka bayyana masu Yesu sa'adda ya kakkarya gurasa. 36Sa'adda suke fadin wadannan abubuwan, sai Yesu ya tsaya a sakaninsu, sai ya ce masu, “Salama a gareku.” 37Amma suka firgita suna cike da tsoro, suna tsammani sun ga fatalwa. 38Yesu ya ce masu, don me ku ke damuwa? Don me tambayoyi ke tasowa a zuciyarku? 39Duba hannayena da kafafuna, cewa nine da kaina. Taba ni ku gani. Gama ruhu ba shi da jiki da kashi, kamar yadda ku ka ga nake da su.” 40Bayan da ya fadi wannan, sai ya nuna masu hannayensa da kafafunsa. 41Sa'adda suke cike da farin ciki, da mamaki, Yesu ya ce masu, “Kuna da wani abinci?” 42Sai suka bashi gasasshen kifi. 43Yesu ya karba, ya ci a gabansu. 44Sai ya ce masu, “Sa'adda nake tare da ku na gaya maku cewa duka abin da aka rubuta a cikin dokokin Musa da na annabawa da Zabura dole su cika.” 45Sai ya bude hankalinsu, saboda su gane littattafai. 46Ya ce masu, “A rubuce yake, cewa Almasihu za ya sha wuya, zai tashi kuma daga matattu a rana ta uku. 47Ku yi wa'azin tuba da gafarar zunubai a cikin sunansa ga dukan al'ummai, ku fara daga Urushalima. 48Ku shaidu ne ga wadannan abubuwan. 49Duba, ina aiko da alkawarin Ubana a kanku. Amma ku jira a birni, sai an suturta ku da iko daga sama.” 50Sa'annan Yesu ya tafi tare da su har sai da suka kai kusa da Betanya. Sai ya daga hannunsa ya albarkace su. 51Ya zama sa'adda yake sa masu albarka, ya bar su sai aka dauke shi zuwa cikin sama. 52Sai suka yi masa sujada, suka komo Urushalima da murna mai yawa. 53Kullayaumin suna cikin haikali, suna albarkatar Allah.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

A manhã da ressurreição e o caminho de Emaús

  • Lucas descreve Emaús como uma aldeia a cerca de sete milhas de Jerusalém. O Easton's Bible Dictionary (1897) cita essa distância como sessenta furlongs e registra duas identificações: el-Kubeibeh, a mais de sete milhas a noroeste de Jerusalém, cujo nome, 'pequena cúpula', vem dos restos de uma igreja dos cruzados que ainda se encontram ali, e Khurbet Khamasa, 'as ruínas de Khamasa', a cerca de oito milhas a sudoeste, onde também há ruínas dos cruzados.Fontes: Emmaus · o próprio texto bíblico
  • Maria Madalena, Joana, Maria, mãe de Tiago, e outras mulheres que iam com elas foram quem contou aos apóstolos o que havia acontecido no túmulo. Maria Madalena recebe o nome de Magdala, sua terra natal, e o Easton's Bible Dictionary (1897) considera um equívoco identificá-la com a mulher chamada 'pecadora' em Lucas 7. Joana, esposa de Cuza, administrador de Herodes Antipas, tetrarca da Galileia, era uma das mulheres que serviam a Jesus, e o mesmo dicionário diz que ele lhe apareceu depois da ressurreição.Fontes: Mary Magdalene · Joanna · o próprio texto bíblico
  • Um dos dois discípulos no caminho chama-se Cléopas, forma abreviada de Cleópatros. O Easton's Bible Dictionary (1897) diz que nada se sabe de certo sobre ele e que não é seguro que fosse o Clopas de João 19:25 nem o Alfeu de Mateus 10:3, embora possa ter sido.Fontes: Cleophas · o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Galilee · 32.760, 35.527 · versículo 6
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 13, 18, 33, 47, 49, 52
  • Nazareth · 32.702, 35.298 · versículo 19

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.