Lucas 20
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Ana nan wata rana, Yesu yana kan koyarwa a haikali da wa'azin bishara, sai shugaban firistoci da marubuta suka zo wurinsa da dattawa. 2Suka yi magana, su na ce masa, “Gaya mana da wanne iko ne ka ke yin wadannan abubuwan? Ko wanene ya baka wannan ikon?” 3Ya amsa sai ya ce masu, “Ni ma zan yi maku tambaya. Gaya mani game 4da baptisman Yahaya. Daga sama take ko kuwa daga mutane ne?” 5Sai suka yi mahawara da junansu, suna cewa, “In mun ce, 'Daga sama,' zai ce, 'To don me ba ku ba da gaskiya gareshi ba?' 6Amma in mun ce, 'Daga mutane ne,' dukan mutane za su jejjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata a ransu Yahaya annabi ne.” 7Sai suka amsa cewa ba su san ko daga ina ne take ba. 8Yesu yace masu, “To haka ni ma ba zan gaya maku ko da wanne iko nake yin wadannan abubuwan ba.” 9Ya gaya wa mutane wannan misali, “Wani mutum ya dasa gonar inabi, ya ba wadansu manoma jinginarta, sai ya tafi wata kasa har ya dade. 10Da lokacin girbi ya yi sai ya aiki wani bawansa zuwa wurin manoman, saboda su bashi daga cikin anfanin gonar. Amma manoman suka doke shi, sai suka kore shi hannu wofi. 11Ya aike wani bawa kuma sai suka daddoke shi, suka kunyatar da shi, suka kore shi hannu wofi. 12Ya kuma sake aike na uku suka yi masa rauni, suka jefar da shi a waje. 13Sai mai gonar inabin ya ce, 'Me zan yi? Zan aiki kaunattacen dana. Watakila zasu ba shi daraja.' 14Amma sa'adda manoman suka gan shi, suka yi shawara a tsakaninsu, cewa, 'Wannan ne magajin. Bari mu kashe shi, saboda gadon ya zama namu.' 15Suka jefar da shi waje daga gonar, suka kashe shi. Menene ubangijin gonar inabin zai yi da su? 16Zai zo ya halakar da wadannan manoma, sai ya ba wadansu gonar.” Da suka ji wannan, suka ce, “Allah ya sawake!” 17Amma Yesu ya kalle su, sai yace, “Menene ma'anar wannan nassi? 'Dutsen da magina suka ki, an mayar da shi kan kusurwa'? 18Duk wanda ya fadi kan dutsen zai farfashe. Amma duk wanda dutsen ya fadi a kansa, zai rugurguza shi.” 19Sai marubutan da manyan firistocin suka so su kama shi a wannan sa'a, domin sun sani ya yi wannan misali a kansu ne. Amma sun ji tsoron mutane. 20Suna fakonsa, suka aiki magewaya, wadanda suke kamar masu adalci, saboda su sami kuskure cikin maganarsa, don su mika shi ga hukumci da kuma ikon gwamna. 21Suka tambaye shi, cewa, “Malam, mun sani da cewa kana fada da koyar da abin ke daidai, kuma ba wanda yake cusa maka ra'ayi, amma kana koyar da gaskiya game da hanyar Allah. 22Wai shin doka ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?” 23Amma Yesu ya gane makircinsu, sai ya ce masu, 24“Nuna mani dinari. Sifar wanene da kuma rubutun wanene akan sa?” Suka ce, “Na Kaisar ne.” 25Sai ya ce masu, “To sai ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar, ku kuma ba Allah, abin da ke na Allah.” 26Marubutan da manyan firistocin ba su sami abin zargi cikin maganarsa, a gaban mutane ba. Suka yi mamakin amsar sa, ba su kuma ce komai ba. 27Sa'adda wadansu Sadukiyawa suka zo wurinsa, wadan da suka ce babu tashin mattatu, 28suka tambaye shi, cewa, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa idan dan'uwan mutum ya mutu, mai mace kuma ba shi da yaro, sai dan'uwansa ya auri matar, ya samar wa dan'uwansa yaro. 29Akwai 'yan'uwa guda bakwai kuma na farin ya yi aure, sai ya mutu babu da, 30haka ma na biyun. 31Na ukun ya aure ta, haka nan na bakwai ma bai bar yaya ba, har suka mutu. 32Daga baya sai matar ma ta mutu. 33To a ranar tashin mattatu, matar wa za ta zama? Domin duka bakwai din sun aure ta.” 34Yesu ya ce masu, “'Ya'yan duniyan nan suna aure, ana kuma ba da su ga aure. 35Amma wadanda aka ga cancantarsu a waccan tsara, sun isa su sami tashin mattatu, ba za suyi aure ko a aurar da su ba. 36Gama ba za su mutu kuma ba, domin suna daidai da mala'iku kuma su 'ya'yan Allah ne, da shike su 'ya'yan tashin matattu ne. 37Amma batun tashi matattu, ko Musa ma ya nuna wannan, a cikin jeji, inda ya kira Ubangiji, Allah na Ibrahim da kuma Allah na Ishaku da Allah na Yakubu. 38Yanzu shi ba Allahn matattu ba ne, amma na masu rai, saboda duka suna raye a wurinsa.” 39Wadansu marubuta suka amsa, “Malam, ka amsa da kyau.” 40Gama ba su sake yi masa wadansu tambayoyi ba. 41Yesu ya ce masu, “Yaya suke cewa Almasihu dan Dauda ne? 42Gama Dauda da kansa ya ce a cikin littafin Zabura, Ubangiji ya ce wa Ubangiji na, 'Zauna a hannun dama na, 43sai na maida makiyanka a karkashin tafin sawunka.' 44Dauda ya kira Kristi 'Ubangiji', to ta yaya ya zama dan Dauda?” 45Dukan mutane suna ji ya ce wa almajiransa, 46“Ku yi hankali da marubuta, wadanda suna son tafiya da manyan riguna, suna kuma son a gaishe su a cikin kasuwanni, da mayan wuraren zama a cikin majami'u, da kuma manyan wurare a wurin bukukkuwa. 47Suna kuma kwace wa gwamraye gidaje, suna kuma badda kama ta wurin yin doguwar addu'a. Wadannan za su sha hukumci mai girma.”

Você sabia?
Debates nos pátios do templo
- Quando lhe perguntam com que autoridade age, Jesus pergunta se o batismo de João vinha do céu ou dos homens. Os líderes não respondem: se disserem que vinha do céu, ele pode perguntar por que não creram nele; se disserem que vinha dos homens, temem que o povo os apedreje, pois a multidão está convencida de que João era profeta. O Easton's Bible Dictionary (1897) descreve João Batista como de linhagem sacerdotal — seu pai, Zacarias, sacerdote do turno de Abias, e sua mãe, Isabel, das filhas de Arão — e observa que a missão dele foi objeto de profecia.Fontes: o próprio texto bíblico · John the Baptist
- Alguns saduceus, que dizem não haver ressurreição, perguntam de quem seria esposa uma mulher se, como Moisés escreveu, sete irmãos a tivessem desposado, um após o outro, para suscitar descendência. Jesus aponta a passagem da sarça ardente, em que Moisés chama o Senhor de Deus de Abraão, Deus de Isaque e Deus de Jacó, e afirma que Deus é Deus dos vivos. O Easton's Bible Dictionary chama Abraão, filho de Terá, de pai de uma multidão; Isaque, de único filho de Abraão com Sara; e Jacó, também chamado Israel, de segundo gêmeo de Isaque e Rebeca, aquele que segue nos calcanhares de outro.Fontes: o próprio texto bíblico · Abraham · Isaac · Jacob (Israel)
- Jesus pergunta como o Cristo pode ser filho de Davi se o próprio Davi, no livro dos Salmos, o chama de Senhor. O Easton's Bible Dictionary identifica Davi como o oitavo e mais novo filho de Jessé, cidadão de Belém, que no início apascentava as ovelhas do pai nas terras altas de Judá.Fontes: o próprio texto bíblico · David
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org