Nations Bible

Lucas 10

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Bayan wadannan abubuwa, Ubangiji ya sake nada wadansu saba'in ya aike su biyu biyu, domin su tafi kowanne birni da wurin da yake niyyan zuwa. 2Ya ce da su, “Girbin yana da yawa, amma ma'aikatan sun yi kadan. Saboda haka kuyi addu'a sosai ga Ubangijin girbin, domin ya aiko da ma'aikata cikin gonarsa. 3Ku tafi, duba na aike ku kamar 'yan raguna cikin kyarkyetai. 4Kada ku dauki jakan kudi, ko jakar matafiyi, ko takalma, kada ku gai da kowa a kan hanya. 5Dukan gidan da ku ka shiga, ku fara cewa, 'Bari salama ta kasance a wannan gida.' 6Idan akwai mutum mai salama a gidan, salamar ku za ta kasance a kansa, amma idan babu, salamar ku za ta dawo wurinku. 7Ku zauna a wannan gidan, ku ci ku sha abin da suka tanada maku. Gama ma'aikaci ya wajibci ladansa. Kada ku bi gida gida. 8Dukan birnin da ku ka shiga kuma sun karbe ku, ku ci abin da suka sa a gabanku. 9Ku warkar da marasa lafiyar da ke wurin. Ku ce da su, 'Mulkin Allah ya zo kusa da ku.' 10Amma dukan birnin da ku ka shiga, idan ba su karbe ku ba, ku tafi cikin titunansu, ku ce, 11'Ko kurar birninku da ta like a kafafunmu, mun karkabe maku ita a matsayin shaida a kanku! Amma ku sani mulkin Allah ya zo kusa da ku.' 12Na gaya maku, a ranar shari'a Saduma za ta fi wannan birni samun sauki. 13Kaiton ki, Korasinu! Kaiton ki, Baitsaida! Ayyuka masu girma da aka yi a cikinku, da an yi su a cikin Taya da Sidon, da sun tuba tuntuni a zaune cikin toka da tufafin makoki. 14Amma a ranar shari'a Taya da Sidon za su fi ku samun sauki. 15Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani har zuwa sama za a daukaka ki? Babu, za a gangarar dake har zuwa hadas. 16Wanda ya saurare ku ya saurare ni, wanda ya ki ku, ya ki ni, kuma wanda ya ki ni, ya ki wanda ya aiko ni.” 17Su saba'in din suka dawo da murna, suna cewa, “Ubangiji, har ma aljanu suna yi mana biyayya, a cikin sunanka.” 18Sai Yesu ya ce masu, “Na ga Shaidan yana fadowa daga sama kamar walkiya. 19Duba, na ba ku iko ku taka macizai da kunamai, da kuma kan dukan ikon magabci, kuma ba zai iya yin illa a gareku ba ko kadan. 20Amma duk da haka kada ku yi murna a kan wannan kadai cewa ruhohi suna yi maku biyayya, amma ku yi murna domin an rubuta sunayenku a cikin sama.” 21Cikin wannan lokacin, ya yi farin ciki kwarai cikin Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na ba ka girma, ya Uba, Ubangijin sama da kasa. Domin ka rufe wadannan abubuwa daga masu hikima da ganewa, ka bayyana su ga wadanda ba koyayyu ba ne, kamar kananan yara. I, Uba gama haka ne ya gamshe ka.” 22Dukan abu, Ubana ya damka su gare ni, kuma babu wanda ya san Dan, sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Dan. Sai kuma wanda Dan ya yi niyyar ya bayyana Uban a gareshi.” 23Ya juya wajen almajiran, ya ce da su a kadaice, “Masu albarka ne su wadanda suka ga abin da kuke gani. 24Na fada maku, annabawa da yawa, da sarakuna da yawa sun so da sun ga abubuwan da kuke gani, amma ba su gani ba. Kuma sun so da sun ji abubuwan da kuke ji, amma ba su ji su ba.” 25Sai ga wani malamin shari'ar Yahudawa, ya zo ya gwada shi da cewa, “Malam, me zan yi domin in gaji rai na har abada?” 26Sai Yesu ya ce masa, “Yaya kake karanta abin da aka rubuta cikin shari'a?” 27Ya amsa ya ce,”Dole ne ka kaunaci Ubangiji Allah da dukan zuciyarka, da dukan ranka da dukan karfinka, da dukan lamirinka. Ka kuma kaunaci makwabcinka kamar kanka.” 28Yesu ya ce ma sa, “Ka amsa daidai, idan ka yi haka za ka rayu.” 29Amma, malamin ya na so ya 'yantar da kansa, sai ya ce da Yesu, “To, wanene makwabcina?” 30Ya amsa ya ce, “Wani mutum yana tafiya daga Urushalima za shi Yariko. Sai ya fada hannun mafasa, suka tube shi, suka kwace dukan abin da ya ke da shi, suka yi masa duka, suka bar shi kamar matacce. 31Ya zama sai ga wani firist ya na bin wannan hanya, da ya gan shi sai ya bi ta gefe daya ya wuce. 32Haka kuma sai ga wani Balawi, sa'adda ya zo wurin, ya gan shi sai ya bi ta wani gefe ya wuce shi. 33Amma wani Basamariye, ya na tafiya sa'adda ya zo wurin da mutumin yake, sa'adda ya ga mutumin sai tausayi ya kama shi. 34Ya zo inda mutumin yake, ya daure masa raunukan da aka ji masa, yana shafa masu mai da ruwan inabi. Ya dora shi a kan dabbarsa ya kawo shi wurin kwana, ya kula da shi 35Washegari ya kawo dinari biyu, ya ba mai wurin kwanan ya ce 'Ka kula da shi, idan ma ka kashe fiye da haka, idan na dawo zan biya ka.' 36A cikinsu ukun nan, wanene kake tsammani makwabcin wannan mutum da ya fada hannun 'yan fashi?” 37Sai malamin ya ce, “Wannan da ya nuna masa jinkai” Sai Yesu yace masa, “Ka je kai ma ka yi haka.” 38Sa'adda suke tafiya, sai ya shiga cikin wani kauye, sai wata mata mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. 39Tana da 'yar'uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a kafafun Ubangiji tana jin abin da yake fadi. 40Amma ita Marta ta na ta kokari ta shirya abinci. Sai ta zo wurin Yesu ta ce, “Ubangiji, ba ka damu ba 'yar'uwata ta bar ni ina ta yin aiki ni kadai? Ka ce da ita ta taya ni.” 41Amma Ubangiji ya amsa ya ce da ita, “Marta, Marta, kin damu a kan abubuwa da yawa, 42amma abu daya ne ya zama dole. Maryamu ta zabi abu mafi kyau, wanda ba za a iya kwace mata ba.”

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

A missão, as cidades e Marta e Maria

  • O Dicionário Bíblico de Easton (1897) identifica Corazim, nomeada nos ais deste capítulo junto com Betsaida e Cafarnaum, com Kerazeh, cerca de duas milhas e meia subindo o Wady Kerazeh a partir de Cafarnaum. Diz que, depois que Jesus foi expulso de Nazaré, Cafarnaum passou a ser a sua própria cidade. O capítulo compara essas cidades com Tiro e Sidom; o dicionário chama Sidom de primeiro lar dos fenícios na costa da Palestina e de cidade-mãe de Tiro, cerca de vinte e cinco milhas ao norte de Tiro.Fontes: o próprio texto bíblico · Chorazin · Capernaum · Sidon
  • O Dicionário Bíblico de Easton (1897) dá ao nome Marta o sentido de amargura e afirma que ela, a irmã Maria e o irmão Lázaro moravam em Betânia, sendo Marta provavelmente a mais velha. Como este trecho chama a casa de casa dela, o dicionário observa que alguns supuseram que ela era viúva e que o irmão e a irmã se hospedavam com ela. Descreve Marta como ansiosa e atarefada no cuidado com o hóspede, ao contrário de Maria, que se sentou aos pés de Jesus e escutou.Fontes: o próprio texto bíblico · Martha · Mary (sister of Lazarus)
  • O Senhor designa outros setenta e dois e os envia dois a dois adiante dele, e uma cronologia de acontecimentos situa esse envio no ano 29 d.C. Quando voltam, alegres porque até os demônios se submetem em nome dele, ele diz que viu Satanás cair do céu como um relâmpago. O Dicionário Bíblico de Easton (1897) explica o nome Satanás como adversário ou acusador e observa que o Novo Testamento o usa de modo intercambiável com o diabo mais de trinta vezes.Fontes: o próprio texto bíblico · 70 Sent Out · Satan

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Sidon · Hoje: Sandikli archaeological site in Sidon · 33.561, 35.372 · versículos 13, 14
  • Tyre · 33.271, 35.196 · versículos 13, 14
  • Jericho · Hoje: Tell el Alayiq · 31.852, 35.436 · versículo 30
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 30, 38

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.