João 3
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1akwai wani Bafarise da ake kira Nikodimu, shugaba a cikin Yahudawa. 2Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dare ya ce masa, “Rabbi, mun sani cewa kai malami ne da kazo daga wurin Allah, gama ba wanda zai iya yin wadannan alamu da kake yi sai idan Allah na tare da shi.” 3Yesu ya amsa masa, “Hakika, hakika, idan ba a sake haifuwar mutum ba, ba zai iya ganin mulkin Allah ba.” 4Nikodimu ya ce masa, “Yaya za a sake haifuwar mutum bayan ya tsufa? Ba zai iya sake shiga cikin cikin uwarsa kuma a haife shi ba, zai iya?” 5Yesu ya amsa, “Hakika, hakika, idan ba a haifi mutum da ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga cikin mulkin Allah ba. 6Abin da aka haifa ta wurin jiki, jiki ne, kuma abin da aka haifa ta wurin Ruhu, Ruhu ne. 7Kada ka yi mamaki don na ce maka, 'dole a maya haifuwar ka.' 8Iska takan hura duk inda ta ga dama. Ka kan ji motsin ta, amma ba ka san inda ta fito ko inda za ta tafi ba. Haka duk wanda aka haifa daga Ruhu.” 9Nikodimu ya amsa yace masa, “Yaya wannan zai yiwu?” 10Yesu ya amsa yace masa, “Kai malami ne a Israila amma ba ka san wadannan al'amura ba? 11Hakika, hakika, ina gaya maka, muna fadin abubuwan da muka sani, kuma muna shaida abubuwan da muka gani. Duk da haka ba ku karbi shaidar mu ba. 12Idan na gaya maka abubuwan da ke na duniya amma baka gaskata ba, to yaya zaka gaskata idan na gaya maka abubuwa na sama? 13Babu wanda ya taba hawa zuwa sama sai dai shi wanda ya sauko daga sama: wato Dan Mutum. 14Kamar yadda Musa ya ta da maciji a jeji, haka ma dole a ta da Dan Mutum 15domin dukan wadanda suka bada gaskiya gareshi su sami rai na har abada. 16Gama Allah ya kaunaci duniya sosai, har ya ba da makadaicin Dansa, domin duk wanda ya bada gaskiya gareshi, kada ya mutu, amma ya samu rai madawwami. 17Gama Allah bai aiko da Dansa cikin duniya domin ya kayar da duniya ba, amma domin a ceci duniya ta wurin sa. 18Duk wanda ya bada gaskiya gare shi ba a kayar da shi ba, amma duk wanda bai bada gaskiya gare shi ba an riga an kayar da shi, domin bai bada gaskiya ga sunan wannan da shi kadai ne Dan Allah ba. 19Wannan shi ne dalilin shari'ar, domin haske ya zo duniya, amma mutane suka kaunaci duhu fiye da hasken, sabili da ayyukan su na mugunta ne. 20Domin duk wanda ke mugayen ayyuka ya ki haske, kuma baya zuwa wurin hasken domin kada ayyukansa su bayyanu. 21Sai dai duk wanda yake aikata gaskiya kan zo wurin hasken domin ayyukansa, da ake aiwatarwa ga Allah, su bayyanu. 22Bayan wannan, Yesu da almajiransa suka tafi kasar Yahudiya. A can ya dan zauna tare da su ya kuma yi Baftisma. 23Yahaya ma yana Baftisma a Ainon kusa da Salim domin akwai ruwa da yawa a can. Mutane na zuwa wurin sa yana masu Baftisma, 24domin a lokacin ba a jefa Yahaya a kurkuku ba tukuna. 25Sai gardama ta taso tsakanin almajiran Yahaya da wani Bayahude akan al'adun tsarkakewa. 26Suka je wurin Yahaya suka ce, “Rabbi, wanda yake tare da kai a dayan ketaren kogin Urdun, kuma ka shaida shi, duba, yana baftisma, kuma mutane duka suna zuwa wurin sa.” 27Yahaya ya amsa, “Mutum ba zai iya samun wani abu ba sai an ba shi daga sama. 28Ku da kanku zaku shaida na ce, 'Ba ni ne Almasihu ba' amma amaimakon haka, 'an aiko ni kafin shi.' 29Amaryar ta angon ce. Yanzu abokin angon, wanda ke tsaye yana saurarensa, yana murna sosai saboda muryan angon. Murnata ta cika domin wannan. 30Dole shi ya karu, ni kuma in ragu. 31Shi wanda ya fito daga sama ya fi kowa. Shi Wanda ya zo daga duniya, na duniya ne, kuma game da duniya yake magana. Shi wanda ya fito daga sama yana saman kowa. 32Ya shaida abubuwan da ya ji ya kuma gani, amma babu wanda ya karbi shaidarsa. 33Duk wanda ya karbi shaidarsa ya tabbatar Allah gaskiya ne. 34Domin duk wanda Allah ya aika kan yi magana da kalmomin Allah. Domin bai bada Ruhun da ma'auni ba. 35Uban ya kaunaci Dan, ya kuma ba da dukan komai a hanunsa. 36Shi wanda ya bada gaskiya ga Dan ya na da rai madawwami, amma wanda ya ki yiwa Dan biyayya ba zai ga rai ba, amma fushin Allah na kansa.

Você sabia?
O novo nascimento e o testemunho de João
- Nicodemos, cujo nome significa "o povo é vencedor", era fariseu e membro do Sinédrio. Ele foi a Jesus de noite para conhecer melhor o seu ensino, e o Evangelho o chama de líder dos judeus; Jesus se dirige a ele como mestre de Israel.Fontes: Nicodemus · o próprio texto bíblico
- Depois dessa conversa, Jesus e seus discípulos foram para a região rural da Judeia, que sob os romanos era a mais meridional das três divisões da Palestina. João também batizava em Enom, perto de Salim, porque ali havia água em abundância; Salim, cujo nome significa "pacífico", ficava a oeste do Jordão. Enom significa "fontes", e o Dicionário Bíblico de Easton (1897) situa o lugar provavelmente perto da nascente superior do Wady Far'ah, um vale aberto cheio de fontes que vai do monte Ebal até o Jordão.Fontes: o próprio texto bíblico · Judea · Aenon · Salim
- Neste capítulo, João diz a seus discípulos que não é o Cristo, mas que foi enviado adiante dele, e a narrativa observa que ele ainda não tinha sido preso. O Dicionário Bíblico de Easton (1897) o descreve como o precursor de Jesus, de descendência sacerdotal, e diz que sua missão foi objeto de profecia.Fontes: o próprio texto bíblico · John the Baptist
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 22
- Judea · Hoje: Judea 1 · 31.777, 35.234 · versículo 22
- Jordan · Hoje: Jordan River · 31.761, 35.558 · versículo 26
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org