João 19
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Sai Bilatus yayi wa Yesu bulala. 2Sojojin kuwa suka saka rawanin kaya. Suka kuwa dora wa Yesu a kai suka sa mashi kaya irin na saurata. 3Suka zo wurin sa sukace, “Ranka ya dade, sarkin Yahudawa! sai suka nushe shi. 4Sai Bilatus ya sake fita waje yace masu, “Dubi, zan kawo maku mutumin domin ku sani ban same shi da wani laifi ba”, 5Yesu kuwa ya fito, da rawanin kaya da kaya irin na sarauta. Sai Bilatus yace “Ga mutumin nan”. 6Da manyan firistocin tare da yan majalisar suka ga Yesu, sai suka yi ta ihu suna cewa “A gicciye shi, A gicciye shi” Sai Bilatus yace masu, “ku dauke shi ku gicciye shi, ni kam ban same shi da wani laifi ba”. 7Sai Yahudawan sukace mashi, “Ai muna da shari'a, kuma bisa ga shari'ar ya cancanci mutuwa domin ya mai da kansa Dan Allah”. 8Da Bilatus ya ji wannan zance sai ya tsorata kwarai. 9Sai ya sake shiga fadar Gwamna, yace wa Yesu, “Daga ina ka fito?” amma Yesu bai amsa mashi ba. 10Sai Bilatus yace masa “Ba zaka yi mani magana ba? Baka san ina da iko in sake ka ba, kuma in gicciye ka? 11Yesu ya amsa masa, “Ai ba ka da iko a kaina sai dai in an baka daga sama, Saboda haka, wanda ya mika ni a gare ka shine mafi zunubi”. 12Da jin haka, sai Bilatus yayi kokari a sake shi, amma sai Yahudawa suka tada murya sukace, “In ka saki mutumin nan, kai ba abokin Kaisar bane, duk wanda ya maida kansa sarki, ya sabawa Kaisar”. 13Da Bilatus ya ji irin maganganunsu sai ya fito da Yesu waje ya kuma zauna akan kujeransa a inda ake kira “Dakalin shari'a,” a Yahudanci kuma, “Gabbata.” 14To a ran nan ana shirye shiryen idin ketarewa, da misalin sa'a ta shidda kenan, wato tsakar rana, Bilatus yace wa Yahudawan “Ga sarkin ku!” 15Su kuwa suka yi ihu, a tafi da shi, a tafi da shi, a gicciye shi, Bilatus yace masu “In gicciye sarkin ku? Sai manyan firistocin sukace “Ba mu da wani sarki sai Kaisar”. 16Sai Bilatus ya mika Yesu domin su gicciye shi. 17Sai suka tafi da Yesu, ya fito yana dauke da gicciyen zuwa wurin da ake kira “Wurin kwalluwa” da Yahudanci kuma “Golgota”. 18Suka gicciye Yesu a wurin, tare da wasu mutum biyu, daya a kowane gefe, Yesu kuwa na tsikiya. 19Bilatus kuwa ya rubuta wata alama a kan gicciyen, “YESU BANAZARE, SARKIN YAHUDAWA”. 20Yahudawa da yawa kuwa suka karanta wannan alama domin wurin da aka gicciye Yesu yana kusa da Birnin. Alamar kuwa an rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da Helenanci. 21Sai manyan firistocin yahudawa sukace wa Bilatus, kada ka rubuta sarkin Yahudawa, amma kace, 'wannan yace “Ni ne sarkin Yahudawa”'. 22Bilatus kuwa ya amsa, “Abinda na rubuta na rubuta kenan.” 23Bayan da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka yayyaga rigarsa kashi hudu, kowane soja da nasa, kashin, sai kuma alkyabbar. Alkyabbar kuwa bata da dinki an saka tane daga sama har kasa. 24Sai sukace wa junansu, “Kada mu yaga alkyabbar, amma kuzo mu jefa kuri'a a kan ta mu gani ko wanene zai dauke ta, anyi haka ne domin a cika nassi cewa “Sun raba rigata a tsakaninsu, sun kuwa jefa kuri'a domin alkyabbata. 25Sojojin suka yi wadannan abubuwa. Uwar Yesu, da 'yar'uwarta, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya. Wadannan mataye suna tsaye kusa da gicciyen Yesu. 26Da Yesu ya ga mahaifiyarsa da almajirin nan da yake kauna tsaye kusa da juna, yace, “Mace, dubi, dan ki!” 27Sai yace wa almajirin, “Dubi, mahaifiyarka!” Daga wannan sa'a almajirin ya dauke ta zuwa gidansa. 28Bayan wannan Yesu, saboda ya san yanzu komai ya kammala, domin a cika nassin, sai yace “Ina jin kishi. 29A gefensu kuma akwai gora cike da ruwan inabi mai tsami, sai suka tsoma soso a cikin ruwan inabin mai tsami suka daura a wata sanda sai suka mika masa a baki. 30Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin, sai yace “An gama” Sai ya sunkuyar da kansa ya kuwa saki ruhunsa. 31Sai Yahudawan, domin ranar shirye shirye ne, domin kada a bar jikunansu akan gicciye har ranar asabacin (domin asabacin rana ce mai muhimmanci), suka roki Bilatus ya kakkarye kafafunsu kuma ya saukar da su. 32Sai sojojin suka zo suka karya kafafun mutum na farko da kuma mutum na biyun wadanda aka gicciye tare da Yesu. 33Da suka iso kan Yesu sai suka tarar ya riga ya mutu, sai basu kuwa karya kafafunsa ba. 34Duk da haka daya daga cikin sojojin ya soki kuibin shi da mashi, nan da nan sai jini da ruwa suka fito. 35Wanda ya ga wannan, shi ya zama shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya sani cewa abinda ya fada gaskiya ne saboda ku ma ku gaskata. 36Wadannan sun faru ne domin a cika nassi, “Babu ko daya daga cikin kasusuwansa da za'a karya”. 37Kuma wani nassin yace, “Zasu dube shi wanda suka soka.” 38Bayan wadannan abubuwa, Yusufu mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne (amma a boye saboda tsoron Yahudawa) ya roki Bilatus izini domin ya dauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya bashi izini, sai Yusufu yazo ya dauki jikin. 39Nikodimu ma ya zo, wanda da farko ya zo wurin Yesu da daddare, ya kawo hadin man kamshi na mur da al'ul wajen nauyin awo dari. 40Sai suka dauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lillin tare da kayan kamshin nan, domin jana'iza bisa ga al'adar Yahudawa. 41To a wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu, a cikin lambun kuma akwai sabon kabari wanda ba'a taba sa kowa ba. 42Da yake ranar shirye shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuwa na kusa, sai suka sa Yesu a ciki.

Você sabia?
Julgamento, cruz e sepultamento
- Pôncio Pilatos, o sexto procurador romano da Judeia (26-36 d.C.), tinha sede em Cesareia, mas subia com frequência a Jerusalém. Os governadores romanos costumavam instalar o tribunal ao ar livre; João situa o tribunal de Pilatos no Pavimento, chamado Gábata em hebraico, um mosaico de pedras coloridas fora do pretório, explicado como o monte do templo pavimentado onde ficava a fortaleza Antônia.Fontes: Pontius Pilate · Pavement · Gabbatha · o próprio texto bíblico
- Os evangelistas interpretam Gólgota como “o lugar da caveira”: o nome transcreve o aramaico Gulgaltha, o hebraico gulgoleth, “caveira”, e designa o mesmo lugar chamado Calvário, descrito como um pequeno outeiro arredondado como um crânio descoberto, fora da porta e perto da cidade. Por estar tão perto, muitos judeus puderam ler o letreiro de Pilatos, escrito em hebraico, latim e grego, que nomeava Jesus de Nazaré — a cidade onde José e Maria tinham morado — como Rei dos Judeus.Fontes: Golgotha · Nazareth · o próprio texto bíblico
- José de Arimateia, membro rico do Sinédrio e natural de Arimateia — provavelmente a Ramá do Antigo Testamento, embora outros a identifiquem com Ramleh ou com Ramá de Benjamim —, pediu o corpo a Pilatos, que consentiu depois que o centurião confirmou a morte de Jesus. Nicodemos, fariseu desse conselho que já visitara Jesus de noite, trouxe cerca de setenta e cinco libras de mirra e aloés; envolveram o corpo em linho com as especiarias, ao modo judaico, e o puseram num túmulo novo num jardim próximo, pois era o dia da Preparação e o dia seguinte era um grande sábado.Fontes: Joseph (of Arimathea) · Nicodemus · Arimathea · o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org