João 17
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Da Yesu ya fadi wandannan abubuwa, sai ya tada idanunsa sama ya ce, ya Uba, sa'a ta zo; ka daukaka Danka, domin Dan shi ya daukaka ka, 2kamar yadda ka ba shi iko akan dukkan 'yan adam, ya ba da rai madawwami ga duk wanda ka ba shi. 3Wannan ne rai madawwami: wato su san ka, Allah makadaici na gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Almasihu. 4Na daukaka ka a duniya, na gama aikin da ka ba ni in yi. 5Yanzu, ya Uba, ka daukaka ni tare da kai da daukaka wadda ni ke da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasanci. 6Na bayyana sunanka ga mutunen da ka ba ni acikin duniya. Na ka suke, ka ba ni su, sun kuwa kiyaye maganarka. 7Yanzu kuwa sun san duk iyakar abinda ka ba ni daga gare ka yake, 8don kuwa maganganun da ka fada mani. Na fada masu, sun kuma karba, sun sani kuwa hakika na fito daga gareka ne, kuma sun gaskata kai ne ka aiko ni. 9Ina yi masu addu'a. Ba domin duniya ni ke yin addu'a ba, amma domin wadanda ka bani gama na ka ne. 10Gama dukan abinda ke nawa na ka ne, naka kuwa nawa ne, an kuma daukaka ni a cikinsu. 11Ba na cikin duniya kuma, amma wadannan mutane suna cikin duniya, ni kuwa ina zuwa wurin ka. Ya Uba mai Tsarki, ka adanasu cikin sunanka da ka ba ni domin su zama daya, kamar dai yadda muke daya. 12Lokacin da ina tare da su, na adanasu acikin sunanka da ka ba ni. Na kiyaye su, kuma ko daya kuwa daga cikinsu ba ya bace ba, sai dai dan hallakar nan, domin Nassi ya cika. 13Amma yanzu ina zuwa wurinka, Ina fadar wadannan abubuwa tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu. 14Na ba su maganarka, kuma duniya ta tsane su domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne. 15Ba ina roko ka dauke su daga cikin duniya ba, amma domin ka tsare su daga mugun nan. 16Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne. 17Ka kebe su domin kanka cikin gaskiya. maganarka gaskiya ce. 18Kamar dai yadda ka aiko ni cikin duniya, haka kuma na aike su cikin duniya. 19Na kebe kaina gareka sabili da su, domin su ma kansu a kebe su gareka cikin gaskiya. 20Ina addu'a ba domin wadannan kadai ba, amma har da wadanda zasu gaskata da ni ta wurin maganarsu, 21Domin su zama daya dukansu, kamar yadda kai, ya Uba, ka ke ciki na, ni kuma na ke cikin ka. Ina roko suma su kasance a cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa ka aiko ni 22Daukakar da ka bani, ita nake basu, domin su zama daya, kamar yadda mu ke daya; 23ni a cikinsu, kai kuma a ciki na. Domin su kammalu cikin zama daya, domin duniya ta sani cewa ka aiko ni, kuma ka kaunace su, kamar yadda ka kaunace ni. 24Ya Uba, ina so wadanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, domin su dubi daukakata da ka yi mani. Domin ka kaunace ni tun kafin halittar duniya. 25Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta sanka ba, amma ni na sanka; kuma wadannan sun sani kai ne ka aiko ni. 26Na sanar masu da sunanka, zan kuma sanar da shi domin kaunar da ka yi mani ta kasance a cikinsu, ni kuma in kasance a cikinsu,

Você sabia?
João 17: a hora chegou
- A oração começa quando Jesus, depois de ter dito essas coisas, ergue os olhos ao céu e diz que a hora chegou. Ela está associada ao Discurso do Cenáculo, indicado como um dia, e à Semana Santa, indicada como oito dias.Fontes: o próprio texto bíblico · Upper Room Discourse · Holy Week
- Aqui a vida eterna é conhecer o único Deus verdadeiro e Jesus Cristo, a quem o Pai enviou. Jesus também fala da glória que tinha com o Pai antes de o mundo existir e do amor do Pai por ele antes da fundação do mundo.Fontes: o próprio texto bíblico
- Ele ora por aqueles que o Pai lhe deu do mundo, os que guardaram a palavra, e também por quem crerá por meio da mensagem deles, pedindo que sejam um. Não pede que sejam tirados do mundo, mas que sejam guardados do maligno e santificados pela verdade, que ele identifica como a palavra do Pai.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org