Nations Bible

João 12

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Kwana shidda kafin idin ketarewa, Yesu ya zo Baitanya inda Li'azaru yake, wato wannan da Yesu ya tada daga matattu. 2Sai suka shirya masa abinci a wurin kuma Matta ce ke hidima, Li'azaru kuwa ya kasance cikin wadanda ke kan tebiri tare da Yesu. 3Sai Maryamu ta dauki wani turare da aka yi da man nard, ta shafe kafafun Yesu da shi, ta kuma share kafafun nasa da gashin kanta. Sai gida ya cika da kamshin turaren. 4Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin almajiransa, wanda zai bashe shi, ya ce, “ 5“Me yasa ba a sayar da wannan turare dinari dari uku a ba gajiyayyu ba?” 6Ya fadi haka ba don ya damu da gajiyayyu ba, amma domin shi barawo ne: shi ne ma'aji, kuma yana sata daga jakkar kudi. 7Yesu ya ce, “Ku kyale ta ta ajiye abinda ta tanada domin jana'iza ta. 8Gajiyayyu suna tare da ku a koyaushe, ni kuwa ba zan kasance da ku koyaushe ba. 9To babban taron Yahudawa sun ji cewa Yesu yana wurin, sai suka zo, ba don Yesu kawai ba amma domin su ga Li'azaru, wanda Yesu ya tada daga matattu. 10Sai manyan firistoci suka kulla makirci akan yadda za su kashe Li'azaru shima; 11domin saboda shi ne yahudawa dayawa suka je suka bada gaskiya ga Yesu. 12Kashegari, babban taro suka zo idin. Da suka ji cewa Yesu na zuwa Urushalima, 13Sai suka dauki ganyen dabino suka fita gari suka tare shi da kira mai karfi suna cewa, “Hosanna! Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji, Sarkin Isra'ila. 14Yesu ya sami wani Aholakin jaki, ya hau kansa; kamar yadda aka rubuta, 15“Kada ki ji tsoro ke 'yar Sihiyona; duba, ga Sarkinki na zuwa, zaune a kan danJaki”. 16Almajiransa basu fahimci wannan al'amari ba da farko, amma bayan da aka daukaka Yesu, sai suka tuna cewa an rubuta wadannan abubuwa game da shi, kuma sun yi masa wadannan abubuwa. 17Sai taron da ke tare da Yesu a ranar da ya kira Li'azaru daga kabari ya kuma tashe shi daga matattu, suka bada shaida. 18Domin wannan ne kuma taron suka zo domin su sadu da shi saboda sun ji cewa ya yi wannan alama. 19Don haka, sai farisawa suka shiga magana a tsakanin su suna cewa “Duba, babu abinda zaku iya yi; kun ga, duniya ta gama bin sa. 20Akwai wadansu Helinawa cikin wadanda suka je sujada a idin. 21Wadannan suka tafi wurin filibus, mutumin Betsaida da ke Galili, suka ce masa, “Mallam, muna so mu ga Yesu. 22Filibus ya tafi ya fadawa Andrawus; sai Andrawus ya tafi tare da Filibus, suka kuwa gaya wa Yesu. 23Yesu ya amsa masu ya ce, “sa'a ta zo da za'a daukaka Dan mutum. 24Hakika, hakika, Ina ce maku, in ba kwayar alkama ta fadi kasa ba ta mutu, za ta kasance ita kadai; amma idan ta mutu, za ta bada 'ya'ya masu yawa. 25Duk wanda yake son ransa, zai rasa shi; amma wanda ba ya son ransa a duniyan nan za ya kiyaye shi domin rayuwa ta har abada. 26Idan wani na bauta mani, to bari ya biyo ni; kuma duk inda nike, a can bawana zai kasance kuma. Duk wanda ke bauta mani, Uban zai girmama shi. 27Yanzu raina na cikin damuwa, to me zan ce? 'Uba, ka cece ni daga wannan sa'a? Amma Saboda wannan dalili ne na zo wannan sa'a. 28Uba, ka daukaka sunanka”. Sai wata murya daga sama ta ce, “Na daukaka shi, zan kuma sake daukaka shi. 29Daganan sai taron dake tsaye kuma suka ji muryar, suka ce an yi tsawa. Wasu suka ce, “Mala'ika ya yi magana da shi”. 30Yesu ya amsa ya ce, “wannnan murya ta zo ba saboda ni ba, amma domin ku.” 31Yanzu za'a shar'anta duniya. Yanzu za'a kori mai mulkin duniyan nan. 32Sa, annan ni, idan an daga ni daga duniya, zan jawo dukan mutane zuwa gare ni”. 33Ya fadi wannan ne domin ya nuna irin mutuwar da za ya yi. 34Taro suka amsa masa cewa, “Mun ji a cikin shari'a cewa Almasihu za ya kasance har abada. Yaya za ka ce, 'za'a daga dan mutum'? Wanene wannan dan mutum?” 35Yesu ya ce masu, “Nan da lokaci kadan za ku kasance da haske, ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya mamaye ku. Wanda ke tafiya cikin duhu, bai san inda za shi ba. 36Ku gaskata ga haske tun yana tare da ku domin ku zama yayan haske”. Yesu ya fadi wadannan abubuwa sannan ya tafi ya boye masu. 37Kodashike Yesu ya yi alamu da dama a gabansu, duk da haka ba su gaskata shi ba. 38Saboda maganar annabi Ishaya ta cika, wadda ya ce, “ Ubangiji, wa ya gaskata rahoton mu? Ga wa kuma hannun Ubangiji ya bayyana? 39Saboda wannan dalili basu gaskata ba, gama Ishaya ya sake cewa, 40ya makantar da su, ya kuma taurare zuciyarsu, saboda kada su gani da idanunsu, su kuma sami fahimta da zuciyarsu, su juyo wurina in warkar da su. 41Ishaya ya fadi wadannan abubuwa ne domin ya hangi daukakar Yesu ya kuma yi magana game da shi. 42Amma duk da haka, dayawa cikin shugabanni suka gaskata Yesu. Amma saboda farisawa, basu shaida shi a sarari ba, domin kada a kore su daga majami'a. 43Suna son yabo daga mutane fiye da yabon dake zuwa daga Allah. 44Yesu ya yi magana da babbar murya, ya ce, “Wanda ya gaskata ni, ba ni yake gaskatawa kadai ba, amma kuma yana gaskata wanda ya aiko ni, 45kuma wanda ke gani na, yana ganin shi wanda ya aiko ni. 46Na zo ne a matsayin haske a duniya, saboda duk wanda ya gaskata da ni ba za ya yi tafiya cikin duhu ba. 47Duk wanda ya ji maganata baya gaskata ba, ba ni hukunta shi; gama ban zo in yi wa duniya hukunci ba, amma don in ceci duniya. 48Wanda ya ki ni, ya kuma ki ya karbi magana ta, akwai wanda za ya yi masa hukunci. Kalmar da na fada, ita ce za ta yi masa hukunci a rana ta karshe. 49Maganar da ni ke yi, ba ra'ayina ba ne. Amma Uba wanda ya aiko ni shi ke bani umarni game da abin da zan ce da abin da zan fadi. 50Na san umarninsa rai ne madawwami, don haka na ce - kamar yadda Uba ya fada, haka ni ma nake fadi.”

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

A unção em Betânia e a entrada em Jerusalém

  • Betânia, onde Jesus chegou seis dias antes da Páscoa, ficava a cerca de duas milhas a leste de Jerusalém, na encosta sudeste do monte das Oliveiras, à beira da estrada para Jericó, e recebeu o nome das palmeiras que cresciam ali. Era o lar de Lázaro, a quem Jesus havia ressuscitado dos mortos depois de quatro dias no túmulo, e de suas irmãs Marta e Maria; os principais sacerdotes planejaram matar Lázaro também, porque por causa dele muita gente estava crendo em Jesus.Fontes: o próprio texto bíblico · Bethany · Lazarus
  • Num jantar em que Marta servia e Lázaro se reclinava à mesa, Maria ungiu os pés de Jesus com cerca de uma pinta de perfume caro feito de nardo puro e os enxugou com os cabelos, de modo que a casa ficou cheia da fragrância. Judas Iscariotes, filho de Simão, cujo sobrenome significa um homem de Kerioth, perguntou por que o perfume não foi vendido por trezentos denários para os pobres; ele era ladrão e, como responsável pela bolsa, costumava tirar do que era colocado nela, e ia trair Jesus.Fontes: o próprio texto bíblico · Judas Iscariot · Simon
  • No dia seguinte, a grande multidão que viera para a festa tomou ramos de palmeira e saiu ao encontro de Jesus, que vinha para Jerusalém sentado num jumentinho, gritando louvor ao Rei de Israel, como está escrito a respeito da Filha de Sião. Sião era o monte sudeste de Jerusalém, onde Davi construiu uma cidadela e um palácio depois de tomá-lo, de modo que se tornou a cidade de Davi. A princípio seus discípulos não entenderam essas coisas, mas, depois que Jesus foi glorificado, lembraram-se de que elas também tinham sido escritas a respeito dele.Fontes: o próprio texto bíblico · Zion

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 11, 12, 20
  • Zion · Hoje: Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 15
  • Galilee · 32.760, 35.527 · versículo 21

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.