Hebreus 3
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Don haka yanuwana tsarkaka, a bokan kira a samaniya. Yi la'akari da Yesu. wato Manzo da babban firist na shaidar bangaskiyarmu. 2Shi amintacce ne na Allah, wanda ya bashi hidima, kamar yadda Musa ya kasance amintacce a gidan Allah. 3Gama Yesu ya cancanci daukaka mafi girma fiye da ta Musa. Domin wanda ya gina gida, ya fi gidan nan daukaka. 4Gama kowane gida, akwai wanda ya gina shi, amma mai ginin komai shine Allah. 5Musa hakika amintaccen bawa ne a gidan Allah, yana ba da shaidar abubuwan da za su faru a nan gaba. 6Amma Almasihu shi Da ne mai mulki a gidan Allah. Mu ne gidansa idan mun rike begenmu da dukkan zuciyarmu. 7Saboda haka, kamar yadda Ruhu Mai Tsarki ya fadi: ''Yau, Idan kun ji muryarsa, 8kada ku taurare zuciyarku kamar yadda 'ya'yan isra'ila suka yi cikin tawaye a lokacin gwaji a jeji. 9A lokacin nan ne kakanninku suka yi mani tawaye, ta wurin gwada ni, bayan shekara arba'in suna ganin ayyukana. 10Saboda haka na yi bakin ciki da wannan tsarar, sai na ce,' Kullum suna yawan bijirewa a zukatansu. Basu san tafarkuna ba.' 11Don haka na yi rantsuwa a cikin fushina, ba za su shiga cikin hutuna ba.” 12Ku yi hankali 'yan'uwa kada a tarar da mummunar zuciya marar bangaskiya a tsakaninku, zuciya wadda ke juyawa daga Allah mai rai. 13Maimakon haka, ku karfafa juna a kowacce rana, muddun muna cikin wannan rana kada wani cikinku ya taurare zuciyarsa saboda yaudarar zunubi. 14Gama mun zama abokan aiki da Almasihu, idan mun rike begenmu cikinsa da karfi, daga farko zuwa karshe. 15Game da wannan, an fadi “Yau idan kun saurari muryarsa, kada ku taurare zuciyarku, kamar a kwanakin tawaye nan.” 16Su wanene suka ji muryar Allah suka yi tawaye? Ba wadanda Musa ya yi masu jagora daga Masar ba ne? 17Kuma da su wa Allah ya yi fushi shekara arba'in? Ba da wadanda suka yi zunubi ba ne, wadanda gawawwakinsu suka warwatsu a jeji? 18Da su wa Allah ya rantse ba za su shiga hutunsa ba? In ba wadanda suka yi masa rashin biyayya ba? 19Mun kuma gani cewa basu iya shiga hutunsa ba saboda rashin bangaskiyarsu.

Você sabia?
Glória maior do que a de Moisés
- Hebreus pede aos leitores que fixem a atenção em Jesus, o apóstolo e sumo sacerdote que confessam. Ele foi fiel àquele que o designou, assim como Moisés foi fiel em toda a casa de Deus, mas Jesus é considerado digno de maior glória do que Moisés, como o construtor de uma casa tem mais honra do que a própria casa. Moisés foi fiel como servo; Cristo é fiel como Filho sobre a casa de Deus.Fontes: o próprio texto bíblico
- A advertência volta-se ao povo que Moisés tirou do Egito. Durante quarenta anos no deserto, eles puseram Deus à prova; Deus se irou contra aquela geração e jurou que jamais entrariam no seu descanso, e os corpos deles caíram no deserto. O capítulo diz que a incredulidade os impediu de entrar.Fontes: o próprio texto bíblico
- O Egito, a terra que deixaram com Moisés, é a terra do Nilo e das pirâmides. O dicionário bíblico de Easton (1897) explica o nome Moisés como tirado, ou o liga à palavra egípcia mesu, que significa filho.Fontes: o próprio texto bíblico · Egypt · Moses
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Egypt · 30.129, 31.308 · versículo 16
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org