Hebreus 12
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Da shike muna kewaye da wannan irin kasaitaccen taro na shaidu, sai mu watsar da dukkan abubuwan dake nawaita mana da kuma zunubin da zai saurin makale ma na. Bari a cikin hakuri mu yi tseren da ke gabanmu. 2Bari mu kafa idonmu ga Yesu, wanda shine mafarin bangaskiyarmu da cikarta. Wanda sabili da murnar da a ka sa a gabansa ya jimre giciye, ya kuma yi watsi da kunyarsa, wanda kuma ya zauna a hannun dama na kursiyin Allah. 3Ku dube shi wanda ya jimre irin wannan adawa daga masu zunubi, domin kada ku gaji ko ku karai. 4Ba ku yi tsayayya ko jayayya da zunubi har ta kai ga zub da jininku ba tukunna. Kun kuma manta da gargadin da a ka yi maku a matsayin 'ya'ya: 5''Dana, kada ka dauki horon Ubangiji da wasa, kadda kuma ka yi suwu lokacin da ka sami horonsa,'' 6Domin kuwa Ubangiji yana horon dukkan wadanda yake kauna, yana kuma hukunta duk wadanda ya karba. 7Ku daure wahala a matsayin horo. Allah yana yi da ku kamar 'ya'yansa, domin kuwa wanne da ne wanda ubansa bazai yi masa horo ba? 8Amma idan baku da horo kamar yadda sauran mutane ke da shi, kun zama shegu kenan ba 'ya'ya ba. 9Hakannan kuma kamar yadda muke da iyaye a duniya wadanda suke yi mana horo, kuma muna basu daraja. To ba sai mu yiwa Ubanmu na Ruhaniya biyayya don mu rayu ba? 10Ta wani fanni kuwa iyayenmu suna yi mana horo na kwanaki kadan bisa ga yadda suka ga ya dace, Amma Allah kuwa yana yi mana horo domin anfanin kanmu, domin kuma mu sami rabo daga cikin tsarkinsa. 11Ba horon da ke da dadi a lokacin yinsa, amma sai zafi. Sai dai kuma bayan haka yakan haifar da 'ya'ya na ruhaniya da kuma adalci ga dukkan wadanda aka yi rainonsu a ciki. 12Don haka sai ku karfafa hannayenku da ke reto, da kuma guwawunku da ke kaduwa. 13Ku bi hanyoyi mikakku domin abin da ya gurgunce kada ya karye amma ya warke. 14Ku bidi salama da kowa, da kuma rayuwar tsarki wanda in ba tare da shi, babu wanda zai ga Allah. 15Ku mai da hankali domin kada waninku ya rasa, alherin Allah, kuma kada wani tushe mai daci ya tsiro a cikinku har ya haifar da fitina, domin kada da dama daga cikinku su gurbata ta wurinsa. 16Ku yi hankali kuma kada a sami mazinanci ko marar ibada a cikinku, kamar Isuwa, wanda sabili da abinci ya sayar da 'yancinsa na dan fari. 17Kun kuwa san cewa sa'adda ya yi marmarin ya gaji albarka a gaba, an kishi, domin kuwa bai sami damar tuba ba, ko da shike ya nema har da hawaye. 18Domin kuwa baku zo ga dusen da ake tabawa da hannu ba, dutse ne mai ci da wuta, da tukuki da bakin hayaki da hadari. 19Ba Ku zo ga karar kaho mai ban razana da murya mai firgitarwa ba, da masu sauraro suka yi roko kar su sake jinta. 20Don basu iya jimre abin da aka yi doka a kan saba: ''koma dabba ce ta taba dutsen, sai a jejjefe ta.'' 21Abin tsoro ne kuwa kwarai, har Musa yace, ''A tsoroce nake kwarai har na firgita.'' 22Maimakon haka kun zone ga Dutsen Sihiyona da kuma birni na Allah mai Rai, kuma na Urushalima ta Samniya, da kuma dubun dubban mala'iku cikin murna da farin ciki. 23Kun zo taro na dukkan 'ya'yan fari, rubuttatu a sama, kuma kun zo ga Allah wanda shine alkalin dukka, hakannan kuma zuwa ga ruhu na adalai wanda a ka rigaya aka tsarkake. 24Kun zo ga Yesu, wanda shine matsakancin sabon alkawari, kuma ga jinin yayyafawa da ke magana fiye da na jinin Habila. 25Ku yi lura kada ku ki wannan da ke yi mu ku magana. Gama in har basu kubuta yayin da su ka yi jayayya da wanda ya yi mu su gargadi a duniya ba, balle ma mu ba za mu kubuta ba in mun ki wanda ke mana gargadi daga sama. 26A wani karo, muryar sa ta girgiza duniya. Amma yanzu yayi alkawari da cewa, ''Har'ila yau ba duniyar kadai zan girgiza ba, amma har da sammai.'' 27Wannan kalma, ''Harl'ila yau,'' ta bayyana cirewar abubuwan nan da za su girgizu, wato abubuwan da a ka halitta, domin abubuwan da ba zasu girgizu ba su kasance. 28Don haka, samun mulkin da ba za ya girgizu ba, sai mu zama masu godiya, kuma a cikin wannan yanayi mu yi wa Allah sujada cikin daraja da tsaninin gimamawa. 29Domin kuwa Allahnmu wuta ne mai konewa.

Você sabia?
A corrida, a disciplina e o monte Sião
- Hebreus 12 adverte contra ser profano como Esaú, que vendeu a primogenitura por uma única refeição. Esaú, o gêmeo primogênito de Rebeca, era caçador; faminto ao voltar da caça, vendeu esse direito ao irmão Jacó por um cozido de lentilhas vermelhas, e daí também lhe veio o nome Edom, “vermelho”. Depois, diz o capítulo, ele buscou a bênção com lágrimas e foi rejeitado.Fontes: Esau (Edom) · o próprio texto bíblico
- Hebreus 12 diz que seus leitores chegaram não a um monte que se pode tocar e que arde em fogo, em trevas, escuridão e tempestade — onde até Moisés disse: “Estou tremendo de medo” —, mas ao monte Sião e à Jerusalém celestial, a cidade do Deus vivo. O monte Sião era a colina do sudeste de Jerusalém; Davi a tomou dos jebuseus, construiu ali uma cidadela e um palácio, e ela se tornou a cidade de Davi. O nome Jerusalém é explicado como “posse da paz” ou “fundamento da paz”, e a cidade também era chamada de cidade santa.Fontes: o próprio texto bíblico · Mount Zion · Jerusalem
- Hebreus 12 fala do “sangue aspergido, que fala uma palavra melhor do que o sangue de Abel”. Abel, o segundo filho de Adão e Eva, foi morto pelo irmão Caim, depois que o Senhor olhou com favor para Abel e para sua oferta, os primogênitos do rebanho, mas não para Caim e sua oferta, os frutos do campo.Fontes: o próprio texto bíblico · Abel
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org