Nations Bible

Atos 21

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Da muka rabu da su, muka shiga jirgin ruwa muka mike hanya zuwa birnin Kos, washegari sai birnin Rodusa, daga nan sai kuma zuwa birnin Batara. 2Da muka sami jirgi mai hayewa zuwa Fonisiya sai muka shiga. 3Da muka hango tsibirin Kubrus muka bar shi a hagun mu muka nufi Suriya, muka sauka a birnin Taya domin a nan ne jirgin ruwan zai sauke kayansa. 4Bayan mun sami almajirai sai muka zauna can kwana bakwai. Al'majiran suka ce ma Bulus, ta wurin Ruhu, kada ma ya je Urushalima. 5Bayan 'yan kwanaki muka cigaba da tafiyarmu. Dukansu da matansu da 'ya'yansu suka raka mu har bayan birnin. Sa'annan muka durkusa a bakin gacci muka yi addu'a muka yi sallama da juna. 6Sai muka shiga jirgin ruwa, su kuma suka koma gida. 7Da muka gama tafiyarmu a Taya muka iso Talamayas. A nan ne muka gaisa da 'yan'uwa, muka zamna kwana daya da su. 8Washegari muka tashi muka tafi Kaisariya. Muka shiga gidan Filibus mai shaida bishara, daya daga cikin bakwai din, muka zauna da shi. 9Wannan mutum yana da 'ya'ya hudu mata, budurwai masu yin annabci. 10Sa'anda muka zauna can 'yan kwanaki, wani annabi ya zo daga Yahudiya mai suna Agabus. 11Ya zo wurinmu ya dauki damarar Bulus ya daure tasa kafar da hannayensa ya ce, “Ruhu Mai Tsarki ya ce, 'Haka Yahudawa za su daure mai wannan damarar, zasu kuma bashe shi ga al'ummai.'” 12Da muka ji wannan sakon, sai dukanmu da mazaunan wurin muka roki Bulus kada ya tafi Urushalima. 13Sai Bulus ya amsa ya ce, “Me kuke yi, kuna kuka kuna karya mani zuciya? Bama a shirye don dauri kadai nake ba har ma da mutuwa a Urushalima, sabili da sunan Ubangiji Yesu.” 14Tun da Bulus bashi da niyyar a rinjaye shi, muka daina kuka muka ce, “Bari nufin Ubangiji ya tabbata.” 15Bayan wadannan kwanaki, muka dauki jakkunanmu muka haura Urushalima. 16Wadansu almjirai daga Kaisariya suka bi mu. Sun zo ne tare da wani ana ce da shi Manason, mutumin Kuburus mai bi na farko, wanda za mu zauna da shi. 17Da muka isa Urushalima, 'yan'uwa suka marabce mu da farin ciki. 18Washegari Bulus ya tafi tare da mu zuwa wurin Bitrus, dukan dattawa kuma suna nan. 19Bayan ya gaishe su, sai ya shaida masu daya bayan daya abubuwan da Allah ya yi cikin al'ummai ta wurin hidimarsa. 20Da suka ji haka, suka yabi Ubangiji suka ce masa, “Ka gani, dan'uwa, dubban Yahudawa sun bada gaskiya suna kuma da niyyar kiyaye shari'a. 21An kuma gaya masu a kanka cewa, kana koya wa Yahudawan da suke zaune cikin al'ummai su yi watsi da Musa. Kana koya masu kada su yi wa 'ya'yansu kaciya, kada kuma su bi tsofaffin al'adu. 22Me ya kamata mu yi? Hakika za su ji ka zo. 23Sabo da haka ka yi abin da muka fada maka yanzu. Muna da maza hudu da suka dauki wa'adi. 24Tafi da wadannan ka tsarkake kanka tare da su, ka dauki dukan dawainiyar su dana askin kai. Ta haka kowanne mutum zai sani abubuwan da ake fadi a kanka karya ne. Za su sani cewa kai mai kiyaye shari'a ne. 25Game da al'umman da suka bada gaskiya mun yi masu wasika, mun bada umarni su kaurace kansu daga sadakokin da aka mika wa gumaku, da jini, da abin da aka makare da kuma fasikanci. 26Sai Bulus ya dauki mazannan, washegari ya tsarkake kansa tare da su, suka shiga haikali, domin ya sanar da cikar ranakun tsarkakewarsu, wato ranar ba da sadaka domin kowanne dayansu. 27Da kwanakin nan bakwai suka yi gab da cika, wadansu Yahudawa daga Asiya suka ga Bulus a haikali, sai suka zuga taro, suka danke shi. 28Suna ta kururuwa, “Mutanen Isra'ila ku taimaka mana. Wannan shine mutumin da ke koya wa dukan mutane ko'ina abubuwa gaba da mutane, da shari'a da kuma wannan wurin. Banda haka ya kawo Helenawa cikin haikalin nan ya kazantar da wannan wuri tsatsarka.” 29Domin dama sun ga Tarofimas mutumin Afisa tare da Bulus cikin birni, suka yi zaton ya kawo shi cikin haikali. 30Sai duk gari ya rude, mutane suka runtuma suka danke Bulus. Suka ja shi waje daga cikin haikalin, nan da nan aka rufe kofofin. 31Suna kokarin kashe shi kenan, sai labari ya kai wurin hafsan sojoji cewa Urushalima duk ta yamutse da tarzoma. 32Nan take ya dauki mayaka da jarumawa, suka sheka da gudu wurin taron. Da mutane suka ga hafsan sojoji da rundunansa sai suka daina dukan Bulus. 33Sai hafsan ya tafi ya danke Bulus ya sa aka daure shi da sarkoki biyu. Ya tambaya ko shi wanene da kuma laifinsa. 34Wadansu cikin taron suna ta kururuwa wadansu su ce wannan, wadansu su ce, wancan. Tunda hafsan bai fahimci abin da suke fadi ba, sabo da ihunsu, ya dokaci a shigar da Bulus farfajiyar sojoji. 35Da suka kai matakala, sojoji suka dauki Bulus sabo da tsananin husatar taron jama'a. 36Domin taron suka biyo baya suna ihu suna cewa, “A kashe shi.” 37An kusa shigar da shi farfajiyan kenan sai Bulus ya ce wa babban hafsan, “Ko ka yarda inyi magana da kai?” Hafsan ya ce, “Ka iya Helenanci? 38Ashe ba kai ne Bamasaren nan da kwanakin baya ka haddasa tawaye, ka dauki 'yan ta'adda dubu hudu ka kai su jeji ba?” 39Bulus ya ce, “Ni Ba'ibrane ne daga birnin Tarsus a Kilikiya. Ni dan kasar babban birni ne. Ka amince mani in yi magana da mutanen.” 40Da hafsan ya bashi izni, Bulus ya mike a kan matakala ya daga hannayensa sama ya yi nuni su yi shuru. Da wuri ya yi tsit, Bulus ya yi masu magana da Ibraniyanci. Ya ce,

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

A viagem de Paulo a Jerusalém e sua prisão no templo

  • Em Cesaréia, o profeta Ágabo transmitiu um aviso simbólico vívido ao pegar o cinto de Paulo e amarrar as próprias mãos e pés. Ele predisse que os judeus em Jerusalém amarrariam Paulo e o entregariam nas mãos dos gentios.Fontes: Agabus · o próprio texto bíblico
  • Durante sua viagem, Paulo hospedou-se em Cesaréia na casa de Filipe, o evangelista, um dos Sete escolhidos para servir à igreja primitiva em Jerusalém. Filipe tinha quatro filhas solteiras que tinham o dom de profecia.Fontes: Phillip the Evangelist · o próprio texto bíblico
  • O violento tumulto que resultou na prisão de Paulo pelos romanos começou quando judeus da província da Ásia presumiram que Paulo havia introduzido Trófimo, um cristão gentio de Éfeso, no pátio sagrado do templo.Fontes: Trophimus · o próprio texto bíblico

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Lugares deste capítulo

  • Cos · Hoje: Kos · 36.815, 27.110 · versículo 1
  • Patara · 36.260, 29.314 · versículo 1
  • Phoenicia · 33.271, 35.196 · versículo 2
  • Cyprus · 35.000, 33.000 · versículos 3, 16
  • Syria · Hoje: Syria 2 · 33.511, 36.306 · versículo 3
  • Tyre · 33.271, 35.196 · versículos 3, 7
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículos 4, 11, 12, 13, 15, 17, 18, 21, 31
  • Ptolemais · Hoje: Acre · 32.921, 35.069 · versículo 7
  • Caesarea · Hoje: Caesarea Maritima · 32.500, 34.892 · versículos 8, 16
  • Judea · Hoje: Judea 1 · 31.777, 35.234 · versículo 10
  • Asia · 38.400, 28.300 · versículo 27
  • Ephesus · 37.939, 27.341 · versículo 29
  • Cilicia · 36.913, 34.892 · versículo 39
  • Tarsus · 36.913, 34.892 · versículo 39

Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.