Atos 16
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Bulus ya kuma isa Darbe da Listira, in da akwai wani almajiri mai suna Timoti a wurin, dan wata Bayahudiya wadda ta ba da gaskiya; ubansa kuwa Baheline ne. 2Ana maganar kirki a kansa ta bakin 'yan'uwa da ke Listira da Ikoniyan. 3Bulus ya yi wa Timoti kaciya, domin yana so su yi tafiya tare, domin kuma saboda Yahudawan da ke wurin, sun san cewa ubansa Baheline ne. 4Suna shiga cikin biranen, suna yi wa iklisiyoyi gargadi da su yi biyayya da umurnan da Manzanni da dattawa suka rubuta a Urushalima. 5Bangaskiyar iklisiyoyi kuwa ta karu, ana kuma samun karuwa na wadanda suke ba da gaskiya kowace rana. 6Bulus da abokan aikin sa sun shiga cikin lardin Firigiya da Galatiya, tun da Ruhu Mai Tsarki ya hana su wa'azin kalmar a cikin yankin Asiya. 7Sun zo kusa da Misiya, da nufin shiga cikin Bitiniya, Ruhun Yesu ya hana su. 8Da suka ratse ta cikin Misiya, sai suka shiga birnin Taruwasa. 9Bulus ya ga wahayi cikin dare, wani mutumin Makidoniya na kiransa, yana cewa. ''Ka zo Makidoniya ka taimake mu''. 10Bulus, da ganin haka, ya kama hanya zuwa Makidoniya, da tunanin Allah ne ya ke so su kai wa mutanen Makidoniya bishara. 11Da barin Taruwasa, Bulus da kungiyarsa sun shiga jirgin ruwa zuwa Samutaraki, da gari ya waye kuma sun tafi Niyafolis; 12Daga nan kuma suka tafi Filibi, birni na Makidoniya, mai muhimmanci ne a yankin Roma, in da mun yi zango kwanaki da dama. 13Ranar Asabaci mun je kofar gari, gefen rafi, da tunanin samun wurin addu'a. Mun zauna mun kuma yi magana da matan da sun taru a wurin. 14Wata mace mai suna Lidiya, 'yar kasuwa ce a birnin Tiyatira, mai bautar Allah ce, ta saurare mu. Ubangiji ya bude zuciyarta, ta mai da hankali ga maganar da Bulus ke fadi. 15Sa'anda da aka yi mata Baftisma tare da mutanen gidanta, ta ce da mu, “Idan kun dauke ni mai bautar Allah, ku zo gidana ku zauna.” Sai ta rinjaye mu. 16A daidai wannan lokaci, muna tafiya wurin addu'a, wata yarinya mai ruhun duba ta hadu da mu. Iyayen gijinta na arziki da ita sosai. 17Tana bin Bulus, tare da mu, tana fadi da murya mai karfi cewa, ''Wadannan mutanen, bayin Allah mafi daukaka ne, suna sanar maku hanyar ceto ne''. 18Ta dauki kwanaki tana haka. Amma Bulus ya yi fushi da ita ainun, ya juya ya umarci ruhun, ya ce, ''Na umarce ka, ka rabu da ita a cikin sunan Yesu Almasihu''. Ruhun ya yi biyayya ya rabu da ita nan take. 19Da iyayengijinta suka ga cewa hanyar shigar kudinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila, suka ja su cikin kasuwa suka kai su gaban mahunkunta. 20Da suka kai su Kotu, suka ce, ''Wadannan mutane Yahudawa ne, suna kawo tashin hankali a birninmu. 21Suna koyar da abubuwa da ba su karbuwa a gare mu, balle mu aikata, a matsayinmu na Romawa.” 22Sai jama'a gaba daya sun tayar wa Bulus da Sila; alkalan kuma sun yage rigunansu, sun ba da umarni a duki Bulus da Sila da bulala. 23Bayan dukan, an jefa su Bulus a kurkuku, an ba mai tsaron kurkukun umurni ya kulle su da kyau, kada su gudu. 24Shi kuma ya yi hakanan, ya sa masu sarkoki a kafafun su, kamar yadda aka umurce shi. 25Da tsakar dare, Bulus da Sila suna yin adu'a, su na raira wakoki ga Allah, sauran 'yan sarkar su na jin su. 26Nan da nan sai ga wata girgizar kasa, wadda ta sa ginshikan kurkukun sun kadu, nan da nan kofofin kurkukun sun bude, 'yan sarka kuma, sarkokin su sun karkatse. 27Mai tsaron kurkukun ya tashi daga barci ya ga kofofin kurkukun a bude, ya zaro takobi, zai kashe kan sa, a tunanin sa, 'yan sarkar sun gudu. 28Amma Bulus ya ta da murya da karfi, ya ce, ''kada kayi wa kanka barna, domin dukan mu muna nan''. 29Mai tsaron kurkukun ya aika a kawo fitila, ya shiga ciki a gurguje da rawan jiki, ya fadi a gaban Bulus da Sila, 30ya fitar da su waje ya ce, ''Shugabanni, me ya kamata in yi domin in tsira?'' 31Sun ce masa, ''ka ba da gaskiya ga Yesu Ubangiji, da kai da gidan ka, za ku sami tsira''. 32Bulus da Sila suka fada masa maganar Ubangiji, tare da iyalinsa. 33Shi mai tsaron kurkukun ya dauke su cikin daren, ya wanke raunukansu, an kuma yi masa Baftisma nan da nan tare da iyalinsa. 34Ya kai Bulus da Sila gidansa, ya ba su abinci. Murna ta cika gidan mai tsaron kurkukun, domin iyalin sa duka sun ba da gaskiya ga Allah. 35Da gari ya waye, alkalai sun ba da sako a saki Bulus da Sila. 36Mai tsaron kurkukun kuwa ya sanar wa Bulus wannan magana ta alkalan, saboda haka ya ce wa Bulus, ''Ku tafi cikin salama''. 37Amma Bulus ya ce masu, “Sun yi mana duka a fili a gaban mutane mu da muke Romawa, ba a kashe mu ba, sun kuma sa mu a kurkuku; suna koran mu a asirce? Su zo da kansu su fitar da mu. 38Masu tsaron kurkuku sun mayar da maganar Bulus ga alkalan, wanda ya sa sun firgita, da jin cewa Bulus da Sila Romawa ne. 39Alkalai da kansu sun zo sun roki Bulus da Sila; da suka fitar da su daga kurkukun, sun ce wa Bulus da Sila su bar birnin. 40Da hakanan ne Bulus da Sila suka fita daga kurkuku, sun je gidan Lidiya. Da Bulus da Sila sun ga 'yan'uwa, sun karfafa su, sa'annan suka bar birnin.

Você sabia?
De Listra a Filipos
- Em Listra, Paulo encontrou Timóteo, um discípulo de quem os irmãos de Listra e Icônio falavam bem, filho de uma judia crente e de pai grego. Querendo-o como companheiro, Paulo o circuncidou por causa dos judeus dali, que sabiam que seu pai era grego. O dicionário bíblico de Easton (1897) diz que Timóteo provavelmente morava em Listra e parece ter se convertido na visita anterior de Paulo.Fontes: o próprio texto bíblico · Timotheus
- Depois de serem impedidos de falar na província da Ásia, Paulo e seus companheiros viajaram pela Frígia e pela Galácia. Na fronteira da Mísia não lhes foi permitido entrar na Bitínia, e então desceram a Trôade, o principal porto da Mísia, na costa noroeste da Ásia Menor, cidade que recebeu o nome da antiga Troia, cerca de quatro milhas ao norte. Ali, uma visão noturna de um homem da Macedônia que pedia ajuda os levou a navegar para essa província romana ao norte da Grécia.Fontes: o próprio texto bíblico · Mysia · Troas · Macedonia
- Na colônia romana de Filipos, Paulo e seus companheiros encontraram, junto ao rio e fora da porta da cidade, um lugar onde era costume orar, e ali mulheres estavam reunidas. Entre elas estava Lídia, comerciante de tecidos de púrpura, de Tiatira, e adoradora de Deus; depois que ela e os de sua casa foram batizados, ela convenceu os viajantes a ficarem em sua casa. O dicionário bíblico de Easton (1897) a descreve como uma prosélita de riqueza considerável e como a primeira pessoa na Europa a abraçar o cristianismo.Fontes: o próprio texto bíblico · Lydia
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Lystra · Hoje: Tel Lystra · 37.602, 32.338 · versículos 1, 2
- Iconium · Hoje: Konya · 37.872, 32.492 · versículo 2
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 4
- Asia · 38.400, 28.300 · versículo 6
- Galatia · 39.267, 32.983 · versículo 6
- Phrygia · 39.000, 31.000 · versículo 6
- Bithynia · 40.500, 31.000 · versículo 7
- Mysia · 40.000, 28.500 · versículos 7, 8
- Troas · Hoje: Alexandria Troas · 39.752, 26.159 · versículos 8, 11
- Greece · 37.972, 23.727 · versículo 9
- Macedonia · 41.600, 22.540 · versículos 9, 10, 12
- Neapolis · Hoje: Kavala · 40.935, 24.415 · versículo 11
- Samothrace · Hoje: Samothraki · 40.450, 25.583 · versículo 11
- Philippi · 41.012, 24.285 · versículo 12
- Thyatira · Hoje: Akhisar · 38.920, 27.837 · versículo 14
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org