2 Timóteo 2
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Domin wannan kai, dana, ka karfafa cikin alherin da ke cikin Almasihu Yesu. 2Abubuwan da ka ji daga gare ni a bainar jama'a masu yawa, ka danka su ga mutane masu aminci da za su iya koya wa wadansu kuma. 3Ka daure shan tsanani tare da ni, kamar amintaccen sojan Almasihu Yesu. 4Ba bu sojan da zai yi bauta yayin da ya nannade kansa da al'amuran wannan rayuwar, domin ya gamshi shugabansa. 5Hakanan, idan wani yana gasa a matsayin dan wasa, ba zai sami rawani ba tukuna har sai in ya karasa tseren bisa ga ka'idodin gasar. 6Wajibi ne manomi mai kwazon aiki ya fara karbar amfanin gonarsa. 7Ka yi tunani game da abin da na ke gaya maka, gama Ubangiji zai ba ka ganewa a cikin komai. 8Ka tuna da Yesu Almasihu, daga zuriyar Dauda, wanda a ka tayar daga matattu. Bisa ga wa'azin bisharata, 9wanda na ke shan wahala har ya kai ga dauri kamar mai laifi. Amma maganar Allah ba a daure ta ba. 10Saboda haka na jure wa dukkan abubuwa domin wadanda aka zaba, saboda su ma su sami ceton da ke cikin Almasihu Yesu, da daukaka madawwamiya. 11Wannan magana tabbatacciya ce: “Idan mun mutu tare da shi, za mu kuma rayu tare da shi. 12Idan mun jure, zamu kuma yi mulki tare da shi. Idan mun yi musun sa, shi ma zai yi musun mu. 13Idan mun zama marasa aminci, shi mai aminci ne koyaushe, domin shi ba zai yiwu ya musunta kansa ba.” 14Ka yi ta tuna masu da wadannan abubuwan. Ka yi masu kashedi a gaban Allah kada su yi ta dauki ba dadi game da kalmomi. Saboda wannan bai da wani amfani. Domin wannan zai halakar da ma su sauraro. 15Ka yi iyakacin kokarika domin ka mika kanka ma'aikacin Allah wanda aka tabbatar, wanda babu dalilin kunya a gareshi. Wanda ya ke koyar da kalmar gaskiya daidai. 16Ka guje wa masu maganar sabo, wanda ya kan kara kaiwa ga rashin bin Allah. 17Maganarsu za ta yadu kamar ciwon daji. Daga cikinsu akwai Himinayus da Filitus. 18Wadannan mutanen sun kauce wa gaskiya. Sun fadi cewa an rigaya an yi tashin matattu. Suka birkitar da bangaskiyar wadansu. 19Duk da haka, ginshikin Allah ya tabbata. Ya na da wannan hatimi: “Ubangiji ya san wadanda ke nasa,” Kuma “Duk mai kira bisa ga sunan Ubangiji dole ya rabu da rashin adalci.” 20A gida mai wadata, ba kayayyaki na zinariya da azurfa ba ne kawai. Haka kuma akwai kayayyaki na itace da yunbu. Wadansu domin aikin mai daraja, wadansu kuma ga aiki mara daraja. 21Idan wani ya tsarkake kansa daga rashin daraja, shi kayan aiki ne mai daraja. An kebe shi, abin aiki domin mai gidan, kuma a shirye domin kowanne aiki mai kyau. 22Ka guje wa sha'awoyi na kuruciya, ka nemi adalci, bangaskiya, kauna da salama da wadanda suke kira ga sunan Ubangiji daga zuciya mai tsabta. 23Amma ka ki tambayoyi na wauta da jahilci. Ka sani sukan haifar da gardandami. 24Tilas bawan Ubangiji ya guje wa jayayya. A maimakon haka dole ya zama mai tawali'u ga kowa, mai iya koyarwa, kuma mai hakuri. 25Dole ne ya koyarwa mutane da su ke jayayya da shi a cikin tawali'u. Watakila Allah ya ba su ikon tuba domin sanin gaskiyar. 26Suna iya sake dawowa cikin hankalinsu kuma su bar tarkon Ibilis, bayan da ya cafke su domin nufinsa.

Você sabia?
Um mestre fiel sob pressão
- Este capítulo adverte que a conversa de Himeneu e Fileto se espalha como gangrena: eles se desviaram da verdade ao dizer que a ressurreição já aconteceu e assim abalam a fé de alguns. O Easton's Bible Dictionary (1897) situa Fileto, com Himeneu, em Éfeso, e descreve essa afirmação, de que a ressurreição já havia ocorrido, como uma heresia gnóstica sustentada pelos nicolaítas.Fontes: o próprio texto bíblico · Philetus
- O autor pede que se lembre de Jesus Cristo ressuscitado dentre os mortos e descendente de Davi, a mensagem que ele chama de seu evangelho. O Easton's Bible Dictionary (1897) descreve Davi como o oitavo e mais novo filho de Jessé, cidadão de Belém, cujo trabalho inicial era apascentar as ovelhas do pai nas terras altas de Judá.Fontes: o próprio texto bíblico · David
- O serviço fiel é ilustrado com três imagens: um soldado que evita assuntos civis a fim de agradar a quem o alistou; um competidor que só recebe a coroa se competir segundo as regras; e um lavrador trabalhador, que deve ser o primeiro a participar da colheita. O autor também diz que sofre acorrentado como um criminoso, mas insiste que a palavra de Deus não pode ser acorrentada.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org