2 Pedro 3
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Yanzu, ina rubata maku, kaunatattu, wannan wasika ta biyu domin in tunashe ku, in kuma zuga tunaninku na gaskiya, 2don ku tuna da kalmomin da annabawa tsarkaka suka fada a da, kuma da umurnin Ubangijinmu da mai ceto da aka bayar ta wurin manzaninku. 3Ku san wannan da farko, cewa masu ba'a za su zo a kwanakin karshe. Za su yi ba'a kuma su ci gaba bisa ga sha'awowinsu. 4Za su ce, “Ina alkawarin dawowarsa? Tun lokacin da kakaninmu suka mutu, dukkan abubuwa sun kasance yadda suke, tun farkon halitta.” 5Da gangan suka manta cewa sama da kasa sun kasance daga ruwa, kuma ta wurin ruwa, da dadewa ta wurin umarnin Allah, 6kuma cewa ta wurin wadannan abubuwa duniyar wancan zamani ta halaka, da ambaliyar ruwan tsufana. 7Amma sama da kasa na yanzu, an tanada su domin wuta ta wurin wannan umarnin. An tanada su domin ranar shari'a da halakar marassa ibada. 8Kada ku manta da wanan, kaunatattu, cewa rana daya a gun Allah kamar shekaru dubu ne, kuma shekaru dubu kamar rana daya suke. 9Ubangiji baya jinkiri game da alkawaransa kamar yadda wadansu ke ganin jinkiri. Maimakon haka, yana hakuri da ku. Ba ya so ko dayanku ya hallaka, amma kowanenku ya kai ga tuba. 10Duk da haka, ranar Ubangiji za ta zo kamar barawo. Sammai za su shude da kara mai karfi. Wuta zata kone komai da komai, kuma duniya da dukkan ayyukan da ke cikinta zasu bayyanu. 11Da shike dukkan wadanan abubuwa za a hallaka su haka, wadanne irin mutane yakamata ku zama? Ya kamata kuyi rayuwar tsarki da ta ibada. 12Ku zauna cikin bege da kuma hanzarta zuwan ranar Allah. A ranan nan, za a hallaka sammai da wuta, kuma dukkan komai da komai zai narke cikin zafi mai tsanani. 13Amma bisa ga alkawarinsa, muna jiran sabuwar sama da sabuwar duniya, inda adalci zai kasance. 14Saboda haka, kaunatattu, tun da kuna da begen wadannan abubuwa, ku yi iyakacin kokarinku a same ku marassa tabo da marasa aibu a gabansa, cikin salama. 15Kuma, ku dauki hakurin Ubangiji domin ceto ne, kamar yadda kaunataccen danuwanmu Bulus ya rubuta maku bisa ga hikima da aka ba shi. 16Bulus yayi magana akan wadanan abubuwa cikin dukkan wasikunsa, a ciki akwai abubuwa da suke da wuyar ganewa. Jahilai da mutane marassa natsuwa sukan juya ma'anarsu, kamar yadda suke yi wa sauran nassoshi, don hallakar kansu. 17Saboda haka, kaunatattu, tun da kun san wadannan abubuwa, ku kula da kanku kada a badda ku ta wurin rudun mutanen da ba su bin doka, har ku rasa amincinku. 18Amma ku yi girma a cikin alheri da sanin Ubangijinmu da mai ceto Yesu Almasihu. Bari daukaka ta tabbata a gare shi yanzu da har abada. Amin.

Você sabia?
Zombadores e o Dia do Senhor
- Este capítulo diz que, nos últimos dias, virão zombadores, seguindo os próprios desejos maus, e perguntarão onde está a promessa da vinda dele. Afirmarão que, desde que os pais adormeceram, tudo continua como desde o princípio da criação. A carta responde que eles ignoram de propósito que, pela palavra de Deus, os céus já existiam e a terra foi formada da água e por meio da água, que o mundo daquele tempo pereceu no dilúvio e que os céus e a terra de agora estão reservados para o fogo até o dia do juízo.Fontes: o próprio texto bíblico
- A carta pede aos leitores que não deixem passar isto: para o Senhor, um dia é como mil anos, e mil anos são como um dia. Diz que o Senhor não tarda em cumprir a promessa, como alguns entendem a demora, mas é paciente, não querendo que ninguém pereça, e sim que todos cheguem ao arrependimento. Acrescenta que o Dia do Senhor virá como um ladrão e que o autor e seus leitores aguardam, segundo a promessa de Deus, um novo céu e uma nova terra, onde habita a justiça.Fontes: o próprio texto bíblico
- O autor chama Paulo de irmão amado que também escreveu a esses leitores, com a sabedoria que Deus lhe deu, sobre esses assuntos, e diz que Paulo escreve assim em todas as suas cartas. Algumas partes dessas cartas são chamadas de difíceis de entender, e pessoas ignorantes e instáveis as distorcem, como fazem com o restante das Escrituras, para a própria destruição. O Dicionário Bíblico de Easton (1897) identifica Paulo com Saulo e o descreve como natural de Tarso, capital da Cilícia, província romana no sudeste da Ásia Menor; afirma que o nome Paulo provavelmente lhe foi dado na infância para uso no mundo gentio.Fontes: o próprio texto bíblico · Paul
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org