2 Coríntios 10
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1Ni, Bulus, da kaina nake rokon ku, ta wurin tawali'u da nasihar Almasihu. Ina da saukin kai yayinda nake gaban ku, amma ina da gabagadi a gare ku yayinda ba na tare da ku. 2Ina rokon ku, yayinda nake gabanku, ba ni so in zama mai tsaurin hali. Amma ina ganin zan bukaci zama mai gabagadi sa'adda nake tsayayya da su wadanda ke zaton muna zama bisa ga jiki. 3Kodashike dai muna tafiya bisa jiki, ba ma yin yaki bisa jiki. 4Domin makaman da muke yaki da su ba na jiki ba ne. Maimakon haka, makamai ne na Allah da ke da ikon rushe ikokin shaidan. Suna kawar da dukan gardandamin da ke kawo kaucewa. 5Muna kuma rushe duk wani abinda ke gaba da sanin Allah. Muna kuma kama kowanne tunani zuwa biyayya ga Almasihu. 6Muna kuma shirye mu hukunta kowanne irin aiki na rashin biyayya, da zarar biyayyarku ta tabbata. 7Dubi abin da aka sa a bayyane a gaban ku. In har wani ya tabbata shi na Almasihu ne, bari fa ya tunatar da kansa cewa kamar yadda shi na Almasihu ne, hakanan muma muke. 8Ko da zan yi fahariya da ikon da muke dashi, wanda Ubangiji ya ba mu domin mu inganta ku, ba domin mu rushe ku ba, ba zan ji kunya ba. 9Ba na so ya zama kamar ina firgita ku ne da wasikuna. 10Domin wadansu mutane na cewa, “Wasikunsa na da iko da firgitarwa, amma in ka gan shi kumama ne. Kalmominsa ba abin saurare ba ne.” 11Bari wadannan mutane su sani cewa abinda muke fadi a kalmomin wasikunmu lokacin da ba mu nan, haka za mu yi in muna nan. 12Mu dai ba mu hada kanmu da kowa, ko kuma mu kwatanta kanmu da wadanda ke yabon kansu. Amma yayin da suke gwada kansu da junansu, suke kuma kwatanta kansu da junansu, ba su da ganewa. 13Saidai, ba za mu yi fahariya fiye da yadda ya kamata ba. Maimakon haka, za mu yi haka ne gwalgwadon iyakar abinda Allah ya sa muyi, iyakar da takai gareku. 14Gama bamu yi zarbabi ba sa'adda muka kai gareku. Mune na farko da muka kai gare ku da bisharar Almasihu. 15Ba mu yi fahariya fiye da kima game da aikin wasu ba. Maimakon haka, muna fatan bangaskiyar ku ta karu domin bangaren aikin mu ya kara fadada kwarai, kuma a daidai iyakarsa. 16Muna fatan haka, domin mu kai bishara zuwa yankunan da ke gaba da naku. Ba za mu yi fahariya akan aikin da aka yi a yankin wani ba. 17“Amma bari duk wanda zai yi fahariya, ya yi ta cikin Ubangiji.” 18Domin ba wanda ya ke shaidar kansa shine yardajje ba. Maimakon haka, sai dai wanda Ubangiji ke shaidarsa.

Você sabia?
Cartas, presença e uma guerra que não é deste mundo
- Algumas pessoas avaliavam Paulo pela aparência e pela fala. Admitiam que as cartas dele eram pesadas e enérgicas, mas diziam que a presença física não impressionava e que o falar não tinha valor. Ele responde que o que é nas cartas, quando ausente, será também nas ações, quando estiver presente.Fontes: o próprio texto bíblico
- Ele descreve o conflito em termos militares, mas não como uma luta comum. Viver na carne, diz ele, não significa guerrear segundo a carne. As armas de que fala não são as do mundo; têm poder divino para derrubar fortalezas, desfazer argumentos e toda pretensão levantada contra o conhecimento de Deus, e levar todo pensamento à obediência a Cristo.Fontes: o próprio texto bíblico
- Paulo não quer gloriar-se além do campo de influência que Deus lhe designou, um campo que já inclui os leitores, pois foi o primeiro a chegar até eles com o evangelho de Cristo. Quem se gloria, diz ele, deve gloriar-se no Senhor; a aprovação não é de quem recomenda a si mesmo, mas daquele a quem o Senhor recomenda.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Corinth · 37.906, 22.879 · versículo 14
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org