Nations Bible

1 Timóteo 2

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Don haka da farko dai, Ina roko a yi roke-roke da addu'o'i, da yin roko domin jama, a dukka, da ba da godiya, a yi haka domin dukkan mutane, 2domin sarakuna da dukkan masu mulki, domin mu yi zaman salama da rayuwa a natse cikin Allahntaka da daraja. 3Wannan yana da kyau da karbuwa a gaban Allah mai cetonmu. 4Yana so dukkan mutane su sami ceto, su kai ga sanin gaskiya. 5Domin Allah daya ne, Matsakanci kuma daya ne, tsakanin Allah da mutum, wannan mutum Almasihu Yesu ne. 6Ya bada kansa fansa domin kowa, domin shaida a daidaitaccen lokaci. 7Sabo da wannan dalilin, aka sa ni kaina, na zama mai shelar bishara da manzo. Gaskiya nake fada. Ba karya nake yi ba. Ni mai koyarwa ne na al'ummai cikin gaskiya da kuma imani. 8Saboda haka, ina so maza da ke a kowanne wuri suyi addu'a, kuma suna daga hannuwa masu tsarki a sama ba tare da fushi da gardama ba. 9Kazalika, ina so mata su sa kayan da ya cancanta, da adon da ya dace da kamun kai. Kada su zama masu kitson gashi da zinariya da azurfa da tufafi masu tsada. 10Ina so su sa tufafin da ya cancanci matan da ke rayuwar Allahntaka ta wurin kyawawan ayyuka. 11Mace ta koya cikin natsuwa da saukin kai a cikin komai. 12Ban ba da izini mace ta koyar ko ta nuna iko a kan namiji ba, amma ta zauna da natsuwa. 13Adamu ne aka fara halitta, kafin Hauwa'u. 14Ba Adamu ne aka yaudara ba, amma macen ce aka yaudara cikin laifi. 15Duk da haka, zata sami ceto ta wurin haifuwar 'ya'ya, idan suka ci gaba cikin bangaskiya, da kauna da tsarki da sahihiyar zuciya.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Oração, adoração modesta e Adão e Eva

  • Este capítulo exorta a que se ofereçam petições, orações, intercessões e ações de graças por todas as pessoas, inclusive pelos reis e por todos os que estão em autoridade, para que os crentes possam levar uma vida tranquila e sossegada, em toda piedade e dignidade. Diz também que há um só Deus e um só mediador entre Deus e os homens, o homem Cristo Jesus, que se entregou como resgate por todos.Fontes: o próprio texto bíblico
  • Quando a carta diz que Adão foi formado primeiro, e depois Eva, ela recorre ao primeiro homem de Gênesis. O Easton's Bible Dictionary (1897) explica que Adão é uma palavra babilônica que significa 'vermelho', o nome genérico de homem, com o mesmo sentido em hebraico e em assírio, e que ele foi formado do pó da terra.Fontes: o próprio texto bíblico · Adam
  • A carta diz que não foi Adão quem foi enganado, mas a mulher, que foi enganada e caiu em transgressão. O Easton's Bible Dictionary (1897) diz que Eva significa 'vida' ou 'vivente', o nome que Adão deu à sua mulher, e que o relato da criação dela está em Gênesis 2:21-22.Fontes: o próprio texto bíblico · Eve

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.