1 Tessalonicenses 4
Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
1A karshe, 'yan'uwa, muna karfafa ku kuma muna yi maku gargadi cikin Ubangiji Yesu. Yadda kuka karbi umarni a garemu game da yadda dole za kuyi tafiya kuma ku gamshi Allah, kuma a cikin wannan hanya ku tafi, ku kuma wuce haka. 2Domin kun san umarnin da muka baku cikin Ubangiji Yesu. 3Gama wannan ne nufin Allah: kebewar ku - cewa ku kauce wa zina da fasikanci, 4Cewa kowannenku ya san yadda zai rike mata tasa cikin tsarki da girmamawa. 5Kada kayi mata cikin zautuwar sha'awa ( kamar al'ummai wadanda basu san Allah ba). 6Kada wani ya kuskura yaci amanar dan'uwansa akan wannan al'amari. Gama Ubangiji mai ramuwa ne akan dukkan wadannan al'amura, Kamar yadda a baya muka yi maku kashedi kuma muka shaida. 7Gama Allah bai kira mu ga rashin tsarki ba, amma ga rayuwar tsarki. 8Domin haka, duk wanda yaki wannan ba mutane yaki ba, amma Allah, wanda ya bada Ruhunsa Mai Tsarki a gareku. 9Game da kaunar 'yan'uwa, baku bukatar wani ya sake rubuta maku, gama ku da kanku Allah ya koyar da ku kaunar 'yan'uwa. 10Ba shakka, kunayin haka ga dukkan 'yan'uwa wadanda ke cikin dukkan Makidoniya. Amma muna gargadin ku 'yan'uwa, kuyi haka bugu da kari. 11Kuma muna gargadin ku 'yan'uwa kuyi kokari ku zauna a natse, ku kula da al'amuranku, kuyi aiki da hannuwanku, Yadda muka umarceku a baya. 12Kuyi haka domin tafiyar ku ta zama dai dai a gaban wadanda basu bada gaskiya ba, kuma ya zama baku cikin bukatar komai. 13Bamu so ku zama da rashin fahimta ba, 'yan'uwa, game da wadanda sukayi barci, domin kada kuyi bacin rai kamar sauran wadanda basu da tabbacin abinda ke gaba. 14Domin idan mun bada gaskiya Yesu ya mutu kuma ya tashi, haka kuma tare da Yesu Allah zai maido da duk wadanda suka yi barci a cikinsa. 15Gama muna fada maku wannan daga maganar Ubangiji, cewa mu da muke a raye, da aka bari har zuwan Ubangiji, babu shakka ba za mu riga wadanda suka yi barci ba. 16Gama Ubangiji da kan sa zai sauko daga sama. Zai zo da muryar babban mala'ika, da karar kahon Allah, sai matattu cikin Almasihu su fara tashi. 17Sai mu da muke a raye, wadanda aka bari, tare dasu za'a fyauce mu zuwa cikin gizagizai, mu hadu da Ubangiji cikin sararin sama. Haka zamu cigaba da kasancewa da Ubangiji. 18Domin haka ku ta'azantar da juna da wadannan maganganu.

Você sabia?
Santidade, amor e esperança pelos que morreram
- Este capítulo observa que seus leitores já demonstravam amor a todos os irmãos por toda a Macedônia. Nos tempos do Novo Testamento, a Macedônia era uma província romana situada ao norte da Grécia, governada por um propretor com o título de procônsul. Paulo foi chamado por uma visão do "homem da Macedônia" para pregar o evangelho ali.Fontes: o próprio texto bíblico · Macedonia
- O capítulo fala dos mortos como pessoas que dormem ou adormeceram, e pede aos leitores que não se entristeçam como os demais, que não têm esperança. Porque Jesus morreu e ressuscitou, diz o texto, Deus trará com Jesus os que nele adormeceram; os mortos em Cristo ressuscitarão primeiro, e então os que ainda estiverem vivos serão arrebatados com eles nas nuvens para encontrar o Senhor nos ares.Fontes: o próprio texto bíblico
- Os leitores são exortados a aspirar a uma vida tranquila, a cuidar dos próprios assuntos e a trabalhar com as próprias mãos, como já lhes havia sido instruído. O capítulo apresenta isso como o modo de se portar corretamente diante dos de fora e de não depender de ninguém.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Macedonia · 41.600, 22.540 · versículo 10
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org