Nations Bible

1 Pedro 3

Litafi Mai-tsarki · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.

1Haka ku kuma da kuke matan aure, kuyi biyayya da na ku mazajen, domin in har wadansunsu basa biyayya da maganar Allah, halin matansu ya shawo kansu ba tare da magana ba, 2Domin sun ga tsattsakan halinku da ladabinku. 3Haka ma adonku kar ya zama na kwalliyar waje kitson kai, kayan zinariya ko tufafi masu kawa. 4Amma bari adon ya zama na mutum na cikin zuciya, kuma adon ya zama kyan nan marar dushewa, na kamun kai da natsatsen ruhu, wanda yake da daraja a gaban Allah. 5Haka tsarkakan mata su ka yi ado kamar haka. Suka dogara ga Allah suka yi biyayya ga mazajensu. 6Ta haka Saratu ta yi biyayya ga Ibrahim ta kira shi “ubangiji”. Yanzu ku 'ya'yantane in dai kun yi aiki nagari, idan kuma ba ku ji tsoron wahala ba. 7Kamar yadda na fada wa matan aure haka ma mazaje, ku zauna da mata da sanin su raunana ne abokan tarayya ne na karbar baiwar rayuwa. Ku dinga yin haka domin a rika jin addu'oinku. 8Daga karshe, dukanku ku hada hankulanku, ku zama masu juyayi, masu kauna kamar 'yan'uwa, masu taushin zuciya, masu tawali'u. 9Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi. A maimakon haka ku cigaba da sa albarka, gama sabili da haka ne musamman aka kiraye ku, domin ku gaji albarka. 10“Wanda duk yake so ya more a rayuwarsa ya kuma ga kwanaki masu alheri, to fa, ya kame harshen sa daga mugunta da lebensa daga maganganun yaudara. 11Ya rabu da mugunta ya aikata abin da ke nagari. Bari ya nemi zaman salama ya kuma dimanceta. 12Idanun Ubangiji suna duban adalai, kunnuwansa kuma suna sauraron roke rokensu. Amma fuskar Ubangiji tana gaba da masu aikata mugunta.” 13Wanene ya isa ya cuce ku idan kun himmatu ga yin abin da ke nagari? 14Amma idan kuna shan wuya saboda adalci, ku masu albarka ne. Kada ku ji tsoron abin da su ke tsoro. Kada ku damu. 15Maimakon haka, ku kebe Ubangiji a cikin zukatanku cewa shi mai tsarki ne. Kullum ku zauna da shiri domin ku amsa wa mai tambayar ku dalilin sa begenku ga Allah. Amma fa kuyi haka tare da tawali'u da bangirma. 16Ku zama da tsatsakan lamiri domin mutanen da ke zargin rayuwarku mai kyau cikin Almasihu, su ji kunya domin suna maganar gaba da ku kamar ku mugaye ne. 17Ya fi kyau, a sha wuya akan aiki nagari, idan nufin Allah ne, da a sha wuya sabili da mugun aiki. 18Almasihu ya sha wahala sau daya tak sabili da zunubai. Shi da ya ke mai adalci ya sha wahala domin mu marasa adalci, domin ya kawo mu ga Allah. Aka kashe shi cikin jiki, amma aka rayar da shi cikin Ruhu. 19A Ruhu ne, ya je ya yi wa'azi ga ruhohin da ke a yanzu cikin kurkuku. 20Sun yi rashin biyayya ne sa'adda hakurin Allah yake jiransu a lokacin Nuhu a zamanin sassaka jirgin ruwa, sai Allah ya tsirar da mutane kalilan wato rayuka takwas daga cikin ruwa. 21Wannan kwatancin baftismar da take cetonmu yanzu ne, ba kamar ta wanke Dauda daga jiki ba, sai dai ta rokon Allah da lamiri mai kyau ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu. 22Ya hau sama. Yana dama ga Allah. Mala'iku, da mulkoki da masu iko dole su yi masa biyayya.

Ilustração artística — interpretação, não registro histórico.

Você sabia?

Conduta, sofrimento e esperança

  • Em 1 Pedro 3, a carta lembra as mulheres santas do passado, que puseram sua esperança em Deus e foram submissas a seus maridos, e nomeia Sara, que obedeceu a Abraão e o chamou de senhor. Diz a elas que são filhas de Sara se fizerem o que é certo e se recusarem a ceder ao medo. O dicionário bíblico de Easton (1897) diz que Sara significa “Princesa” e que esse nome lhe foi dado quando se anunciou que ela seria a mãe do filho prometido.Fontes: o próprio texto bíblico · Sarah
  • Abraão, o marido a quem Sara obedeceu e a quem chamou de senhor, é descrito pelo dicionário bíblico de Easton (1897) como “Pai de uma multidão”. O mesmo verbete o chama de filho de Terá e herdeiro das promessas.Fontes: o próprio texto bíblico · Abraham
  • O capítulo também retoma os dias de Noé, quando Deus esperou pacientemente enquanto a arca era construída e apenas oito almas foram salvas por meio da água; a carta diz que essa água simboliza o batismo. O dicionário bíblico de Easton (1897) apresenta o nome Noé com o sentido de “Descanso” e nomeia seus três filhos como Sem, Cam e Jafé.Fontes: o próprio texto bíblico · Noah

Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.

Créditos e licença desta tradução
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Fonte: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Fale com a gente

Conte de onde você lê, como a Bíblia tem te ajudado ou o que podemos melhorar. Lemos todas as mensagens.