Números 33
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
Wurare a tafiye-tafiyen Isra’ila
1Ga wuraren da Isra’ilawa suka yi sansani sa’ad da suka fito runduna-runduna a ƙarƙashin Musa da Haruna daga Masar. 2Bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya rubuta wuraren tafiye-tafiyensu da sansaninsu. Ga yadda tafiye-tafiyen suka kasance.
3Isra’ilawa sun tashi daga Rameses a rana ta goma sha biyar, ga watan fari, kashegarin Bikin Ƙetarewa. Suka fita gabagadi a gaban dukan Masarawa, 4waɗanda suke binne gawawwakin ’ya’yan farinsu da Ubangiji ya karkashe; gama Ubangiji ya hukunta allolinsu.
5Isra’ilawa suka tashi daga Rameses, suka yi sansani a Sukkot.
6Suka tashi daga Sukkot, suka yi sansani a Etam, a gefen hamada.
7Suka tashi daga Etam, suka koma baya zuwa Fi Hahirot, wajen gabashin Ba’al-Zafon, suka yi sansani kusa da Migdol.
8Suka tashi daga Fi Hahirot, suka ratsa cikin teku zuwa hamada, bayan sun yi tafiya kwana uku a cikin Hamadan Etam, sai suka yi sansani a Mara.
9Suka tashi daga Mara, suka tafi Elim, inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu, da itatuwan dabino guda saba’in, suka yi sansani a can.
10Suka tashi daga Elim, suka yi sansani kusa da Jan Teku.
11Suka tashi daga Jan Teku, suka yi sansani a Hamadan Sin.
12Suka tashi daga Hamadan Sin, suka yi sansani a Dofka.
13Suka tashi daga Dofka, suka yi sansani a Alush.
14Suka tashi daga Alush, suka yi sansani a Refidim, inda babu ruwan da mutane za su sha.
15Suka tashi daga Refidim, suka yi sansani a Hamadan Sinai.
16Suka tashi daga Hamadan Sinai, suka yi sansani a Kibrot Hatta’awa.
17Suka tashi daga Kibrot Hatta’awa, suka yi sansani a Hazerot.
18Suka tashi daga Hazerot, suka yi sansani a Ritma.
19Suka tashi daga Ritma, suka yi sansani a Rimmon Ferez.
20Suka tashi daga Rimmon Ferez, suka yi sansani a Libna.
21Suka tashi daga Libna, suka yi sansani a Rissa.
22Suka tashi daga Rissa, suka yi sansani a Kehelata.
23Suka tashi daga Kehelata, suka yi sansani a Dutsen Shefer.
24Suka tashi daga Dutsen Shefer, suka yi sansani a Harada.
25Suka tashi daga Harada, suka yi sansani a Makhelot.
26Suka tashi daga Makhelot, suka yi sansani a Tahat.
27Suka tashi daga Tahat, suka yi sansani a Tera.
28Suka tashi daga Tera, suka yi sansani a Mitka.
29Suka tashi daga Mitka, suka yi sansani a Hashmona.
30Suka tashi daga Hashmona, suka yi sansani a Moserot.
31Suka tashi daga Moserot, suka yi sansani a Bene Ya’akan.
32Suka tashi daga Bene Ya’akan, suka yi sansani a Hor Haggidgad.
33Suka tashi daga Hor Haggidgad, suka yi sansani a Yotbata.
34Suka tashi daga Yotbata, suka yi sansani a Abrona.
35Suka tashi daga Abrona, suka yi sansani a Eziyon Geber.
36Suka tashi daga Eziyon Geber, suka yi sansani a Kadesh, cikin Hamadan Zin.
37Suka tashi daga Kadesh, suka yi sansani a Dutsen Hor, a iyakar Edom. 38Bisa ga umarni Ubangiji, Haruna firist, ya hau Dutsen Hor, inda ya mutu a rana ta fari ga watan biyar, a shekara ta arba’in, bayan Isra’ilawa suka fito daga Masar. 39Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku, sa’ad da ya mutu a Dutsen Hor.
40Sarki Arad Bakan’ane, wanda yake zaune a Negeb na Kan’ana, ya ji labari cewa Isra’ilawa suna zuwa.
41Suka tashi daga Dutsen Hor, suka yi sansani a Zalmona.
42Suka tashi daga Zalmona, suka yi sansani a Funon.
43Suka tashi daga Funon, suka yi sansani a Obot.
44Suka tashi daga Obot, suka yi sansani a Iye Abarim, a iyakar Mowab.
45Suka tashi daga Iyim, suka yi sansani a Dibon Gad.
46Suka tashi daga Dibon Gad, suka yi sansani a Almon Dibilatayim.
47Suka tashi daga Almon Dibilatayim, suka yi sansani a duwatsun Abarim, kusa da Nebo.
48Suka tashi daga duwatsun Abarim, suka yi sansani a filayen Mowab kusa da Urdun, ɗaura da Yeriko. 49A can filayen Mowab, suka yi sansani kusa da Urdun ɗaura da Bet-Yeshimot har zuwa Abel-Shittim.
50A filayen Mowab kusa da Urdun ɗaura da Yeriko ne Ubangiji ya ce wa Musa, 51“Ka gaya wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa Kan’ana, 52ku kori dukan mazaunan ƙasar a gabanku. Ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsu, da siffofinsu na zubi, ku kuma rurrushe dukan masujadansu na kan tudu. 53Ku mallaki ƙasar, ku kuma zauna a ciki, gama na ba ku ƙasar, ku mallake ta. 54Ku rarraba ƙasar ta wurin jefan ƙuri’a, bisa ga kabilanku. Kabilar da take babba, a ba ta babban gādo, ƙarami kabila kuwa, a ba ta ƙaramin gādo. Duk abin da ƙuri’a ta ba su, shi zai zama nasu. Ku rarraba wannan bisa zuriyar kakanninku.
55“ ‘Amma in ba ku kori mazaunan ƙasar ba, waɗanda kuka bari su ci gaba da zama, za su zama muku hakki a idanunku, da kuma ƙayayyuwa a bayanku. Za su ba ku wahala a ƙasar da kuke zama. 56Sa’an nan kuwa zan yi muku abin da na shirya yin musu.’ ”

Você sabia?
O itinerário pelo deserto e as instruções finais
- Por ordem de Deus, Moisés registrou o itinerário completo da jornada de Israel, começando com a partida de Ramessés, no Egito, e concluindo no acampamento nas planícies de Moabe, junto ao Jordão, em frente a Jericó.Fontes: o próprio texto bíblico · Rameses · Moab
- O itinerário registra a morte do sacerdote Arão no topo do monte Hor, na fronteira de Edom, ocorrida no primeiro dia do quinto mês do quadragésimo ano após o Êxodo, quando ele tinha 123 anos de idade.Fontes: o próprio texto bíblico · Mount Hor · Aaron
- Em seu último acampamento junto ao Jordão, Israel recebeu ordens para destruir todas as imagens esculpidas, ídolos de fundição e altos em Canaã, e repartir a terra entre suas tribos e clãs por sorteio, de acordo com o tamanho de cada um.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Egypt · 30.129, 31.308 · versículos 1, 4, 38
- Wilderness of Sinai · Hoje: about 50 km around Jebel Musa · 28.540, 33.973 · versículos 15, 16
- Mount Shepher · Hoje: within 50 km of Wadi Lussan · 30.507, 34.304 · versículos 23, 24
- Terah · Hoje: within 50 km of Wadi Umm Hashim · 30.641, 34.411 · versículos 27, 28
- Zin · Hoje: Zin Desert · 30.971, 35.325 · versículo 36
- Edom · 30.746, 35.604 · versículo 37
- Canaan · 32.767, 35.333 · versículos 40, 51
- Negeb · 31.245, 34.841 · versículo 40
- Moab · Hoje: Moab 1 · 31.181, 35.701 · versículo 44
- Dibon · Hoje: Tall Dhiban · 31.502, 35.777 · versículos 45, 46
- Abarim · 31.754, 35.715 · versículos 47, 48
- Jericho · Hoje: Tell es Sultan · 31.872, 35.445 · versículos 48, 50
- Jordan · Hoje: Jordan River · 31.761, 35.558 · versículos 48, 49, 50, 51
- Moab · Hoje: Moab 2 · 31.840, 35.674 · versículos 48, 49, 50
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org