Números 26
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
Ƙidaya ta biyu
1Bayan annobar, sai Ubangiji ya yi magana da Musa da Eleyazar ɗan Haruna, firist ya ce, 2“Ku ƙidaya dukan jama’ar Isra’ila daga mai shekaru ashirin zuwa gaba da za su iya aikin sojan Isra’ila.” 3Musa da Eleyazar firist suka yi musu magana a filayen Mowab kusa da Urdun daga ƙetaren Yeriko, suka ce, 4“Ku ƙidaya maza daga mai shekara ashirin zuwa gaba yadda Ubangiji ya umarci Musa.”
5Zuriyar Ruben ɗan fari na Isra’ila,
daga Hanok; kabilar Hanokawa;
daga Fallu; kabilar Falluyawa;
6daga Hezron, kabilar Hezronawa;
daga Karmi, kabilar Karmiyawa. 7Waɗannan su ne kabilan Ruben; jimillarsu ta kai 43,730.
8Ɗan Fallu kuwa shi ne Eliyab, 9’ya’yan Eliyab maza kuwa su ne, Nemuwel, Datan da Abiram. Datan da Abiram nan, su ne shugabannin mutanen da suka tayar wa Musa da Haruna, suna kuma cikin waɗanda suka bi Kora sa’ad da ya tayar wa Ubangiji. 10Ƙasa kuwa ta buɗe ta haɗiye su tare da Kora, wanda ƙungiyarsa ta mutu sa’ad da wuta ta cinye mutum 250. Wannan kuwa ya zama alamar faɗakarwa. 11Amma fa, zuriyar Kora ba tă mutu ba.
12Zuriyar Simeyon bisa ga kabilansu,
daga Nemuwel, kabilar Nemuwelawa;
daga Yamin, kabilar Yaminawa;
daga Yakin, kabilar Yakinawa;
13daga Zera, kabilar Zerawa;
daga Sha’ul, kabilar Sha’ul. 14Waɗannan su ne kabilan Simeyon; jimillarsu ta kai 22,200.
15Zuriyar Gad bisa ga kabilansu,
daga Zafon, kabilar Zafonawa;
daga Haggi, kabilar Haggiwa;
daga Shuni, kabilar Shunawa;
16daga Ozni, kabilar Ozniyawa
daga Eri, kabilar Eriyawa;
17daga Arod, kabilar Arodiyawa;
daga Areli, kabilar Areliyawa. 18Waɗannan su ne kabilan Gad, jimillarsu ta kai 40,500.
19Er da Onan, ’ya’yan Yahuda ne, amma sun mutu a Kan’ana.
20Zuriyar Yahuda bisa ga kabilansu,
daga Shela, kabilar Shelayawa
daga Ferez, kabilar Ferezawa;
daga Zera, kabilar Zerawa;
21Zuriyar Ferez kuwa,
daga Hezron, kabilar Hezronawa;
daga Hamul; kabilar Hamulawa. 22Waɗannan su ne kabilan Yahuda; jimillarsu ta kai 76,500.
23Zuriyar Issakar bisa ga kabilansu,
daga Tola, kabilar Tolatawa;
daga Fuwa, kabilar Fuwayawa;
24daga Yashub, kabilar Yashubawa;
daga Shimron, kabilar Shimronawa. 25Waɗannan su ne kabilan Issakar; jimillarsu ta kai 64,300.
26Zuriyar Zebulun bisa ga kabilansu,
daga Sered, kabilar Seredawa;
daga Elon kabilar Elonawa;
daga Yaleyel; kabilar Yaleyewa. 27Waɗannan su ne kabilan Zebulun, jimillarsu ta kai 60,500.
28Zuriyar Yusuf bisa ga kabilansu ta wurin Manasse da Efraim.
29Zuriyar Manasse,
daga Makir, kabilar Makiriyawa (Makir shi ne mahaifin Gileyad);
daga Gileyad, kabilar Gileyadawa.
30Waɗannan su ne zuriya Gileyad,
daga Iyezer, kabilar Iyezerawa;
daga Helek, kabilar Helekawa;
31daga Asriyel, kabilar Asriyelawa;
daga Shekem, kabilar Shekem;
32daga Shemida, kabilar Shemadawa;
daga Hefer, kabilar Heferawa.
33(Zelofehad ɗan Hefer, ba shi da ’ya’ya maza; ’yan mata ne kaɗai ya haifa, sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza.) 34Waɗannan su ne kabilan Manasse, jimillarsu ta kai 52,700.
35Waɗannan su ne kabilan Efraim bisa ga kabilansu,
daga Shutela, kabilar Shutelawa;
daga Beker, kabilar Bekerawa;
daga Tahan, kabilar Tahanawa.
36Waɗannan su ne kabilan Shutelawa,
daga Eran, kabilar Eranawa. 37Waɗannan su ne kabilan Efraim; jimillarsu ta kai 32,500.
38Zuriyar Benyamin bisa ga kabilansu,
daga Bela, kabilar Belawa;
daga Ashbel, kabilar Ashbelawa;
daga Ahiram, kabilar Ahiramawa;
39daga Shufam, kabilar Shufamawa;
daga Hufam, kabilar Hufamawa.
40Zuriyar Bela daga Ard da Na’aman,
daga Ard, kabilar Ardawa;
daga Na’aman, kabilar Na’amawa; 41Waɗannan su ne kabilan Benyamin, jimillarsu ta kai 45,600.
42Waɗannan su ne kabilan Dan bisa ga kabilarsu,
daga Shuham, kabilar Shuhamawa. 43Dukansu kabilan Shuhamawa ne, jimillarsu ta kai 64,400.
44Zuriyar Asher bisa ga kabilansu,
daga Imna, kabilar Imnawa
daga Ishbi, kabilar Ishbiyawa;
daga Beriya, kabilar Beriyawa;
45daga zuriyar Beriya kuwa,
daga Heber, kabilar Heberawa;
daga Malkiyel, kabilar Malkiyelawa. 46(Asher yana da ’ya mace da ake kira Sera.) 47Waɗannan su ne kabilan Asher; jimillarsu ta kai 53,400.
48Zuriyar Naftali bisa ga kabilansu,
daga Yazeyel, kabilar Yazeyelawa;
daga Guni, kabilar Guniyawa;
49daga Yezer, kabilar Yezerawa;
daga Shillem, kabilar Shillemawa. 50Waɗannan su ne kabilan Naftali, jimillarsu ta kai 45,400.
51Dukan jimillar mazan Isra’ila ta kai 601,730.
52Ubangiji ya ce wa Musa, 53“Ka rarraba musu ƙasar a matsayin gādo, bisa ga yawan kabila. 54Ga ƙungiya mafi girma, ka ba ta rabo mafi girma; ga ƙaramar ƙungiya kuwa, ka ba ta ƙarami rabo; kowane zai karɓa rabonsa ga yawan mutanen da aka rubuta. 55Ka tabbatar an rarraba ƙasar ta wurin rabo. Abin da kowace ƙungiya ta gāda zai zama bisa ga sunayen kabilar kakanninta. 56Za a raba kowane gādo bisa ga rabo tsakanin manyan da ƙanana ƙungiyoyi.”
57Waɗannan su ne Lawiyawa da a ƙidaya bisa ga kabilansu,
daga Gershom, kabilar Gershonawa;
daga Kohat, kabilar Kohatawa;
daga Merari, kabilar Merari.
58Waɗannan kuma su ne kabilan Lawiyawa,
kabilar Libniyawa,
kabilar Hebronawa,
kabilar Maliyawa,
kabilar Mushiyawa,
kabilar Korayawa
(Kohat shi ne kakan Amram; 59sunan matan Amram shi ne Yokebed, ita zuriyar Lawi ce, wadda aka haifa wa Lawiyawa a Masar. A wajen Amram kuwa ta haifi Haruna, Musa da kuma ’yar’uwarsu Miriyam. 60Haruna shi ne mahaifin Nadab, Abihu, Eleyazar da kuma Itamar. 61Amma Nadab da Abihu sun mutu sa’ad da suka miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji.)
62Dukan ’ya’yan Lawiyawa maza daga wata ɗaya zuwa gaba, jimillarsu ta kai 23,000. Ba a ƙidaya su tare da sauran Isra’ilawa ba, domin ba a ba su gādo tare da su ba.
63Waɗannan su ne waɗanda Musa da Eleyazar firist, suka ƙidaya sa’ad da suka ƙidaya Isra’ilawa a filaye Mowab kusa da Urdun a hayen Yeriko. 64Ba ko ɗayansu da yake cikin waɗanda Musa da Haruna firist, suka ƙidaya sa’ad da suka ƙidaya Isra’ilawa a Hamadar Sinai. 65Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa waɗancan Isra’ilawa cewa lalle za su mutu a hamada, kuma ba ko ɗayansu da ya rage, sai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.

Você sabia?
O segundo censo nas campinas de Moabe
- Este segundo censo militar foi realizado por Moisés e pelo sumo sacerdote Eleazar nas campinas de Moabe, junto ao Jordão, em frente a Jericó. Foram contados 601.730 homens de vinte anos para cima aptos para o exército, servindo de base para a divisão da terra prometida por sorteio entre as tribos de acordo com o seu tamanho.Fontes: o próprio texto bíblico · Eleazar · Moab
- O censo assinalou uma mudança geracional completa: de todos os israelitas contados originalmente no monte Sinai, nenhum homem continuava vivo, com exceção de Calebe, filho de Jefoné, e Josué, filho de Num.Fontes: o próprio texto bíblico · Sinai
- Os levitas foram contados separadamente das demais tribos, totalizando 23.000 homens de um mês de idade ou mais. Visto que não receberiam uma herança territorial entre os outros israelitas, eles não foram incluídos no censo geral.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Jericho · Hoje: Tell es Sultan · 31.872, 35.445 · versículos 3, 63
- Jordan · Hoje: Jordan River · 31.761, 35.558 · versículos 3, 63
- Moab · Hoje: Moab 2 · 31.840, 35.674 · versículos 3, 63
- Egypt · 30.129, 31.308 · versículos 4, 59
- Canaan · 32.767, 35.333 · versículo 19
- Wilderness of Sinai · Hoje: about 50 km around Jebel Musa · 28.540, 33.973 · versículo 64
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org