Levítico 15
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
Mugunyar da ke sa ƙazantuwa
1Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, 2“Yi wa Isra’ilawa magana, ku ce musu, ‘Duk sa’ad da wani namiji yake ɗiga daga azzakarinsa, wannan ɗiga marar tsarki ne. 3Ko ɗigar ta ci gaba da fitowa daga azzakarinsa ko an tsere ta, za tă sa mutumin yă zama marar tsarki. Ga yadda ɗigarsa za tă kawo ƙazantuwa,
4“ ‘Duk gadon da mutumin mai ɗigar ya kwanta a kai, zai zama marar tsarki, kuma duk abin da ya zauna a kai, zai zama marar tsarki. 5Duk wanda ya taɓa gadonsa dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma. 6Duk wanda ya zauna a inda wannan mai ɗiga ya zauna a kai, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.
7“ ‘Duk wanda ya taɓa jikin mai ɗiga, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
8“ ‘In mai ɗiga ya tofa miyau a kan wani wanda yake tsarkakakke, dole tsarkakakken nan yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
9“ ‘Kowane sirdi da mai ɗigar ya zauna a kai zai ƙazantu, 10kuma duk wanda ya taɓa wani abu cikin abubuwan da suke a ƙarƙashin sirdin zai ƙazantu har yamma; duk wanda ya ɗauki abubuwan nan dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.
11“ ‘Duk wanda mai ɗiga ya taɓa ba tare da ya wanke hannuwansa da ruwa ba, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
12“ ‘Dole a farfashe tukunya lakar da mutumin ya taɓa, kuma dole a ɗauraye duk wani abin da aka yi da katako wanda ya taɓa da ruwa.
13“ ‘Sa’ad da aka tsabtacce mai ɗigar, zai ɗauki kwana bakwai don tsabtaccewarsa; dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka mai tsabta, zai kuwa zama tsarkakakke. 14A rana ta takwas dole yă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, yă zo gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada, yă ba da su ga firist. 15Firist ɗin zai miƙa su, ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mai ɗigar.
16“ ‘Sa’ad da namiji ya ɗigar maniyyi, dole yă wanke jikinsa gaba ɗaya da ruwa, zai kuma ƙazantu har yamma. 17Dole a wanke duk riga ko fatar da yake da maniyyin a kansa da ruwa, zai kuma ƙazantu har yamma. 18Sa’ad da namiji ya kwana da mace ya kuwa zub da maniyyi, dole dukansu biyu su yi wanka, za su kuma ƙazantu har yamma.
19“ ‘Sa’ad mace take al’adarta ta ƙa’ida, rashin tsabtarta ta al’adar zai ɗauki kwana bakwai, kuma duk wanda ya taɓa ta, zai ƙazantu har yamma.
20“ ‘Duk abin da ta kwanta a kai a lokacin al’adarta zai ƙazantu, kuma duk abin da ta zauna a kai zai ƙazantu. 21Duk wanda ya taɓa gadonta dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma. 22Duk wanda ya taɓa wani abin da ta zauna a kai, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma. 23Ko gado ne, ko kuwa wani abin da ta zauna a kai, sa’ad da wani ya taɓa shi, zai ƙazantu har yamma.
24“ ‘In namiji ya kwana da ita, al’adarta kuwa ta taɓa shi, zai ƙazantu na kwana bakwai; duk kuma gadon da ya kwanta a kai, zai ƙazantu.
25“ ‘Idan mace tana ɗigar jini na tsawon kwanaki, ban da kwanakin ganin al’adarta, ko kuwa idan al’adarta ya wuce yawan kwanakin da ya kamata, to, za tă ƙazantu daidai kamar na kwanakin al’adar da ta saba yi. Wato, muddin tana cikin ɗiga, ta zama mai ƙazanta. 26Duk gadon da ta kwanta yayinda ta ci gaba da ɗiga zai zama marar tsarki, kamar yadda gadonta yake a lokacin al’adarta, kuma duk abin da ta zauna a kai zai zama marar tsarki, kamar yadda yake a lokacin al’adarta. 27Duk wanda ta taɓa su zai zama marar tsarki; dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
28“ ‘Sa’ad da aka tsabtacce ta daga ɗigarta, dole tă ɗauki kwana bakwai, bayan haka za tă zama mai tsarki. 29A rana ta takwas, dole tă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabari biyu ta kawo su ga firist a bakin ƙofar Tentin Sujada. 30Firist zai miƙa ɗaya saboda hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda ƙazantar ɗigarta.
31“ ‘Ta haka za ka tsarkake Isra’ilawa daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da wurin zamana wanda yake tsakiyarsu.’ ”
32Waɗannan su ne ƙa’idodi a kan wanda yake ɗiga, da wanda yake zubar da maniyyi, 33ƙa’idodi ne kuma ga mace wadda take al’ada, ga namiji ko macen da take ɗiga, ga kuma namijin da ya kwana da mace marar tsarki.

Você sabia?
Leis sobre Fluxos Corporais e Purificação
- As leis de pureza em Levítico 15 regulavam fluxos corporais naturais e anormais em homens e mulheres, os quais tornavam as pessoas cerimonialmente impuras. Objetos tocados por uma pessoa com fluxo, como camas, assentos e selas, transmitiam impureza, exigindo que quem os tocasse lavasse as roupas, se banhasse e ficasse impuro até o entardecer.Fontes: o próprio texto bíblico
- A purificação de fluxos prolongados exigia uma espera de sete dias após a cura, a lavagem das vestes e o banho em água corrente. No oitavo dia, a pessoa levava duas rolinhas ou dois pombinhos ao sacerdote na entrada da Tenda do Encontro para serem oferecidos como oferta pelo pecado e holocausto.Fontes: o próprio texto bíblico
- O objetivo explícito dessas normas era manter os israelitas conscientes dos limites rituais, evitando que contaminassem o tabernáculo estabelecido no meio do acampamento.Fontes: o próprio texto bíblico
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org