Levítico 11
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toque num versículo para ver as referências cruzadas.
Abinci mai tsabta da marar tsabta
1Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, 2“Ku ce wa Isra’ilawa, ‘Cikin dabbobin da suke a doron ƙasa, waɗannan ne za ku ci. 3Za ku iya cin dabbobin da suke da rababben kofato, waɗanda suke kuma tuƙa.
4“ ‘Akwai waɗanda suke tuƙa ko kuwa suna da rababben kofato kawai, duk da haka ba za ku ci su ba. Waɗannan kuwa su ne, raƙumi, ko da yake yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato; saboda haka cin namansa haram ne gare ku. 5Rema, ko da yake tana tuƙa, duk da haka ba ta da rababben kofato; saboda haka namanta haram ne gare ku. 6Zomo, ko da yake yana tuƙa, duk da haka ba shi da rababben kofato; saboda haka namansa haram ne gare ku. 7Alade, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa, saboda haka namansa haram ne gare ku. 8Ba za ku ci namansu ba, ko ku taɓa gawawwakinsu, gama haram ne gare ku.
9“ ‘Cikin dukan halittu masu rai da suke a cikin ruwan tekuna da rafuffuka, za ku iya cin kowane da yake da ƙege da kamɓori. 10Amma kowace halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, ko cikin dukan abubuwa masu rai a ruwa ko kuma sauran halittu a cikin ruwa za ku ɗauka su marasa tsaki ne gare ku. 11Da yake abubuwan ƙyama ne a gare ku, ba za ku ci namansu ba, kuma dole ku yi ƙyamar gawawwakinsu. 12Duk abin da yake a ruwa amma ba shi da ƙege ko kamɓori, za ku yi ƙyamarsa.
13“ ‘Waɗannan su ne tsuntsayen da za ku yi ƙyamarsu, ba za ku ci su ba domin sun zama abin ƙyama. Tsuntsayen kuwa su ne, gaggafa, ungulu, baƙin ungulu, 14shirwa, da duk wani irin baƙin shirwa, 15kowane irin hankaka, 16mujiya mai ƙaho, jimina, shaho, da kowane irin shaho, 17ƙaramin ƙururu, babba da jaka, zalɓe, 18kazar ruwa, kwasakwasa, da ungulu, 19shamuwa, kowane irin jinjimi, katutu da kuma jamage.
20“ ‘Dukan ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu abin ƙyama ne gare ku. 21Sai dai akwai ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu da za ku ci; waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle. 22Za ku iya cin kowane irin fāra, gyare, ƙwanso da danginsu. 23Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, suna kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku.
24“ ‘Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har fāɗuwar rana. 25Duk wanda ya ɗauki ɗaya daga cikin gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har zuwa yamma.
26“ ‘Kowace dabbar da ba ta da rababben kofato ko ba ta tuƙa, haram ce gare ku; duk wanda ya taɓa gawarsu zai ƙazantu. 27Duk abin da yake tafiya a kan dāginsa cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa yamma. 28Duk wanda ya ɗauki gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har yamma. Waɗannan dabbobi za su zama marasa tsabta a gare ku.
29“ ‘Waɗannan ƙananan dabbobi da suke rarrafe a ƙasa, haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa, 30da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo. 31Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma. 32Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai, zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma, sa’an nan zai tsarkaka. 33In waninsu ya fāɗi a cikin tukunyar laka, kome da yake a tukunyar zai ƙazantu, kuma dole a fashe tukunyar. 34Duk abincin da aka yarda a ci, wanda ya taɓa ruwa daga irin tukunyan nan zai zama marar tsabta, kuma duk ruwan da za a sha daga irin tukunyan nan ƙazantacce ne. 35Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai ya ƙazantu ke nan; ko a kan murhu, ko a tukunyar dahuwa, dole a farfashe su. Su haramtattu ne kuma dole ku ɗauke su haramtattu. 36Maɓuɓɓuga ko tafki na tarin ruwa zai ci gaba da zauna mai tsabta, amma duk wanda ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan gawawwakin ya haramtu. 37In gawa ta fāɗi a irin da za a shuka, irin zai ci gaba da zama mai tsabta. 38Amma in an sa ruwa a irin sai kuma gawar ta fāɗi a kai, to, irin ya zama haram gare ku.
39“ ‘In dabbar aka yarda a ci ta mutu, duk wanda ya taɓa gawarta zai ƙazantu har yamma. 40Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma.
41“ ‘Duk dabba mai rarrafe a ƙasa abin ƙyama ne; ba kuwa za a ci shi ba. 42Ba za ku ci wani halittar da take rarrafe a ƙasa, ko tana jan ciki, ko tana tafiya a kan ƙafafu huɗu, ko a kan ƙafafu da yawa ba; abin ƙyama ne. 43Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani daga waɗannan halittu. Kada ku ƙazantar da kanku ta dalilinsu, ko a mai da ku haramtattu ta wurinsu. 44Ni ne Ubangiji Allahnku; ku tsarkake kanku ku kuma zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani halittar da take rarrafe a ƙasa. 45Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku; saboda haka ku zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne.
46“ ‘Waɗannan ne ƙa’idodi game da dabbobi, tsuntsaye, da kowane abu mai rai da yake motsi a cikin ruwa, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa. 47Dole ku bambanta tsakanin haramtacce da halaltacce, tsakanin halittu masu ran da za a iya ci da waɗanda ba za a iya ci ba.’ ”

Você sabia?
Animais Limpos e Impuros
- As leis alimentares de Levítico estabelecem critérios duplos claros para animais terrestres e aquáticos: as criaturas da terra precisavam ruminar e ter cascos fendidos para serem comidas, enquanto as criaturas das águas precisavam ter tanto barbatanas quanto escamas.Fontes: o próprio texto bíblico
- As leis de pureza se estendiam aos utensílios domésticos: panelas de barro e fornos contaminados pelo cadáver de um animal rastejante impuro não podiam ser apenas lavados como objetos de madeira ou tecido, mas deviam ser completamente quebrados.Fontes: o próprio texto bíblico
- O propósito teológico declarado para distinguir entre o puro e o impuro era a consagração de Israel a Deus, que os tirou do Egito e os chamou a serem santos porque Ele é santo.Fontes: o próprio texto bíblico · Egypt
Notas escritas com auxílio de IA a partir de fontes abertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, domínio público) e revisadas antes de publicar.
Lugares deste capítulo
- Egypt · 30.129, 31.308 · versículo 45
Só aparecem lugares com identificação de alta confiança (90% ou mais segundo as fontes acadêmicas reunidas pelo OpenBible). Mapa da época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa atual: © colaboradores do OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos e licença desta tradução
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fonte: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org